SHUGABAN Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi kira ga ma’aikatan hukumar da su tabbatar da cewa sun ci gaba da aiki tuƙuru tare da tsare gaskiya don samun irin nasarar da su ka yi a Jihar Edo kwanan nan a zaɓen da za a yi ran Asabar ɗin nan a Jihar Ondo.
A saƙon da ya miƙa ga ma’aikatan hukumar ran Alhamis don ƙara masu ƙwarin gwiwa, shugaban ya ce, “Tilas ne mu jaddada nasarar da mu ka samu kwanan nan don tabbatar da cewa kowace ƙuri’a da aka kaɗa a ranar 10 ga Oktoba ta yi amfani wajen tabbatar da cewa wanda mutane su ka zaɓa shi ne ya ci zaɓen.
“Saboda haka ina kira a gare ku baki ɗaya da ku guji duk wani kwaɗayi, ku tabbatar dukkan abin da ku ka yi ya na kan doka da kuma tsoron Allah.
“Ko yaushe ku tuna da cewa duk wani abu da wani ma’aikacin INEC ya aikata zai iya shafar dukkan mu.
“Ku kasance cikin shiri da riƙe gaskiya kuma ku sadaukar da kan ku ga manufofi da burin Hukumar.”
A saƙon nasa, shugaban na INEC ya ce: “Kamar mako uku da su ka gabata, ana gobe za a yi zaɓen Gwamnan Jihar Edo, na yi kira ga ma’aikatan Hukumar nan masu aiki tuƙuru da su maida hankali wajen ganin sun bi hanyar gaskiya, mai nagarta, kuma bisa tsarin da mu ke da shi.
“Tabbas, ma’aikatan mu, tare da taimakon hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da nasara a wajen zaɓen.
“A bayyane ya ke cewa ‘yan Nijeriya da abokan Nijeriya sun yi murna da sakamakon zaɓen, kuma mun samu ƙwarin gwiwa daga yabon da su ka yi mana.
“Duk da haka, kada mu kuskura mu yi sanyi a aikin mu. Ga wani zaɓen Gwamna ɗin ya zo mana. Yanzu an ma fi saka ido a kan Jihar Ondo. Tilas ne mu jaddada nasarar da mu ka samu kwanan nan don tabbatar da cewa kowace ƙuri’a da aka kaɗa a ranar 10 ga Oktoba ta yi amfani wajen tabbatar da cewa wanda mutane su ka zaɓa shi ne ya ci zaɓen.”
A ƙarshe, Farfesa Yakubu ya yi godiya a gare su saboda ƙoƙarin su.