INNA lillahi wa inna ilahair raji’un! Allah ya yi wa mahaifin fitacciyar ‘yar jaridar nan mai aiki a gidan Rediyon Nagarta da ke Kaduna, Hajiya Bara’atu Sa’eed, rasuwa.
Alhaji Sa’eed Awaisu ya rasu ne a ranar Asabar, 1 ga Agusta, 2020 da misalin ƙarfe 11 na dare, a Asibitin Musulmi da ke Tudun Wada, Kaduna.
Alhaji Sa’eed, mai kimanin shekara 83, ya rasu ne bayan ciwon ciki na kwana biyu da ya yi.

Ya rasu ya bar mata ɗaya da ‘ya’ya goma: maza biyar, mata biyar.
Hajiya Bara’atu, wadda ta gi fice wajen bada labaran ‘yan fim da hira da su a gidan rediyo, ita ce ta huɗu a cikin su.
Da fatan Allah ya jiƙan shi da rahama, ya albarkaci dukkan abin da ya bari, ya sa Aljannar Firdausi ce makoma, amin.
![]()







