JARUMI kuma darakta a Kannywood, Malam Al-Amin Ciroma, ya bayyana cewa jajircewa tare da haƙuri da juna su ne silar ɗorewar auren sa da tsohuwar jaruma Wasila Isma’il.
A yau Alhamis, 6 ga Oktoba, Ciroma da Wasila su ka cika shekara 20 cur da aure.
Tun wajen ƙarfe 10:00 na safe daraktan ya wallafa wata fosta mai ɗauke da hoton sa da iyalin sa gaba ɗaya a soshiyal midiya, aka rubuta: “Our 20th Wedding Anniversary,” sannan aka kawo wannan lissafin: “Watanni 240, makwanni 1,043, kwanaki 1, 306, sa’o’i 176, 344, mintuna 10, 520, 640, sakwanni 631, 238, 400, ‘ya’ya biyar, ɗaya ya rasu, Allah ya jiƙan Muhammad Al-Baqir, amin.”

A bayanin da ya yi wa mujallar Fim kan sirrin daɗewar su tare, Ciroma ya ce, “Alhamdu lillah. Shekara ashirin a zaman aure ana tare, sai dai hamdala. Ka san rayuwar aure rayuwar addini ce, kamar yadda kowa ya sani. Tilas ne mutum ya jajirce, ya kuma yi haƙuri da duk jarabawan da zai ci karo da su na zaman taren, musamman a yanzu ma da riƙon auren ya ke da tsada a ƙasar Hausa. Galibi, za ka iske da dama cikin aurarrakin yanzu su na saurin rugujewa saboda matsaloli daban-daban na haɗakar zamantakewa.
“To, ka ga kenan, duk wanda Allah a raya shi har ya shafe shekaru irin wannan ana tare, shakka babu, tilas ka yi godiya a gare shi.”
Ciroma, wanda shi ne kuma kakakin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), ya yi tsokaci kan masu ‘yan fim ba su daɗewa a aure, ya ce, “Auren ‘yan fim shi ma wata makaranta ce ta daban. Baya ga sa ido da mutanen gari ke yi mana, akwai yadda kuma ake kallon mu. Ana saurin nuna cewa matan fim ba sa zama a gidajen su na aure. Hakan ne ma ya sa ake yi masu kuɗin goron.
“Amma kuma da hikimar Allah, sai mu mu ka tsallake duk waɗannan maganganun.”
Ya bayyana wani abu wanda ba kowa ya sani ba, ya ce: “Ba na tsammanin akwai wata ‘yar fim da su ka yi aure tare da Wasila wadda ta kai ta daɗewa ba tare da wani rikici ko ce-ce-ku-ce ba.
“Don haka na ke yin kira ga sauran ‘yan’uwa da abokan arziki a cikin masana’antar Kannywood da mu ci gaba da ba maraɗa kunya, mu jajirce mu riƙe wa juna amana.”