FITACCIYAR jaruma Rahama Sadau a jiya Talata ta wallafa sababbin hotuna masu zafi da ta ɗauka tare da ƙannen ta mata.
Hotuna guda huɗu da jarumar ta Kannywood ta tura a Instagram na nuna ta tare da Zainab Sadau, Fatima Sadau da Aisha Sadau, kowaccen su ta tsuke da shuɗin wando ‘jeans’ da farar shat da ɗankwali.
Yayin da ƙannen ta ke sanye da buɗaɗɗun takalma, Rahama kuwa sau-ciki ta sanya.

Bakin ƙafafun wandon jaruma masu faɗi ne, irin shigar shekarun ’70s, amma na ƙannen ta tsukakku ne.
An ɗauki hotunan a shagon hoto na Artisan Studios a Kaduna, sannan gwanar kwalliya, Jiddah Abubakar, ita ce ta yi masu aikin gyaran fuska da gashi, wato ‘makeup’.
Rahama ta yi rubutu a saƙon hotunan, inda ta ce da Turanci, “Sisters make the best friends in the world”, wato “‘Yan’uwa mata su ne abokai mafi dacewa a duniya”.

Ɗaruruwan mabiyan Rahama a Instagram da kuma waɗanda su ka ga hotunan a shafukan mujallar Fim na Instagram da Facebook sun bayyana ra’ayoyi mabambanta. Yayin da wasu ke mamakin cewa kyawawa kuma riɗa-riɗan ‘yanmata irin waɗannan ba su yi aure ba har yanzu, wasu kuma na addu’ar Allah ya ba su masu mazan aure nagari.
Akwai waɗanda su ka ɗora laifin rashin yin auren a kan Rahama saboda wai tunda ita ce babba, kamata ya yi ta kafa wa sauran misali da yin aure. Akwai ma waɗanda su ka ce duk laifin mahaifin ‘yanmatan ne, wato Alhaji Ibrahim Sadau, da bai aurar da ko ɗaya daga cikin su ba.
Amma ita Rahama ko a jikin ta, domin ba ta tanka wa kowa ba. Ban san ky na yi ba, wai an tsikari kakkausa kenan!

A yau da safe ma ta sake wallafa wasu hotuna uku na ita da Fatima da kuma Aisha kwatankwacin waɗanda ta wallafa jiya.
A ɗakin su Rahama dai su shida ne – mata huɗu da maza biyu; a mazan, ɗaya wan ta ne, sannan ɗayan kuma shi ne ɗan’autan su.


