Gwamnatin Tarayya ta ce ta kammala shirye-shiryen fara bayar da N20,000 ga duk matan karkara a faɗin kasar nan a ƙoƙarin Shirin Inganta Rayuwar na Ƙasa (NSIP).
An ƙirƙiro shirin bayar da tallafin ne ga ‘yan ƙasa mabuƙata a cikin shekarar 2020 don inganta rayuwar su da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi a ƙarƙashin shirin fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin talauci.

Ministar Harkokin Agaji, da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja yayin wani taron manema labarai da masu ruwa da tsaki kan aiwatar da tallafin ga mabuƙata.
Hajiya Sadiya ta ce an fito da wannan sabon tsarin bada tallafin ne domin agaza wa mata masu fama da talauci a yankunan karkara da ke ƙasar nan.
Ta ce: “Za a raba tallafin kuɗi na N20,000 ga kowace mace ko namiji masu fama da talauci a faɗin jihohi 36 da Gundumar Babban Birnin Tarayya.”
Ministar ta roƙi waɗanda za su ci gajiyar tallafin da su yi amfani da shi ta hanyar zuba kuɗaɗen a kasuwanci mai ɗorewa don inganta rayuwar su.
![]()






