FITACCEN mawaƙi Ado Isa Gwanja ya faɗa wa mujallar Fim dalilin sa na yin “hotunan aure” tare da jaruma Momee Gombe, wanda ya haifar da surutai a soshiyal midiya.
Kwana biyu da su ka gabata ne mawaƙin kuma jarumi ya ɗora hotunan guda biyu a Instagram, inda aka gan shi tare da jarumar a yanayi irin na hotunan amarya da ango kafin auren su (prewedding pictures).
Gwanja da Momee sun nuna kamar aure ne za su yi, domin a ƙasan hoton ya rubuta ‘Time’, ma’ana Lokaci, ita kuma da ta ɗora hoton sai ta rubuta, “Alhamdu lillah”.
Ɓullar hotunan ke da wuya sai duk soshiyal midiya ta ɗauka da magana, kowa na tofa albarkacin bakin sa a kai.
Wani abu da ya ƙara sanya wa mutane tunanin lallai aure ne za a yi shi ne yadda ‘yan fim su ka yi ta taya jaruman biyu murna, su na yi masu fatan alheri.
Mutane da dama sun ce lallai Gwanja ya darje da tsaleliyar mace wadda ta dace da maye gurbin matar sa da su ka rabu, wato Maimunat Ɗan’auta.
Wasu na cewa ashe ba zai daɗe a zaman tazuranci ba.

Tun a ranar da hotunan su ka ɓulla, mujallar Fim ta so jin gaskiyar maganar ta bakin jaruman, amma ba ta samu dama ba, sai a yau Ado Gwanja ya tabbatar mata da cewa hotunan fim ne.
Amma bai bayyana sunan fim ɗin ba.
Sai dai wasu masu sharhi kan hotunan sun ce tallar bidiyon waƙar ‘Chass’ ne Gwanja ke yi.
A baya, ‘yan fim sun sha yin irin waɗannan hotunan na fim ko waƙa domin su ja hankalin jama’a.
Ko a kwanan baya jaruma Zarah Diamond da mawaƙi Abba Harara sun yi irin waɗannan hotunan. Su ma su Ali Nuhu, Sani Musa Danja, Sadiq Zazzaɓi, Sadiq Sani Sadiq, Maryam Booth, Rahama Sadau da sauran su sun yi irin waɗannan hotunan, don haka ba sabon abu ba ne.
A wannan makon dai ana iya cewa Ado Gwanja shi ne tauraron kafafen soshiyal midiya da sauran kafafen yaɗa labarai.
![]()







