• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 18, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau

by IBRAHIM SHEME
November 27, 2024
in Marubuta
0
Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau

Daga hagu: Amrah Auwal Mashi, Zainab Muhammad Chubaɗo da Hajara Ahmad Hussain

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A CIKIN wasu taurarin rubutun onlayin guda uku — ɗaya budurwa, biyu matan aure – a yau za a fitar da gwarzuwar gasar rubutun mata ta Hikayata ta 2024 wadda gidan rediyon BBC Hausa take shirya wa mata.

Marubutan, wato Zainab Muhammad Chubaɗo, ’yar shekara 25 da haihuwa daga garin Kafanchan a Jihar Kaduna; da Amrah Auwal Mashi ’yar shekara 25 da haihuwa daga garin Mashi a Jihar Katsina, da kuma Hajara Ahmad Hussain, ’yar shekara 28, daga Haɗeja a Jihar Jigawa, sun zama zakaru ne bayan sun doke mata 13 a matakin ƙarshe na gasar.

A yammacin yau Laraba za a bayyana sunan gwarzuwar gasar da wadda ta zo ta biyu da ta uku a wurin wani ƙwarya-ƙwaryan biki da BBC Hausa za su shirya a otal ɗin Continental (Sheraton a da) da ke tsakiyar birnin Abuja.

Zainab ta shiga matakin ƙarshe da gajeren labari mai taken ‘Tsalle Ɗaya’, ita kuma Hajara Auwal Hussain ta hau matakin da labari mai taken ‘Amon ’Yanci’, yayin da Amrah Auwal Mashi ta kai matsayin da labari mai suna ‘Kura A Rumbu’.

Gasar ta bana ita ce ta tara da BBC Hausa ta shirya tun daga farkon gudanar da gasar a cikin 2016.

Gasar, wadda ɗaruruwan marubuta ke shiga a kowace shekara, ta matasan mata ce zalla, inda kowace marubuciya take zaɓar jigon da take so ta yi rubutu a kai.

Alƙalai uku waɗanda ba ma’aikatan BBC ba su ne suke zaɓar gwarzayen gasar na ƙarshe a bisa ƙa’idojin da BBC Hausa suka kafa.

A matakin farko ana fitar da labarai 30, daga nan sai a fitar da 12, sannan sai ukun da ake karramawa.

Mujallar Fim ta tattauna da gwarazan gasar na bana, inda kowacce ta bayyana farin ciki mai yawa kan nasarar da ta samu. Haka kuma sun bayyana tarihin su da rawar da suke takawa a fagen rubutu na wannan zamanin.

Zainab Muhammad Chubaɗo

Zainab, wadda ’yar shekara 25 da haihuwa ce, haifaffiyar Kafanchan ce a Jihar Kaduna.

Ta yi karatun firamare a Kano, ta yi na sakandare a GGSS Kafanchan inda ta gama a 2017, sannan ta shiga Kwalejin Horas Da Malamai ta Tarayya (FCE) da ke Kano, inda bayan ta gama sai ta shiga karatun digirin B.Ed a dai kwalejin, ƙarƙashin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Yanzu tana a shekarar ƙarshe ta karatun.

Da muka tambaye ta batun iyali, sai ta ce, “Ba ni da aure, kuma ban taɓa yi ba, amma zan yi idan lokaci ya zo.”

Zainab ta zama marubuciya “tun daga yarinta”, amma ta fara rubutu a 2015 sakamakon yawan karanta littattafan marubuta irin su Abdul’aziz Sani Madakin Gini wanda ta ce shi ne “ya busa wa mafarki na na zama marubuciya rai. Karanta littafan shi shi ne sila.”

Sunan littafin ta na farko ‘Bafulatana’, wanda ta wallafa a yanar gizo.

Ta rubuta littattafai aƙalla 12 a kan jigogi daban-daban, kuma dukkan su a onlayin suka fito.

Ta shiga gasar Hikayata har karo shida, daga 2018, amma faɗuwa ba ta sanya mata karaya a zuci ba saboda ita mai naci ce. Ta ce: “Gaskiya ban taɓa jin na karaya ba. Hasali ma dai ina da naci.”

