WATA malamar makarantar Islamiyya da ke unguwar Mubi, kusa da Ƙofar Nassarawa a cikin birnin Kano, ta zargi ɗan wasan barkwanci Aminu Baba Ari, da yi mata dukan tsiya har ya kai ta ga faɗuwa ƙasa. Jarumin ya kuma yi barazanar zai taka ta da takalmi, inji ta.
Malama Zainab ta shaida wa mujallar Fim yadda abin ya faru, ta ce yara ne su ke karatu, a cikin su har da ‘yar Aminu Baba Ari, inda su ka yi laifin da za a hukunta su. To amma kuma da hukuncin ya zo kan ‘yar Baba Arin sai ta riƙe bulalar, ta kafe a kan ita ba za a dake ta ba.
A yunƙurin dukan nata ne har ta faɗi ƙasa, aka ce “aljannun ta ne su ka tashi.”
Ta ci gaba da cewa, “Bayan shi Aminu Baba Ari ya samu labarin, sai ya zo ya rufe ni da duka, har na faɗi ƙasa. Sannan ya yi ƙoƙarin taka ni da takalmin sa.”
A sakamakon wannan abu dai shugabannin makarantar sun nuna ɓacin ran su tare da ɗaukar mataki a kan wannan cin zarafi da aka yi wa malamar domin kiyaye ƙara faruwar haka a nan gaba.
Amma a nasa ɓangaren, da mujallar Fim ta tuntuɓe shi kan lamarin, Baba Ari, ya ce lallai shi bai yi dukan da ake cewa ya yi ba. Ya ce ya dai daki ɗankwalin malamar ta baya.
“Kuma a yanzu ma an daidaita, komai ya wuce,” inji shi.