HAƊAƊƊIYAR Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta jan kunnen ‘yan da ke amfani da sunan ƙungiyar su na harkar siyasa da su daina.
A wata takarda ga manema labarai mai taken “MOPPAN Ba Ƙungiyar Siyasa Ba Ce, Masu Amfani Da Ita A Harkar Siyasa Su Daina,” wadda ya aiko wa mujallar Fim da kwafen ta a yau, Kakakin MOPPAN na ƙasa, Malam Al-Amin Ciroma, ya ce: “Ana jawo hankalin dukkanin masu ruwa da tsaki gami da shugabanni a matakin jiha da na ƙasa cewa ƙungiyar MOPPAN ba ƙungiya ce ta siyasa ba, kuma ba ta da alaƙa da wata jam’iyya.
“Wannan tunatarwar ta na zuwa ne a daidai lokacin da labarai su ka zo wa shugabanni na ƙasa cewar wasu jihohi na amfani da inuwa gami da sunan MOPPAN wajen shiga harkokin siyasa a jihohin su, wanda hakan babban zunubi ne ga ƙungiyar da kuma masana’antar baki ɗaya. Hakan kuma ya na rarraba kawunan ‘yan ƙungiyar.”
Ciroma ya ci gaba da cewa: “Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Muhammad Sarari, ya nuna takaicin sa ga masu irin wannan ɗabi’ar, ya kuma ja kunnen dukkanin waɗanda ke aikata hakan, da ma masu tunani ko yunƙurin shiga harkokin siyasa da sunan ƙungiyar, su gaggauta janyewa daga aikata wannan ɗanyen aikin.”
Sarari ya yi kira ga dukkan shugabanni da membobin ƙungiyar da su mutunta martabar MOPPAN, su aikata abin da ya dace.