Duk labarin da ta shiga da shi a baya bai taɓa shiga ko cikin 30 na farko da ake zaɓa ba sai a 2023 lokacin da ta fito cikin 15. “Wannan ya sa na ƙara zumma.”

Mahaƙurci mawadaci, a bana labarin ta ya kai matakin ƙarshe.

A kan jigon labarin, Zainab ta ce: “‘Tsalle Ɗaya’ na gina shi a kan wata matar aure mai ɗauke da ciki tsoho, wadda ta faɗa hannun masu garkuwa da mutane a ƙoƙarin ta na ceton kan ta da abin da ke cikin ta. Kuma cikin rashin sa’a ta ɓige da jifar gafiyar Ɓaidu – ita ba ta tsira ba, ita kuma ba ta samu ta gudu ba, sukai ram da ita.

“Labarin yana nuna juriya a kan bala’ira da kuma fafutuka ta ceton rai, sannan da soyayyar da ke dabaibaye da zuciyar uwa kan abin da ke cikin ta, ko ta haifa ko ba ta haifa ba.”

Matashiyar marubuciyar ta yi tsananin murnar kaiwa matakin ƙarshe.

A kan abin da ta sa a gaba a fagen rubutu kuwa, sai ta ce: “Gaskiya yanzu buri na da girma, amma dai ina son in zama shahararriyar marubuciyar da duniya za ta san ni, ba ma iya arewacin Nijeriya ba. Duniya gabaki ɗaya nake so ta shaida.

“Dama ce ka ga Allah ya bayar, saboda akwai mutane da dama da suke so su kasance a wannan matsayin, sai Allah bai ba su ba, sai ya ɗauko mu ya ba mu. Ka ga ba mun fi kowa ba ne ya ɗauko mu ya ba mu. Ya jiƙan mu ne; mun nema kuma ya taimake mu.

“Kuma (mutane) su sani cewa yadda suke ɗaukar yaren Hausa a banza, ba banzan ba ne ba, abu ne da zai iya cicciɓa mutum ya cimma nasarar da tunani bai taɓa zuwa wa mutum ba.”

Hajara Auwal Hussain

Hajara Auwal Hussain matar aure ce daga Haɗeja, Jihar Jigawa. Ta yi aure a cikin Afrilu 2010, yanzu ita da mijin ta suna da ’ya’ya biyar.

Shekarun ta na haihuwa 28.

Ta kasance mai karance-karancen littattafan ƙirƙira na Hausa tun tana ajin JSS3 a makarantar sakandare. A cikin 2015, lokacin an samu sauyin zamani a fagen rubutu, wato aka fara komawa onlayin, sai ta lura da yadda mata musamman suka raja’a wajen karance-karancen littattafan nishaɗi.

Ta ce: “Sai na ce to me zai hana tunda mata sun fi ɗaukar darasi a littattafai ni ma in fara yin rubutu? Sai na fara yin littafi na na farko, ‘Kowane Tsuntsu…’ To daga nan sai na samu mabiya, mutane suna son rubutun. To daga nan kuma aka ci gaba da fafatawa har zuwa wannan shekarar.”

Ita ma littatafan Abdul’aziz Sani Madakin Gini sun yi tasiri a kan ta, haka kuma na su Fauziyya D. Sulaiman da Sa’adatu Waziri Gombe, har ma na da irin sun Magana Jari, Iliya Ɗan Maiƙarfi, da sauran su.

Hajara ta sha cin gasar rubutu a baya, domin ta ci gasanni ƙanana da manya sun fi goma; ita ce gwarzuwar gasar rubutu ta Gusau Institute, Kaduna, a 2022, inda ta zo ta ɗaya da littafi mai suna ‘Ɗanyen Kasko’, wanda ta yi kan jigon yara mata-maza da ƙalubalen da suke fuskanta.

‘Ɗanyen Kasko’ shi ne kaɗai littafin ta da aka buga a takarda, sauran littattafan ta duk a onlayin suka fito.

Ta fara shiga gasar Hikayata a shekarar 2020, amma ba ta taɓa kaiwa kowane mataki ba.

