• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, November 3, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen Ondo: INEC na neman tallafin sarakuna don cimma nasara

by DAGA WAKILIN MU
September 25, 2020
in Nijeriya
0
Hedikwatar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa a Abuja

Hedikwatar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa a Abuja

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi kira ga sarakunan gargajiya a Jihar Ondo da su taimaka wajen ganin masu zaɓe sun tabbatar da zaman lafiya da bin ƙa’idojin kare kai daga annobar korona a zaɓen gwamna da za a yi a jihar a ranar 10 ga Oktoba.
 
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya yi wannan kiran a ranar Alhamis lokacin da ya yi wani zama a garin Akure da sarakunan da ke jihar kan batun zaɓen.
 
Yakubu ya ce an zo taron ne domin a nemi goyon bayan sarakunan don su ja hankalin talakawan su kan buƙatar da ke akwai ta tabbatar da zaman lafiya da guje wa tashin hankali a dukkan tsawon lokacin da za a yi zaɓen da ma bayan zaɓe.
 
Ya ce: “A taƙaice, mu na neman tallafin ku ne ta hanyoyi uku. Na farko, ku ci gaba da kira ga jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da magoya bayan su da su rungumi zaman lafiya, kamar yadda ku ka saba yi, a yankunan ku.
 
“Na biyu, ku yi kira ga al’ummar ku da su bi ƙa’idojin kare lafiyar su da ta jama’a daga kamuwa da cuta.
 
“Wannan zaɓe ne da za a yi shi a zamanin da ake fama da annobar cuta a duk duniya – wato annobar cutar korona. Ya na da muhimmanci ga masu zaɓe su kaɗa ƙuri’ar su kuma su tafi gida ba tare da ɓata lokaci ba.
 
“Na uku, mu na neman addu’ar ku don a samu zaman lafiya a Jihar Ondo. Kuma mu na neman addu’ar ku ga INEC don zaɓen da za a yi a ranar Asabar ya kasance cikin lumana da adalci, kuma ba tare da nuna bambanci ba, sannan ingantacce.
 
“Zaɓen Ondo ya yi kyau. Mun duƙufa wajen ganin cewa na Ondo ma ya fi shi. Mun yi hakan a  2016. Wannan hukumar ta yi wancan zaɓen duk da fargabar da lulkiɓe zukata kafin zaɓen.
 
“Ya na daga cikin zaɓuɓɓuka mafi kyau da hukumar ta gudanar ta yadda ya kasance shi kaɗai ne zaɓen gwamna da aka yi a tarihin Jihar Ondo tun daga 1999 wanda ba a je kotu kan sakamakon sa ba.”
 
Farfesa Yakubu ya ce a yayin da ake gudanar da zaɓen a zamanin cutar COVID-19, INEC ta na ƙoƙarin ganin an yi shi lafiya lau, bisa shawarar Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Cutar Korona da Cibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Nijeriya.
 
Ya ce, “INEC za ta samar da takunkuman fuska, gilasan fuska, magungunan mantaleta da auduga saboda share injinan karanta katin zaɓe masu aiki da ƙwaƙwalwa a duk lokacin da aka tantance wani mai zaɓe, kuma za a samar da maganin fesawa a hannu.
 
“Kwamitin Shugaban Ƙasa kuma ya taimaka mana da na’urar auna ɗumin jiki da za a yi amfani da ita a kowace rumfar zaɓe.
 
“Duk da haka, a duk inda aka samu wani mai zaɓe ko ma’aikacin INEC ko jami’in tsaro ya nuna alamun kamuwa da cutar, to mun shirya da ‘yan Kwamitin Shugaban Ƙasa da ‘yan rundunar yaƙi da korona na Jihar Ondo su yi saurin ɗauke wannan mutum zuwa cibiyoyin su inda su ke aje masu fama da cutar don a ba su magani.
 
“Daga darasin da na koya a Jihar Ondo, na ga cewar mutane ba su kula sosai da bada tazarar da aka ce su riƙa ba junan su. 
 
“Mun yi amanna da cewa ku sarakuna masu martaba za ku iya taimaka mana wajen yin amfani da ƙarfin muryar ku ku yi kira ga jama’a da su bi muhimman ƙa’idojin kiyaye lafiya.
 
“Hakan zai ƙarfafa saƙon da mu ka bayar cewa ba za a yarda wani mai zaɓe ya yi zaɓe ba har sai ya saka takunkumin fuska. Babu takunkumin fuska, babu yin zaɓe.”
 
Shugaban ya  tabbatar wa da sarakunan cewa hukumar sa ta shirya sosai domin gudanar da zaɓen, ya na mai jaddada cewa INEC za ta kiyaye dokar ta ta ƙin nuna bambanci ga kowa a zaɓen kuma za ta yi aikin ta kamar yadda doka ta tanadar.
 
Ya ce, “Masu zaɓe a Jihar Ondo kaɗai ne za su yanke hukunci kan wanda zai zama gwamnan su na nan gaba a ranar Asabar, 10 ga Oktoba.”
 
Tun da farko a nasa jawabin a taron, Oba Frederick Akinruntan, wanda shi ne Olugbo na Ugbo kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta Jihar Ondo, ya yaba wa shugaban na INEC da ita hukumar kan aikin da su ka yi a zaɓen gwamnan Jihar Ondo.
 
Daga nan Akinruntan ya yi kira ga hukumar da ta yi irin wannan aikin a Jihar Ondo wajen tabbatar da cewa an yi zaɓen cikin nuna rashin fifiko ko wariya, kuma cikin inganci.
 
 

Loading

Previous Post

Minista Sadiya ta jajanta wa jama’ar Kogi kan fashewar tanka

Next Post

Cewar Minista Sadiya: Ba hannu na a ɓacewar kuɗin ciyar da ‘yan makaranta

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Hajiya Sadiya Umar Farouq

Cewar Minista Sadiya: Ba hannu na a ɓacewar kuɗin ciyar da 'yan makaranta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!