LABARIN da muka samu yanzu-yanzun nan shi ne Allah ya ɗauki ran shahararriyar jarumar Kannywood, Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a safiyar yau.
Majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa Saratu, wadda ta yi fice a wasannin barkwanci ko na mugunta, ta kwanta barci lafiya ƙalau bayan ta yi sahur ɗin azumin yau, to amma tafiyar kenan.
Majiyar ta ce ana nan an fara shirin yi mata jana’iza anjima kaɗan.
Mutuwar ta girgiza masana’antar shirya finafinai ta Kannywood matuƙar gaske.
Allah ya rahamshe ta, amin.