Tare da dariya, ta ce Hikayata “ita ce gasar da ban taɓa hayewa na fito ko a cikin 25 ba. Sai na ce anya kuwa ana karanta labarai na?”

A kan nasarar kaiwa matakin ƙarshe da ta yi a bana, Bahaɗejiyar mai laƙabin ‘Hajjo Ikon Allah’ ta ce, “Shekarar da ta wuce ina fama da tunanin haihuwa ne ko rubutu? Kamar ma ba zan rubuta ba. Sai aminai da ƙawaye suna, ‘Ki rubuta, ki rubuta’. Sai na yi rubutu a kan jigon matan da suke barace-barace, waɗanda suka mai da bara dai sana’a. Shi ma haka labarin shiru, bai fito a talatin ba.

“Sai na ce kai, na karaya gaskiya! Ina ganin ban da rabo a gasar BBC; in da a ce ma ka fito a mataki na farko, ka ɗan fito a 25 ɗin, za ka sa rai wata rana za ka kai na farko. To sai a wannan shekarar na ga labari na ya fito a cikin 30.

“Ana ta, ‘Hajjo Ikon Allah!” Da yake ina tsokanar mutane da suna na Hajjo Ikon Allah. ‘Hajjo Ikon Allah, sunan ki ya fito a cikin talatin.’ Sai na ce, ‘O! Su Hajjo Ikon Allah, an taka leda, to alhamdu lillahi. Ko a haka dai na san BBC bana sun tuno da labari na. To sai ga shi na shigo cikin fifteen, har na shigo cikin uku. To alhamdu lillah.”

Da wakilin mu ya buƙaci ta faɗa masa maudu’in da ke cikin labarin ‘Amon ’Yanci’ da ya kai ta wannan matakin, sai ta ce: “Yana magana ne kan wata ɗaliba ’yar makaranta da take fafutikar sama wa jama’ar ta ’yanci saboda matsalolin da suka taru suka masu yawa, na yunwa, mace-macen aure, mutuwar yara ƙanana, rashin kuɗi, rashin aikin yi; ga ita kuma jarumar ’yar makaranta ce, gwamnati ta janye tallafin kuɗin karatu, to abin sai ya yi mata yawa.

“A haka sai ta ci karo da yadda matasa suka ha]a kai kan kai wa gwamnati koke. To sai sai ta ce ah, ita ma bari ta haɗa nata mutane. Sai ta haɗa tawagar mutane ɗari, matasa da tsoffi da mata da ’yan makaranta wanda suka rinjayi tawagar. Sai suka fita kaiwa koke.

“To kuma sai aka yi rashin sa’a, buƙatar ta ta suɓuce saboda wasu ɓatagari da suka shiga suka lalata kayan gwamnati. Ita kuma sai aka kama ta, wanda haka ya yi sanadiyyar zuwan ta kotu. Aka yi niyyar kai ta gidan yari saboda wannan matsalar a matsayin su na masu tunzura jama’a, suna zanga-zanga da ɓata dukiyar gwamnati. To wannan shi ne jigon da na shiga labari na da shi.”

Ta bayyana burin ta a fagen rubutu kamar haka: “Ina da burin nan gaba rubutu ya zame mani silar zuwa inda ba na tunani. Ina son sa}on da nake isarwa zuwa ga mutane ya zamana cewa abin da nake rubutawa suna aiki da shi. Sannan ina fata nan gaba labarin da nake rubutawa ya zama ba iya Hausa ba ya zama har Ingilishi yaren kowa yadda zai zagaye duniya, saƙon ciki ya amfani jama’a gaba ɗaya. Ina so silar labari na a samu sauye-sauye da abubuwa.”

Amrah Auwal Mashi

Amrah Auwal Mashi ma ba ɓoyayya ba ce a fagen rubutu, tana cikin taurari kuma zaƙaƙuran marubutan onlayin.

Haifaffiyar Mashi a Jihar Katsina, Amrah ta yi karatun firamare kuma ta fara na sakandare har ta kai JSS3 a Jihar Kebbi, sai iyayen ta suka sake dawowa Katsina. A nan ta kammala karatun sakandare a 2014, ta shiga Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua ta karanci Biology, ta gama a 2019.

