• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar Minista Sadiya: Ba hannu na a ɓacewar kuɗin ciyar da ‘yan makaranta

by DAGA WAKILIN MU
September 28, 2020
in Nijeriya
0
Hajiya Sadiya Umar Farouq

Hajiya Sadiya Umar Farouq

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
MINISTAR Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa babu hannun ta a ɓacewar wasu daga cikin kuɗi naira biliyan biyu da miliyan saba’in da biyu (N2.72b) daga asusun shirin ciyar da ‘yan makarantar kwalejojin Gwamnatin Tarayya saboda zaman annobar korona kamar yadda wasu ke yaɗawa a kafafen watsa labarai.
 
An riƙa yaɗa labarin ne bayan da shugaban hukumar binciken cin hanci da rashawa (ICPC), Farfesa Bolaji Owasanoye, ya gabatar da wani jawabi a wajen Babban Taron Ƙasa Kan Raguwar Cin Hanci, karo na 2, wanda aka yi a gaban Shugaba Muhammadu Buhari a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja a ranar Litinin.
 
Rahoton shugaban na ICPC ya faɗa ƙarara cewa: “binciken farko ya nuna cewa wani ɓangare na kuɗi naira biliyan 2.67 an kautar da su zuwa asusun wasu mutane. Kuma (binciken) ya nuna cewar wani babban ma’aikacin Ma’aikatar Aikin Gona (mun ɓoye sunan sa), wanda yanzu ya rasu, shi da wasu aminan sa, sun sace sama da naira biliyan 2.5.”
 
Mai ba Minista Sadiya shawara kan harkokin watsa labarai, Madam  Nneka Ikem Anibeze, ta ce wasu magulmata sun murɗa bayanin na shugaban ICPC, su ka yi masa muguwar fassarar cewa wai akwai hannun Minista Sadiya a cikin lamarin sace kuɗin.
 
Ta ce ministar ta na mai sanar da duniya cewa shirin ciyar da ‘yan makaranta na Gwamnatin Tarayya da ake magana a kan sa ya bambanta da shirin ma’aikatar ta na ciyar da ‘yan makaranta wanda wani sashe ne na shirin ta na inganta rayuwar al’umma.
 
Kuma ta yi nuni da cewa shirin ciyarwar da ake bincike a kai shi ne wanda ake ciyar da ɗaliban da ke  kwalejojin Gwamnatin Tarayya da ke faɗin ƙasar nan, kuma ba a ƙarƙashin Ma’aikatar Harkojin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ya ke ba, domin ita ta kula ne da shirin ciyar da ‘yan makarantar firamare ‘yan aji 1 zuwa 3 a makarantun gwamnati da ke ƙasar nan.
 
Ta ƙara da cewa ba ma’aikatar ta ko ita ce ta ke kula da wancan shirin da ake kira “Home Grown School Feeding” ba. 
 
A cewar ta, ko kaɗan kuɗin shirin ba su biyo ta  hannun ta ko ta ma’aikatar ta ba.
 
Ta ƙara da cewa kuɗi sama da naira biliyan biyu da rabi da ake cewa wani babban ma’aikaci da abokan sa sun zaftare, abin ya faru ne a wata ma’aikatar daban, ba Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ba.
 
Ta ce dukiya ta kimanin naira biliyan 16 da ICPC ta karɓe daga cikin kuɗin da aka sace ɗin a waccan ma’aikatar, waɗanda aka ce an saka su a asusun wasu mutane ba don gudanar da aikin da ya shafi gwamnati ba, ba a Ma’aikatar Harkokin Agaji ba ne.
 
Ma’aikatar ta ce waɗanda su ke zagi ko sukar Sadiya Umar Farouq a kan wannan batun, su na dai yi ne saboda tsana da kuma nuna mata rashin adalci. 
 
Ta yi kira ga hukumar ICPC da ta wallafa sunayen dukkan mutane da kwalejojin Gwamnatin Tarayya da shugabannin makarantun da ake zargi da sa hannu cikin wannan almundahana, kuma a rufe asusun bankin su inda su ka ɓoye kuɗin.
 
Saboda haka ma’aikatar ta na  kira ga dukkan jama’a da su yi watsi da wancan rahoton ƙaryar da wasu ke yaɗawa, domin kuwa ko kaɗan babu hannun ministar a wannan shirin na ciyar da ɗaliban kwaleji.

Loading

Previous Post

Zaɓen Ondo: INEC na neman tallafin sarakuna don cimma nasara

Next Post

Shugaban ICPC ya ce babu hannun Minista Sadiya a wawurar biliyan N2.7

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Hagu zuwa dama: Hajiya Sadiya Umar Farouq da Farfesa Bolaji Owasanoye

Shugaban ICPC ya ce babu hannun Minista Sadiya a wawurar biliyan N2.7

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!