• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, November 3, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Aminu Ala: Zan fitar da ‘Damuwa’ a ranar Babbar Sallah

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
July 29, 2020
in Mawaƙa
0
Fostar faifan 'Damuwa'

Fostar faifan 'Damuwa'

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
AMINU Ladan Abubakar (Ala) zai fitar da sabon faifan waƙoƙin sa a jibi, wato ranar Babbar Sallah.
 
Ala, wanda shi ne Sarkin Waƙar Sarkin Dutse, ya ɗan jima bai fitar da wata sabuwar waƙa ba.
 
Fitaccen mawaƙin ya faɗa wa mujallar Fim cewa zai fitar da waƙoƙin ne a matsayin kundin waƙar sa na bana, kuma ya raɗa masa suna ‘Damuwa’.
 
Ya ƙara da cewa, “Na yi shi ne kamar yadda na saba yin waƙoƙi na a baya, ina fitar da su ga ɗimbin masoya na domin faɗakarwa da nishaɗantarwa.”
 
Sunayen waƙoƙin sun haɗa da ‘Damuwa’, wadda ita ya bai wa sunan kundin, da wata mai suna ‘Ya Aka Kwana Ya Aka Tashi?’, da ‘Malam Nagurafe’, da sauran su.
 
A kan dalilin sa na yin album bayan kasuwar sidi da dibidi ta durƙushe, fasihin sha’irin ya ce, “Kowa ya san yadda lamarin kasuwancin finafinai da waƙoƙi ya ke a wannan lokacin, wanda a yanzu ya koma ‘online’. A nan ake tallata haja ana sayarwa kuma a ci riba. Don haka a yanzu ma ‘yan kasuwa sun daina bugawa ma.
 
“Amma dai saboda yanayi na al’adar taskace waƙoƙi a kundi saboda masu nazari a jami’o’i da malaman nazari, da kuma damar da na ke da ita ta tafiyar da waƙoƙi na cikin tsari na lissafi, wanda duk shekara an san na kan yi kundin waƙa ɗaya ko biyu, kuma wani lokaci idan ba a saka su a mazubi ba waƙoƙin su na ɓata, har ma ba a sanin cewar ka yi waƙar, don haka na yi wannan kundin, amma ba wai don kasuwancin ba. 
 
“Ribar dai shi ne jama’a su san ka yi, sannan kuma a shigar da shi a cikin wata ƙa’ida ta cewa wannan shekarar ma an yi waƙar ko an yi wani kundin waƙa da ya ke ɗauke da waƙoƙi kaza a cikin sa, wanda hakan zai sa idan ana neman waƙar an san kundin da za a same ta. 
 
“To wannan lissafin ne ya sa ni har yanzu na ke yin kundin waƙa na ce na fitar da shi, amma ba don a sayar a ce an ci riba ba. Don haka ina yi ne domin manazarta da ɗaliban jami’a, da kuma masoya na.”
 
Ala ya yi fatan alheri ga masoyan sa waɗanda kullum su ke yi masa fatan alheri.

Loading

Previous Post

Hamza Prince: Ban ci ribar waƙa ba, shi ya sa na daina

Next Post

Mahaifin Bara’atun Rediyo Nagarta ya kwanta dama

Related Posts

Tijjani Gandu ba zai iya amsa gayyatar hukuma ba, inji lauya
Mawaƙa

Tijjani Gandu ba zai iya amsa gayyatar hukuma ba, inji lauya

October 5, 2026
Hukumar Tace Finafinai za ta hukunta Tijjani Gandu saboda sakin waƙa ba tare da izini ba
Mawaƙa

Hukumar Tace Finafinai za ta hukunta Tijjani Gandu saboda sakin waƙa ba tare da izini ba

October 3, 2026
Mawaƙin yabon Annabi, Kamsusi Bala Maiyafe, ya kwanta dama
Mawaƙa

Mawaƙin yabon Annabi, Kamsusi Bala Maiyafe, ya kwanta dama

September 7, 2026
An zaɓi Bashir Yahuza Malumfashi shugaban sha’iran Jihar Katsina
Mawaƙa

An zaɓi Bashir Yahuza Malumfashi shugaban sha’iran Jihar Katsina

September 2, 2026
Hassada da gasa ne matsalar sha’irai mata – Shamsiyya Khadimar Ma’aiki
Mawaƙa

Hassada da gasa ne matsalar sha’irai mata – Shamsiyya Khadimar Ma’aiki

August 30, 2026
Za a gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ran Asabar
Mawaƙa

Za a gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ran Asabar

August 23, 2026
Next Post
Marigayi Alh. Sa'eed Awaisu tare da Hajiya Bara'atu Sa'eed

Mahaifin Bara'atun Rediyo Nagarta ya kwanta dama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!