• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

ZPreety: Babban buri na shi ne…

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
October 10, 2020
in Taurari
0
ZPreety: "Asali ba fim na ke son yi ba"

ZPreety: "Asali ba fim na ke son yi ba"

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
ZULAIHAT Abdullahi (ZPreety) matashiyar mace ce wadda Allah ya ba basirar iya wasan kwaikwayo ta sigar da ba kowace jaruma za ta iya ba, wato ban-dariya. A wannan fage ta yi fice a cikin ƙanƙanen lokaci, wanda ya sa ta kasance ɗaya daga cikin jaruman da ake ji da su a Kannywood yanzu. Sai dai abin mamaki shi ne ta bayyana wa mujallar Fim a cikin wata tattaunawa ta musamman cewa ita fa tun farko ba ta da sha’awar harkar fim, kuma ba fim ya kawo ta industiri ba. Shin me ya kawo ta? Sannan menene babban burin ta na rayuwa a yanzu?
 
Ban da sana’ar fim, kwanan baya kuma sai aka ga kyakkyawar jarumar ta buɗe shago na sayar da kayayyaki. Shin me ya sa ta yi hakan? Za ta daina fim ne?
 
Sannan ina batun yin aure ya kwana? Ko ya na cikin ajandar jarumar kuwa?  
 
Duk za ku amsoshi a wannan tattaunawar da ZPreety ta yi da wakilin mujallar Fim, Muhammad Lawan Rano:
 
FIM: Wai shin wacece Zulaihat Abdullahi?
 
ZPREETY: Assalamu alaikun wa rahmatullah. Da farko dai suna na Zulaihat Abdullahi, wacce aka fi sani da ZPreety. Ni dai an haife ni a 1997. Na yi rayuwa ta a Legas, wanda aiki ne ya kai mahaifi ma can. Kazalika mu ka dawo Abuja, daga nan kuma mu ka dawo Kano. 
 
Sannan na yi makarantar firamare, sakandire, da ma ta gaba da sakandire, inda na je na yi N.C.E.
 
Daga nan kuma na je garin Zariya na yi digiri na a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU).
 
FIM: Menene ya ja ra’ayin ki ki ka shiga harkar fim? 
 
ZPREETY: Ba abin da ya ja ra’ayi na sai dai irin yadda ake faɗakarwa a diramance, wato yadda ake nuna wa mutane ga abin da ya kamata, ga yadda duniya ta ke ciki, ga yadda ya kamata a sarrafa wannan abin zuwa wannan. 
 
Sannan tun asali ma ba fim na ke son yi ba tun farko, gaskiya ‘modelling’ na ke so, kamar na dinga ‘advertisement’, wato na dinga tallace-tallace, irin tallar motoci, wayoyi, kayayyaki, ko menene, ko ma wane abu ne ƙarami wanda ake tunanin ba zai je wani guri ba aka ba ni tallar shi to zan yi. Da man shi ne na ke da buri, ba wai fim ba, tunda ka ga mafi akasari idan ka na so ka zama ‘model’, wato mai tallace-tallace, mafi sauƙi shi ne ka fara yin fim, to idan ka fara yin fim za ka samu dama sosai wanda idan aka ga ka fara yin fim ka zama ‘superstar’, wato sananniya, shi zai ba ka dama a dinga kiran ka ka na tallace-tallace ta ko wanne fanni.
 
FIM: Ga shi kin samu nasarar buɗe shago. Shin me ya ƙunsa?
 
ZPREETY: Shago na na ‘ZPreety Collection’, idan aka ce ‘collection’ ya ƙunshi abubuwa da dama kamar kayan maza, kayan mata, English wears, takalmi, ɗankunne, agoguna, turare, man shafawa, jallabiyoyi, hijabai da sauran su. Abubuwa ne dai da dama na ke sayarwa.
 
FIM: Ban da wannan shagon, ki na da rassan shi a wasu jihohin?
 
