AN bayyana cewa gidaje 124,589 ne su ka amfana daga shirin nan na ciyar da ɗalibai a gida a jihohi 3, kuma kowane gida ya amfana da N4,200.
Ministar Harkokin Agaji, Jinƙai da Inganta Rayuwar Marasa Galihu, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta bayyana haka a lokacin da ta ke ƙarin haske kan shirin, a wani taro a Abuja.
Ta ƙara da cewa ba kamar yadda mutane da dama su ke zato ba, Gwamnatin Tarayya ta bada kuɗaɗen shirin ne ga gwamnatocin jihohi uku kacal, su kuma su ka aiwatar da shirin.
Ministar ta na bayani ne dangane da ji-ta-ji-ta da labaran bogi da ake yaɗawa kan adadin kuɗaɗen da ake kashewa a kullum a kan shirin.
A takardar sanarwa da aka raba wa manema labarai tare da sa-hannun hadimar ministar a ɓangaren yaɗa labarai, Hajiya
Halima Oyelade, an ruwaito ministar ta na faɗin cewa: “Ana ta watsa ji-ta-ji-ta da ƙarairayi a kan ɗaya daga cikin ɓangarorin tallafin da wannan ma’aikatar ke bayarwa, wato shirin ciyar da ɗalibai daga gida, wanda aka aiwatar a jihohi uku, bisa umarnin da Shugaban Ƙasa ya bayar tun a ranar 29 ga Maris, 2020.
“Wannan shiri na ciyar da ɗalibai daga gida a lokacin zaman gida sakamakon ɓarkewar cutar korona, ba shiri ne da wannan ma’aikata ita kaɗai ta ƙirƙiro ba.”
Hajiya Sadiya ta ƙara da cewa kafin a aiwatar da shirin, sai da ma’aikatar ta ta tuntuɓi ɗaukacin gwamnonin ƙasar nan, su su ka bada shawarar cewa ciyar da ɗalibai daga gida a lokacin shi ne hanyar mafi dacewa a lokacin zaman kullen korona a gida.
“Daga nan kuma masu ruwa da tsaki a harkar su ka amince a fara da FCT Abuja da Legas da Ogun a matsayin jihohin da za a yi gwajin shirin.”
“Yadda Aka Amince A Raba N4,200 A Gidaje”
Hajiya Sadiya ta ce: “An amince cewa za a raba wa kowane gidan da ke cikin lissafi N4,200. Kuma ba haka kawai aka kintaci adadin kuɗaɗen aka rubuta ba.
“An yi amfani da ƙididdigar alƙaluman ƙiyasin yawan iyalin da ke kowane gida da Hukumar Ƙididdigar Alƙaluma ta Ƙasa (NBS) da kuma Babban Bankin Najeriya (CBN) su ka yi, cewa aƙalla kowane gida a ɗauka akwai mutum 5 zuwa 6 a ciki. A cikin su shida ɗin kuma ƙididdigar ta ƙiyasta akwai cima-zaune mutum 3.
“Saboda haka sai mu ka yi amfani da tsohuwar ƙididdigar da ke ƙasa ta Ciyar da Ɗalibai daga Gida, wadda ake bai wa kowane ɗalibi abinci kyauta sau ɗaya a rana. Abincin kowane yaro na daidai da N70 ne. Idan ka dauki kwanaki 20 da ake zuwa makaranta a wata ɗaya, to yaro ɗaya zai ci abincin N1,400 kenan a wata. Cikin wata 3 yaro ya ci abincin N4,200 kenan. To kun ji yadda aka bi diddigin kaiwa ga adadin kuɗaɗen da aka kashe a kowane gidan da ya amfana da shirin.”
“A FCT, Legas Da Ogun Kaɗai Aka Ƙaddamar Da Shirin”
Minista Sadiya ta bayyana cewa wannan shiri an ƙaddamar da shi ne a FCT Abuja, Jihar Legas da Jihar Ogun kaɗai.
“A yankin FCT Abuja, an shiga garuruwa aka raba wa gidaje 29, 609, a Jihar Legas gidaje 37,589 su ka ci moriyar shirin. A Jihar Ogun kuma gidaje 69,391 su ka amfana.
“Baki ɗaya jimillar gidaje 124,589 kenan su ka ci moriyar shirin ciyarwar da aka ƙaddamar tsakanin ranakun 14 ga Mayu zuwa 6 ga Yuli, 2020. Kenan gaba ɗaya adadin kuɗaɗen za su kama N523,273,800.
“Kuma a kula cewa ba fa a kullum ne aka riƙa kashe waɗannan kuɗaɗen ba. An fara ƙaddamar da na FCT Abuja, sai na Legas, daga nan kuma sai na Ogun.”
Ministar ta ce babu inda ta taɓa cewa an raba wa kowane gida a ƙasar nan kuɗaɗe ko kayan tallafi. Ta ce amma dai an raba wa kowace gwamnatin jiha ta karɓi nata tallafin da aka ce ta raba wa marasa galihu da mabuƙata a jihohin su.
A ƙarshe ta ce ma’aikatar ta ba za ta saki miƙaƙƙiyar hanyar da ta ke bi wajen aiwatar da shirye-shiryen ta masu muhimmanci ga al’umma ba.