MAI Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa an ga watan Shawwal a Nijeriya, wanda hakan ya kawo ƙarshen watan Ramadan.
Ya bayyana hakan ne a sanarwar da ya bayar ta rediyo da talabijin a Sokoto a daren yau.
Ya ce: “A yau 29 ga Maris, 2025, wanda ya yi daidai da 29 ga Ramadan 1446AH mun samu rahotanni daga shugabannin Musulmi daban-daban da ƙungiyoyi, irin su Shehun Borno, Sarkin Dutse, Sarkin Argungun, Sarkin Daura da shugabannin also the leadership of JIBWIS a Jos na ganin sabon watan Shawwal na 1446AH. Saboda haka gobe 30 ga Maris wanda ya yi daidai da 1 ga Shawwal 1446AH kuma ranar Eid-el-Fitr.”