“Sai muka dawo Kaduna da zama, daga nan na yi aure a Abuja. Ina da aure da yara biyu.”

Shekarun Hajiya Amrah dai 25 a duniya yanzu.

Dangane da yadda ta zama marubuciya, ta ce tun tana ’yar shekara 16 take rubutu.

Abin mamaki, ita ’yar gado ce a fagen domin kuwa ta ga mahaifiyar ta tana yin rubutun ƙirƙira, shi ne ita ma ta ɗauka.

A cewar ta: “Mama na takan samu littafi ta yi rubutu kan abin da yake damun ta ko in ta je wani wuri ta ga abin da ya faru, za ta samu littafi ta rubuta. To, a shekarar da na gama sakandare, 2014, ana jiran admission a jami’a, ba a kai ga an samu ba, sai na ɗauko wani littafi ɗaya cikin waɗanda ta rubuta, ba ta yi mashi suna ba. A lokacin na ga an ɗan fara rubutun onlayin, bai yi yawa ba. Sai na ɗauko wannan littafin ɗaya nata, sai na yi mashi suna da ‘Mahaƙurci’.”

A kan batun ta yi gado kenan, sai ta ce, “E, haka zan ce, duk da dai ba ta taɓa fitarwa ba, za ta rubuta ne kawai ta aje, ni kuma da ta rubuta sai na ɗauka, ina ɗan fitar da shafi ɗaya sai na ga ya samu karɓuwa, ana ta, ‘A turo cigaban shi.’ Sai na ce, ‘A’a!’ Kawai sai na ɗauka na ci gaba da rubutawa.”

Littafin Amrah na farko sunan sa ‘Yaudara’, wanda ta rubuta kan yadda samari suke yaudarar ’yanmata.

Ta ce: “Abin ya faru a kan wata ƙawa ta, ta kira ni tana ta kuka, daf da za a yi auren su ma, bayan mun gama secondary school, ya yaudare ta. Ashe akwai wasu ’yanmatan da yawa da yake mu’amala da su, mu’amala ma ba mai kyau ba, wanda asirin shi ya bayyana, iyayen ta suka ce a fasa auren. Ta sha kuka, ta shiga damuwa.

“Sai na yi sha’awar wannan abin da ya faru da ita in yi rubutu a kan shi, ba wai exactly abin da ya faru da ita ba, makamancin dai abin… Daga nan kawai sai na ji sha’awar na ci gaba da rubutu.”

Amrah ta rubuta littattafai aƙalla akalla 30, waɗanda duk an yaɗa su a onlayin.

Ta ce tana yin rubutun onlayin ne saboda “hankalin kowa a onlayin yake. Su ma na da ɗin ana sake ɗauko su ana dawo da su onlayin.”

Ta fara shiga gasar Hikayata a 2024, kuma wannan shi ne karo na takwas cikin tara da ta shiga.

Ta ce: “2016 da aka fara shekaru na ba su cika 18 ba. Sai a 2017 ina da shekaru 18 cif-cif sai na shiga. Don ban san kan rubutun ba, ban san cewa akwai wasu applications da suke ƙirga adadin kalmomi ba. Ni na zauna ɗaya bayan ɗaya na dinga ƙirga kalmomin nan! Na yi na ga ba su kai dubu ɗaya ba, kuma an ce ƙaranci dubu ɗaya, kada ya haura 1,500. Na ƙara, na tisa ƙirga. Ta haka dai, na yi na aika. Sai ban dace ba.

“Sai a 2018 ana sakin sakamako, lokacin shekaru na 19, sai na gan ni a cikin 30. Daga nan sai ga ni a cikin 12, aka karanta labari na. Lokacin ma gidan mu ba a san ina rubutu ba, sai da baban mu yai ta amsa kiran wayar an ji wata ɗiyar sa a BBC an karanta littafin ta.

“Ya kira ni ya ce, ‘Ke ya aka yi?’ Na ce, ‘Ai Baba…’ Ya ce, ‘Ai ba a shiru, wannan abin alkairi ne, ba abin ki shiru ba ne.’ To tun daga nan sai na ci gaba da yi tare da goyon bayan su.”

