• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 25, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Satar basira: Misbahu Ahmad ya ja kunnen mawaƙan zamani

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
July 6, 2021
in Labarai
2
Satar basira: Misbahu Ahmad ya ja kunnen mawaƙan zamani
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN mawaƙin Kannywood, Misbahu M. Ahmad, ya yi kakkausan gargaɗi ga matasan mawaƙa masu tasowa kan satar basira, inda ya ce zai sanya ƙafar wando ɗaya da su.

Misbahu ya yi gargaɗin ne bayan ya lura da yadda wasu mawaƙa su ka ɗauki waɗansu tsofaffin waƙoƙi irin na da su ka juya su zuwa wani salo na daban, ya ce shi kam zai ɗauki matakin shari’a kan duk mawaƙin da ya kama ya yi masa haka.

Juya fitattun waƙoƙin finafinan Hausa da su ka yi tashe a da wanda matasan mawaƙa ke yi a yanzu ya zama ruwan dare.

Misbahu ya ɗora laifin barin matasan mawaƙan su na cin karen su ba babbaka kan shugabannin industiri.

A wani saƙon murya da ya tura cikin wani guruf na shugabannin masana’antar a jiya Litinin, wanda mujallar Fim ta samu, shahararren mawaƙin ya bayyana cewa abubuwa da dama su na faruwa a Kannywood waɗanda ya kamata a ce mahukunta sun tsawatar a kan su, to amma sun shafa wa idon su kwalli tare da kauda kai daga abin da ke faruwa.

Misbahu, wanda kuma babban jarumi ne, ya ce, “Alal haƙiƙa, mu na da shuwagabanni, amma a baka. Shugabanci kullum ya na da’awar shugabanci ne shi ko kuma shuwagabanni ne, amma da yawa akwai abubuwan da su ka kamata a ce akwai jagoranci, a ce akwai tsawatarwa, akwai doka, amma ba a tafiyar da su, ba a san da su ba.

“Yanzu mu na raye a matsayin mu na mawaƙa waɗanda an san irin waƙoƙin da mu ka yi kuma waƙoƙin nan an san irin tasirin da su ka yi a cikin masana’antar nan, an san cigaban da su ka kawo, an san irin arzikin da aka samu da su, ba ma mu kankin kan mu ba, ‘ya’yan mu ma da mu ke gadara za su yi alfahari da su, to sai ga shi tun da ran mu ma yanzu mu na ji mu na gani yaro ya taso, bai san hawa ba bai san sauka ba, bai san ya aka yi aka yi waƙa ba, idan ka tambaye shi waye mawaƙin  bai sani ba, kawai saboda ya na situdiyo a zaune tare da wani furodusa ko ya na tare da wani mawaƙi, kawai sai ya zo ya ɗauki waƙa ya je ya zauna a gida ya sa ta a kaset ya na ji, ya na bin ta baiti bayan baiti, ɗango bayan ɗango, ya rubuta ta a takarda ya zo ya biya kuɗi dubu biyu ko dubu uku, ya zauna a situdiyo a sake mata kiɗa ya ɗora muryar sa, ya nemo yarinya ta ɗora muryar ta. Kawai sai ya zo ya sake ta a YouTube ko ya sake ta a duniya, kawai ya na samun kuɗi.”

Cikin ɓacin rai, Misbahu ya ƙara da faɗin, “Da ran mu mu na ji mu na gani waƙoƙin nan mu mu ka ƙirƙire su, ba ma waƙa ce irin ta nanaye ko ahayye ko irin ayye mama ayye mama da za a ce waƙa ce ta dandali ba, a’a, wasu waƙoƙin kai ka ƙirƙiri abin ka da karin da rubutun da komai, ka na ji ka na gani ka na raye wani yaro ya ɗauka!”