ZPREETY: A’a, ba ni da wani reshe sai wannan da ya ke a garin Sokoto.  Amma ina da burin  na sa a fara neman min wani wurin a garin Kano da Kaduna inda na ke so na buɗe wani reshen, in-sha Allahu.
 
FIM: Tun bayan buɗe shagon, ya ki ke ganin karɓuwar sa a gurin al’umma?
 
ZPREETY: E, tun a lokacin da na buɗe shagon ma, tun kafin a fara ‘posting’ ɗin abubuwan da ke cikin shagon, mun zo mun ɗauki shagon a hoto ba komai a ciki, da dai kayayyakin da mu ka ɗan gwada sawa haka, mutane su ka dinga ƙorafin yaushe za a buɗe, yaushe za a bude. 
 
Akasari ma abubuwan da mu kai ‘posting’ wanda mutane su ka saya tun kafin mu buɗe ne. Amma duk da ba a so buɗewa ba sai an yi addu’a, sannan kuma boss (wato oga na) ya zo, wato Adam A. Zango, sannan a yi bikin buɗewa. Sai kawai mu ka ga mutane sun matsu a zo a buɗe shagon saboda su fara sayayya. Sai kawai aka sauke Alƙur’ani na kwanaki biyu, sannan aka buɗe shagon. Gaskiya kuma ya samu karɓuwa, sannan an samu duk wani abu  da ake so.
 
Burin Zulaihat shi ne ta zama babbar ‘yar kasuwa, kuma ta riƙa taimakon jama’a
 
FIM: Kamar yadda aka sani, kowanne irin kasuwanci da matsaloli irin nasa. Waɗanne irin matsaloli ki ke fuskanta zuwa yanzu?
 
ZPREETY: Gaskiya duk abin da mutum ya ke yi dole ya samu ƙalubale, kuma ƙalubalen da na samu dai na buɗe shago to wasu mutanen idan sun zo sayen kaya su ka tarar ba na nan sai su ce ba sa so su sayi kayan sai ina cikin shago. Shi ne kawai ƙalubalen. Ka ga dole kenan in kasance a cikin shago lokaci zuwa lokaci, ko da a ce na zo na tafi, mutane dai su san ni ce na zo.
 
FIM: To me ya sa ba sa so su saya in ba kya nan tunda ga kayayyakin a cikin shago?
 
ZPREETY: Ko ba don wani abu ba, wani dai ya na so ya gan ni ya sayi kaya mu yi hoto da makamancin haka. Ka ga sai dai hamdala kawai saboda kasuwancin ana samun duk wani abu da ake so. An fara kaɗan amma yanzu in ka ga yadda gurin ya ke, ba ƙaramin guri ba ne.
 
FIM: Menene burin ki a kan wannan kasuwancin naki?
 
ZPREETY: Yanzu buri na shi ne wannan kasuwancin nawa ya faɗaɗa, na buɗe rassa daban-daban a cikin jihohin ƙasar nan. Ban ƙi ma a ce jihohi ashirin da tara na Najeriya duk ina da reshe ba! (Dariya)
 
In na buɗe kuma, ɗaya burin nawa shi ne in dinga fita ƙasashen waje irin su Dubai, Chaina da Amerika dai duka haka, in rinƙa ɗauko kaya daga can in Allah ya yarda. Shi ne babban buri na: Allah ya buɗa min in ga yadda zan dinga taimaka wa mutane da dama game da kasuwanci na. Wanda su ke buƙatar taimako irin in buɗa masu hanyoyi ko da kaɗan ne, irin su fara samun nasu na kan su, in Allah ya yarda.
 
FIM: A ɓangaren fim, har yanzu ki na taka rawa a matsayin jaruma? Ko kin koma harkar kasuwancin naki baki ɗaya?
 
