• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, October 15, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tarayya ta haramta sanya waƙar ‘Warr’ ta Ado Gwanja a gidajen rediyo da talbijin

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
September 7, 2022
in Labarai
0
Gwamnatin Tarayya ta haramta sanya waƙar ‘Warr’ ta Ado Gwanja a gidajen rediyo da talbijin
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Gidajen Rediyo da Talbijin ta Nijeriya (Nigerian Broadcasting Corporation, NBC) ta haramta sanya waƙar ‘Warr’ ta Ado Gwanja a dukkan gidajen rediyo da talbijin da ke ƙasar nan.

Ofishin shiyyar Kaduna na hukumar ne ya bayyana hakan a cikin wata takardar sanarwar da ya bayar mai ɗauke da kwanan wata 6 ga Satumba, 2022.

Hukumar ta ce ta lura da cewa waƙar ta karaɗe gidajen rediyo da talbijin a faɗin arewacin ƙasar nan, sannan akwai yiwuwar masu gidajen kafafen yaɗa labarai ma ba su saurare ta da kyau ba domin kuwa ta na ɗauke da wasu kalamai na rashin ɗa’a a cikin ta.

Shafin farko na takardar haramcin ‘Warr’ da NBC ta bayar

“Waƙar na nuna cewa shan kayan maye karɓaɓɓen al’amarin rayuwa ne,” inji hukumar.

Ta ci gaba da ba da misalan wasu kalmomi da waƙar ta ƙunsa kamar haka:

“…kafin a san mu ai mun ci ƙashin uban mu…”

“…Za ni zo bari in shafa hoda, ko kin zo da ke da hodar ki uban ki zan ci, warr…”

“…Kowa ya ce zai hana mu uban sa zan ci…”

Hukumar ta ce: “Bidiyon waƙar na nuna shan giya kai-tsaye, wanda hakan ya saɓa wa sashe na 3.18.2 (c) da na 3.9 na dokar yaɗa bayanai ta hanyar rediyo da talbijin da ta ce, ‘Gidan rediyo ko talbijin ya tabbatar da cewa wajen watsa bayanai ta kafar sa ya nuna kyakkyawan hali’.”

Mujallar Fim ta riga ta ba da labarin yadda wata kotun shari’ar Musulunci da ke Jihar Kano da kuma Sufeto-Janar na ‘yan sanda su ka ba da umarnin ‘yan sanda su binciki Ado Gwanja kan wannan waƙar da ma ɗayar da ya rera mai suna ‘Chass’.

Loading

Previous Post

Siyasar 2023: Zan yi kyakkyawar tafiya da ‘yan Kannywood idan na zama gwamnan Kano, inji Gawuna

Next Post

Cewar mawaƙi Gwanja: Dalili na na yin ‘hotunan aure’ da jaruma Momee Gombe

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Ado Gwanja da Momee Gombe a matsayin ango da amarya

Cewar mawaƙi Gwanja: Dalili na na yin 'hotunan aure' da jaruma Momee Gombe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!