• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Shugaban ICPC ya ce babu hannun Minista Sadiya a wawurar biliyan N2.7

by DAGA WAKILIN MU
September 29, 2020
in Nijeriya
0
Hagu zuwa dama: Hajiya Sadiya Umar Farouq da Farfesa Bolaji Owasanoye

Hagu zuwa dama: Hajiya Sadiya Umar Farouq da Farfesa Bolaji Owasanoye

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
HUKUMAR Binciken Ayyukan Cin Hanci Da Rashawa (ICPC) ta bayyana cewa ko kaɗan ba Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ba ce ta ke nufi da saka hannu cikin sace wasu kuɗi na shirin ciyar da ɗalibai a lokacin zaman korona.
 
A yau ɗin nan ne wasu kafafen yaɗa labarai da mutane a soshiyal midiya su ka baza labarin cewa wai ana zargin Minista Sadiya Umar Farouq da taka rawa wajen sace sama da naira biliyan biyu da miliyan dubu sittin da bakwai (N2.67b) daga cikin kuɗin da aka ware don ciyar da ɗalibai lokacin da ake zaman dirshan saboda annobar korona.
 
Hakan ya biyo bayan jawabin da shugaban hukumar, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya yi a jiya Litinin, 28 ga Satumba, 2020 a wajen Babban Taro na Ƙasa kan Raguwar Cin Hanci da Rashawa, karo na biyu, a Abuja.
 
Hukumar ICPC ta ce rahotannin sun tafka kuskuren cewa Hajiya Sadiya ce ta kautar da kuɗin na shirin da ake kira “Home-Grown School Feeding Programme”. 
 
Abin da Farfesa   Owasanoye ya faɗa a jawabin sa a taron, shi ne, “… mun gano cewa wasu kuɗaɗen da aka biya ga wasu kwalejojin gwamnatin tarayya (makarantun sakandare) don ciyar da ɗalibai ‘yan sakandare, wanda sun kai N2.67 biliyan lokacin zaman dole a sa’ilin da ‘yan makaranta ba su zuwa makaranta, sun shige aljifan mutane ne.
 
“Mun soma bincike kan waɗannan abubuwan da mu ka gano.”
 
Hukumar ta ce ta na so ta faɗakar da jama’a cewa “ciyarwar ‘yan makaranta” da shugaban ICPC ya ambata ita ce ta ɗalibai da ke kwana a Kwalejojin Gwamnatin Tarayya, waɗanda duk su na zaune a gida a lokacin zaman dole na annobar COVID-19.
 
Ta ce: “Wannan BA shirin ‘Home-Grown School Feeding Programme’ ba ne wanda Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya. 
 
“Hukumar ta gano a lokacin da ta ke nazari kan takardun Gidan Yanar Buɗaɗɗen Asusu (Open Treasury Portal) cewa kuɗaɗen da aka kasafta za a riƙa kashewa a wata-wata kan ciyar da ɗaliban makarantun sakandare na WASU daga cikin Kwalejojin Gwamnatin Tarayya ana kautar da su zuwa asusun wasu mutane.
 
“Mun fitar da wannan sanarwar ne domin mu yi ƙarin haske kan bayanin da Shugaba ya yi.
 
“Saboda haka, mu na sanar da dukkan jama’a cewa su yi watsi da waɗancan rahotannin da su ke cewa shirin ciyar da ɗaliban makarantun firamare ne mu ka yi magana a kai.”
 
Hukumar ta faɗa wa duk mai buƙata cewa zai iya sauko da cikakken jawabin da shugaban ya yi daga gidan yanar hukumar da ke intanet a wannan adireshin, wato www.icpc.gov.ng.

Loading

Previous Post

Cewar Minista Sadiya: Ba hannu na a ɓacewar kuɗin ciyar da ‘yan makaranta

Next Post

Bashir Nura Alkali ya zama babban sakataren Ma’aikatar Harkokin Jinƙai

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Bashir Nura Alkali

Bashir Nura Alkali ya zama babban sakataren Ma'aikatar Harkokin Jinƙai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!