ƊAN takarar zama gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar APC a zaɓen 2023, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ya sha alwashin zai yi kyakkyawar tafiya tare da ‘yan fim idan ya zama gwamnan jihar a zaɓen da za a yi a baɗi.
Gawuna, wanda shi ne mataimakin gwamnan jihar a yanzu, ya bayyana haka ne lokacin da wasu gamayyar ‘yan fim da mawaƙan Kannywood su ka kai masa ziyara a daren shekaranjiya Litinin domin yin mubaya’ar su a gare shi tare da nuna goyon bayan su ga takarar sa.
‘Yan Kannywood ɗin sun kai ziyarar ne domin tabbatar masa da cewar su na tare da shi a tafiyar siyasar sa kuma su na da ƙudirin tallata shi domin ganin ya samu nasara a zaɓen.

A yayin da ya ke mayar da jawabi a gare su, Gawuna ya nuna farin cikin sa kan goyon bayan su da ya samu, kuma ya yi alƙawarin idan aka samu nasara a zaɓen za a dama da su saboda yadda su ka bayar da gudunmawar su ga tafiyar tasa.
Tawagar ‘yan fim ɗin, a ƙarƙashin jagorancin Shu’ibu Yawale da Kabiru Maikaba, ta ƙunshi jarumai irin su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Abdul Amart, Sadiq Mafiya da Momee Gombe da kuma mawaƙa irin su Naziru M. Ahmad, Ado Isa Gwanja da Hamisu Breaker.
Tuni dai ‘yan Kannywood kowa ya fara laluben makomar sa da kuma ɗan takarar da zai bi a kakar zaɓe mai zuwa, don haka kowanne ya ke neman hanyar da ya ke ganin za ta ɓulle masa.