A kan yadda ta riƙa ji saboda rashin samun nasara a gasar a baya, marubuciyar Bakatsina ta ce: “Gaskiya ba na jin da]i duk da yake cikin karo takwas ɗin nan wani lokaci zan shiga talatin. Yanzu haka ina da satifiket. Karo biyu kenan ina shiga 12, an karanta labari na.

“Ina jin ba daɗi. Don gaskiya waccan shekarar da babu ni cikin 30 ɗin nan har da ƙwalla sai da na yi! Na shiga ɗaki. Na ga na zo a 2022 na samu an karanta nawa cikin 12, na shiga tare da hope shekarar gaba in samu ɗaukaka, sai na ga babu ni a talatin. Sai na sare, na ce ma ba zan ƙara shiga ba.

“Lokacin na koma gida, bayan na haihu ne, sai mahaifiya ta, da ta ji sanarwar BBC za ta ce, ‘Wai ke wance kin rubuta naki ne?’ Sai na ce, ‘Ni fa na ce ba zan ƙara shiga ba.’

“Haka shi ma maigida na daga nan Abuja, da ya ji sanarwar zai kira ni ya ce, ‘Wai kin rubuta kuwa? Sun kusa rufewa!’ Na ce, ‘Ni fa na ce ba zan shiga ba.’

“To a haka dai da ƙwarin gwiwar su, suna ta ce min in daure in shiga, kawai dai irin da babu gara ba daɗi, na dai shiga a kan da rashin tayi akan bar arha. Sai kuma ga shi Allah ya sa a bana rabon yake.

Amrah ta bayyana mana abin da labarin ‘Kura a Rumbu’ ya ƙunsa: “A kan matan aure da suke tu’ammali da mazajen waje ta hanyar wayar hannun su, irin wanda suke raina samun mazajen su. Sai su rinƙa mu’amala da wasu mazajen waje. To a kan haka na yi shi, inda har ta afka ga wani ƙasurgumin ɗan garkuwa da mutane. Ita ba ta sani ba, ashe fansa ya zo ɗauka saboda mijin ta ɗan sanda ne mai ƙaramin mu}ami. Ya zo ɗaukar fansa ita ba ta sani ba, yana mata aman kuɗi. Har ta yarda da shi za su haɗu da rana.”

Marubuciyar ta bayyana cewa ta yi ɗimbin farin ciki lokacin da Malam Usman Minjibir na BBC Hausa ya kira ta a waya ya fa]a mata cewa ta kai matakin ƙarshe a gasar. Ta ce, “Ina kusa da ’yar’uwa ta ya kira ni, ina jin haka na ce, ‘Halima, BBC, shi kenan na haye!’ Na yi farin ciki gaskiya. Zan ce farin cikin da na yi, kwatankwacin shi sadda mahaifi na ya biya min aikin Hajji.”

Yanzu dai kowa ya zuba ido ya ga yadda za ta kwashe a yammacin yau, wato a wacece gwarzuwar gasar Hikayata ta bana, da mai take mata baya, da kuma mai bi masu. Hausawa dai sun ce ba a san maci-tuwo ba sai miya ta ƙare.

Loading

Previous Post

KILAF AWARD 2024: Rana ta 2

Next Post

Yanzu an wuce matakin gaba da Ninanci, inji Farfesa Abdallah Uba Adamu

Related Posts

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 
Marubuta

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 

January 1, 2025
Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 31, 2024
‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 20, 2024
Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai

November 30, 2024
Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa
Marubuta

Gasar rubutu: Hukumar Tace Finafinai ta bayyana gwaraza 50 na zagayen farko

November 24, 2024
Buri na in auri marubuci ɗan’uwa na, inji marubuciya Gimbiya Rahama
Marubuta

Buri na in auri marubuci ɗan’uwa na, inji marubuciya Gimbiya Rahama

November 23, 2024
Next Post
Yanzu an wuce matakin gaba da Ninanci, inji Farfesa Abdallah Uba Adamu

Yanzu an wuce matakin gaba da Ninanci, inji Farfesa Abdallah Uba Adamu

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!