Mawaƙin ya faɗi abin da ka iya faruwa idan fasihai irin sa su ka yanke hukuncin bin haƙƙin su a kan masu satar basirar su, ya ce, “Abin da ya sa na ke magana, daga lokacin da ka yunƙuro ka ce za ka nemi haƙƙin ka ko ba ka yarda ba, ko ka nuna ba ka amince ba ko ka nemi bahasi, sai ka ji a cikin masana’antar za a dawo ana zagin ka, ana cewa kai mafaɗaci ne, ba ka da mutunci, ko ka yi rashin mutunci ko ka na yi wa yaro hassada don zai ci gaba, da kaza da kaza. Wannan abin fa ba daidai ba ne!” 

Ya ƙara da cewa, “Babu yadda za a yi mutum ya shiga ɗakin ka ya ɗaukar maka kaya, ka kama shi ka na raye da ikon ka, ka yi da’awar ka kama ɓarawo a ce don me za ka kama shi? Ya kamata a samu shugabanci ya kalli waɗannan abubuwan.

“Yanzu ta wuce ma a ɗau baiti ko ka ƙirƙiro wata kalma ka sa a waƙar wani mawaƙi ya ɗauka ko wani baiti a ɗauka, a’a, ta wuce wannan; ka yi waƙa da yarinya, ta koma ta ɗauki waƙar ta tafi situdiyo ta rera ta ga baki ɗaya saboda ka ɗaga ta da waƙar, ta ɗaukaka, ta ɗauke waƙar ta na bada tarihi. In ta zo tarihin ma ko sunan ka ba za ta ambata ba! Duk wannan mun haƙura da shi.”

Misbahu ya kira lamarin da hannun-ka-mai-sanda ga shugabannin Kannywood domin su farka su ɗauki matakin da ya kamata.

A ƙarshe, ya yi rantsuwar cewa zai sa ƙafar wando ɗaya da duk wani mawaƙi da ya ɗaukar masa waƙa ya juya ta ba tare da izinin sa ba.

Ya ce, “Wallahil azim, duk wanda ya taɓa waƙa ta ko ya hau waƙa ta, idan na samu labarin inda ya ke sai na kamo shi mun yi shari’a da shi, kuma sai an biya ni haƙƙi na.”

Ba Misbahu M. Ahmad kaɗai ba, mawaƙa da dama, musamman ma dai tsofaffin, su na nuna takaicin su kan yadda wannan abu na satar basirar su da sababbin mawaƙa ke yi ya zame musu ƙarfen ƙafa, wato salon maganar nan ta kura da shan bugu gardi da karɓe kuɗi.

Mujallar Fim ta samu labarin cewa sakamakon wannan koken da Misbahu ya tura, shugaban ƙungiyar ƙwararru masu shirya finafinan Kannywood na ƙasa (MOPPAN), Dakta Ahmad Sarari, ya gayyace shi zuwa ofishin sa domin su tattauna matsalar saboda a yi wa tufka hanci.

Misbahu dai shi ne yayan fitattun ‘yan Kannywood ɗin nan biyu, darakta Aminu Saira da mawaƙi Naziru M. Ahmad.

Loading

Tags: Dr Ahmad Sararihausa actorsHausa singersKannywoodMisbahu M. AhmadMOPPAN
Previous Post

Sai Ka Yi, Aminu Sarki!

Next Post

Gwamnati ta soma sake nazarin Dokar Haƙƙin Mallaka

Related Posts

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
Next Post
Gwamnati ta soma sake nazarin Dokar Haƙƙin Mallaka

Gwamnati ta soma sake nazarin Dokar Haƙƙin Mallaka

Comments 2

  1. Jamila Adamu Yaro says:
    4 years ago

    Haqqun misbahu ina bayan ka Allah dafa muku dukkan tsoffin mawaka Ku tashi ku nemi hakkin Ku, wallahi ranar da naji wakar ‘sangandali’ a gidan radio an juya ta, sai da naji ba dadi…

  2. Habeebah badikko says:
    4 years ago

    wallahi nima abunnan yana bata mani rai kwarai, musamman yadda naji wani ya juya sangandale,, da wakar sa mani kugiya. randa nafarajinta, abub ya daure mani kai har kaji wasu, suna cewa wadanda aka satan aka juya har sunfi na ainahin wai dadi. gaskiyaa muna baku goyon baya kukwaci hakkinku Allah yabaku nasara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!