• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 23, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Salisu Mu’azu ya gode wa jama’a bayan ya tsira daga hannun ɓarayi

by DAGA IRO MAMMAN
May 27, 2019
in Labarai
0
Ana sauko da Salisu Mu'azu daga kan motar ɗaukar icce jim kaɗan bayan sun tsira daga hannun ɓarayi

Ana sauko da Salisu Mu'azu daga kan motar ɗaukar icce jim kaɗan bayan sun tsira daga hannun ɓarayi

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
FITACCEN darakta Salisu Mu’azu ya gode wa masoya kan jajantawar da su ka yi masa sakamakon sace shi da wasu ɓarayi masu garkuwa da mutane su ka yi.
 
Shi dai Salisu, ɓarayin sun sace shi ne tare da darakta Ɗanlami Yanke-Yanke na Bauchi da wani mutum ɗaya mai suna Bature a kan hanyar su ta zuwa Jos daga Kaduna a ranar 23 ga Mayu, 2019.
 
Yayan shi, wato Alh. Sani Mu’azu, wanda shi ma darakta ne kuma fitaccen jarumi, shi ne ya fara bada labarin kama su da aka yi a wani saƙo da ya tura a  Facebook a ranar.
 
Sani ya ce abin ya faru ne a kan hanyar su ta zuwa Jos daga Kaduna, inda su ka halarci wani taro.
 
Ya ce shi kan sa ya na cikin motar lokacin da su ka yi kiciɓis da ɓarayin.
 
Ya ce sun rage wa darakta Ɗanlami Yanke-Yanke da Bature hanya ne, waɗanda za su wuce zuwa Bauchi.
 
Ɓarayin sun saki Sani Mu’azu ganin cewa bai da isasshiyar lafiya, ba zai iya tafiya mai nisa a ƙasa ba. 
 
Daga nan su ka yi cikin daji da su Salisu.
 
A ranar, ɓarayin, waɗanda aka ce Fulanin daji ne, su ka bugo waya su ka buƙaci a biya diyyar fansar su, har naira miliyan goma.
 
Lokacin da ya bada sanarwar sace mutanen uku, Sani ya roƙi jama’ar Annabi da su taimaka da addu’o’in samun nasarar ceto waɗannan bayin Allah.
 
Ga yadda ya bada labarin da Turanci:
“Yesterday on our way back to Jos from Kaduna after attending a conference, we ran into armed robbers/kidnappers at around Saya, after Jengre. We were robbed and I am lucky to have escaped but my younger brother, Salisu Mu’azu, and the two friends we gave a ride to Jos on their way to Bauchi, Ɗanlami Yanke-Yanke and Bature were kidnapped by the, obviously, Fulani attackers. They got in touch this morning demanding 10 million naira.
 
“Please help me pray for their safe release. May Allah help us to see the last of this national confusion. Ameen.”
 
Su Salisu sun shafe kwana uku a hannun ɓarayin, a yayin da ake ta fafutikar neman gudunmawar kuɗi da za a kai wa Fulanin.
 
A yammacin ranar 26 ga Mayu, ɓarayin su ka sako Salisu da sauran mutum biyu da su ka sace.
 
Mujallar Fim ba ta san ko nawa aka biya aka sako su ba.
 
Bayan sakin nasu, Sani Mu’azu ya tura saƙon godiya a Facebook inda ya ce sun biya maƙudan diyya kafin a sako su.
 
Ya ce ɓarayin sun sake su ne a bakin wani daji inda wani mai motar ɗaukar itace ya taimaka ya kawo su.
 
A taƙaitaccen saƙon sa na godiya, Salisu ya rubuta da Turanci a Facebook cewa: “For the incomparable love, care, prayers and support you gave in my trying moments, I say a big thank you!!!”
Fassara: “Saboda ɗimbin soyayya, kulawa, addu’a da goyon bayan da ku ka yi mani a lokacin da na ke cikin garari, ina matuƙar godiya a gare ku.”
 
Salisu Mu’azu ya na daga cikin shugabannin Ƙungiyar Masu Shirya Finafinan Hausa ta Nijeriya, wato MOPPAN. Ya taka muhimmiyar rawa wajen sasanta Ali Nuhu da Adam A. Zango a ɓatawar su ta kwanan baya.
 
Sani Mu’azu kuma shi ne shugaban ƙungiyar na ƙasa na farko.
 

Loading

Tags: BanditsDanlami Yanke-yankehausa filmsKannywoodKidnappingMOPPAN
Previous Post

Hussaina Musa za ta shafe shekara 2 a Oman

Next Post

Taƙaitaccen Tarihin Malam Ibrahim Ɗanmani Caji

Related Posts

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Next Post
Malam Ibrahim Ɗanmani Caji a Kaduna a cikin 1974

Taƙaitaccen Tarihin Malam Ibrahim Ɗanmani Caji

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!