ZPREETY: A’a,  gaskiya har yanzu ina taka rawa a Kannywood sosai saboda an ce taɓa kiɗi taɓa karatu. Na dai ɗan yi wani tunani to ai ba a fim ya kamata a ce na tsaya ba tunda dai abin buɗi ne daga Allah; ya kamata ni ma in buɗe nawa fannin kasuwanci irin haka. So, ina shago kuma wani lokacin idan an kira ni aiki zan tafi in yi aiki na sannan in sake dawowa shago na in zauna. So, ai duk buɗin Allah ne. (Dariya)
 
FIM: Tun shigowar ki Kannywood, an san ki da harkar  ‘comedy’, wato wasannin kwaikwayo na barkwanci. Har yanzu ki na wannan fannin ko kin ajiye shi a gefe?
 
ZPREETI: Ƙwarai kuwa, duk lokacin da na ji a rai na ana wani yanayin da aka samu matsala ko kuma wani abu na faruwa, to zan fito in yi magana da waya ta  in nishaɗantar kuma in isar da saƙo. To wannan gefen ‘comedy’, ina yin shi saboda ai wani fage ne na isar da saƙo. So ina yin shi gaskiya.
 
FIM: A kwanan baya an ji cewa kin kwanta wani rashin lafiya wanda har ya sa ki ka koma gida jihar ku Kebbi. Shin yanzu kin warke ne sosai?
 
ZPREETY: A’a, gaskiya da man ban yi wani ciwo ba; lafiya ta ƙalau. Duk ce-ce-ku-ce ne irin na mutane wanda kowa ya ke faɗa in ya ji shiru ko kuma wani abu sai a ɗauko wani abu a ɗora ma. Amma ni lafiya ta ƙalau na ke wallahi. Alhamdu lillah.
 
FIM: Idan mu ka dawo batun zamantakewa kuma, za mu so mu ji shin wai ZPreety na da aure?
 
ZPREETY: Ita dai ZPreety gaskiya ba ta da aure, amma akwai ƙudiri da niyya a cikin zuciya, so, Allah ya tabbatar min da alheri kuma Allah ya bayyana min miji nagari mai so na kuma ni ma wanda na ke son sa. Ina kuma da niyyar yin aure; a ko yanzu na samu miji, in dai hankali na ya kwanta a kan sa, zan yi aure in-sha Allahu. Ka san komai nufi ne na Ubangiji.
 
ZPreety, kamar yadda laƙabin ta ya nuna, kyakkyawa ce
 
FIM: Akwai wani albishir da ki ke da shi ga masoyan ki?
 
ZPREETY:  Masoya na inai masu albishir da ci gaba da jiran finafinai na. Akwai sabbi wanda za su fito kwanan nan, akwai kuma wanda na daɗe da yin su, su ma na san su na kan hanyar fitowa. Akwai kuma waɗanda yanzu haka ina nan ina taka rawa a kai.
 
Sannan kuma su ci gaba da haƙuri da ni; inda su ka ga ban yi daidai ba a yi min afuwa. Ina godiya gare su.
 
FIM:  A ƙarshe, menene fatan ki ga kasuwancin ki da ma harkokin ki na finafinai?
 
ZPREETY: Fata na shi ne Allah ya ci gaba da rufa mana asiri, ya ƙara mana buɗi da hanyoyin samun mu, ya kuma biya mana buƙatun mu na alkhairi. Allah kuma ya ba ni damar taimaka wa duk wanda ya ke kusa da ni, wanda bai da shi, da ma wanda ya ke neman ƙari.
 
Sannan Allah Ubangiji ya tabbatar min da alkhairi, shi ne kawai in gama da duniya lafiya.
 
Fim: Mu na godiya.
 
ZPREETY: Ni ma ina godiya.

Loading

Previous Post

Shugaban INEC ya na so ma’aikatan hukumar su jajirce a zaɓen Ondo

Next Post

Gaskiyar dalilin cire Safara’u daga ‘Kwana Casa’in’

Related Posts

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan
Taurari

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan

August 24, 2025
Jaruma Hauwa Musa Adam
Taurari

Ina son zama mai taimakon al’umma — jarumar Kannywood Hauwa Musa Adam

August 14, 2025
Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Next Post
Safiya Yusuf (Safara'u)

Gaskiyar dalilin cire Safara'u daga 'Kwana Casa'in'

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!