• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

by ABBA MUHAMMAD
June 13, 2025
in Labarai
0
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

Alh. Shehu Sani Sado, Yerima Shettima, Fati Ladan da Zaharadden Sani a yayin da za a mika wa Hussaini makullin motar.

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MAWAƘI a Kannywood, Malam Hussaini Danko, wanda a yanzu ake kiran shi da Shatan Jarma, ya bayyana irin farin cikin da ya tsinci kan shi a lokacin da shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa na Matasan Arewa (Arewa Youth Consultative Forum) na ƙasa, Alhaji Yerima Usman Shettima ya gwangwaje shi da dalleliyar mota ƙirar ‘Hyundai’.

A cewar sa, ya yi farin ciki sosai da kyautar da Yerima Shettima ya yi masa, duk wasu na ganin cewa a baya wahalar banza kawai ya ke yi.

A yayin tattauwar sa da mujallar Fim a game da kyautar da aka yi masa, Hussaini ya ce, “Wallahi yau dai Alhamdu lillahi, gaskiya ina cikin farin ciki, sannan ina ƙara godiya ga Allah da wannan kyauta da Jarma ya yi min, kuma Billahillazi na ji daɗin ta sosai.

“Abin da ya sa na ce na ji daɗin ta sosai, saboda akwai waɗanda su ke yi mana kallon mu na wahalar banza ne, babu wani abu da za mu amfana da shi a rayuwa. Don ba zan manta ba, akwai wanda ya ce wahalar banza mu ke yi kaza-kaza-kaza. Sai na ce masa, mu in Allah ya yarda ba za mu yi wahalar banza ba.

Hussaini Danko a jikin motar da aka ba shi riƙe da makullin motar.

“Na ce mu mu na son Jarma ko da mulki ko babu mulki ko ba zai ba mu ba, ni ina ƙaunar sa ne a rai na. Kuma ga shi nan ya zo ya gwangwaje ni da sabuwar mota dalleliya, ka ga babu abin da zan ce wa Allah, wannan shi ma ya na daga cikin nasara.”

Ko me Hussaini zai ce wa masu ce masa wahalar banza ya ke yi? Sai ya ce, “Me zan ce masu? Ai ka san hassada ne. Kawai hassada ne don mutum ba ya tare da shi, ko don babu wata mu’amala da ta taɓa haɗa su, kawai wani sai ya yanke maka hukunci, cai zauna da kai ba, bai san waye kai ba.

“Da yawan mutane akwai masu irin wannan halin. Wannan maganar da na ke faɗa maka, wani mai gida na ne ya faɗa min. Ya ce min wahalar banza kawai na ke yi, ni kuma na ce masa ina Allah ya yarda kai ma sai ka mori abin da Jarman zai yi nan gaba in Allah ya yarda.”

Ya cigaba da cewa, “Ina yi wa Jarma addu’ar fatan nasara, Ubangiji Allah ya ba mu nasara. Kuma da yardar Ubangiji Jarma sai ya hau kujerar nan. Ba na sa wa rai na cewa Jarma ba zai hau kujerar nan ba, ganin sa na ke tamkar ya na kan kujerar.

“Haka kuma, ina mai albishir ga masoyan Jarma cewa, yanzu mu ka fara. Babu inda za ka je ba a san Jarma ba, kuma waƙoƙin da mu ka yi sun ƙara fitar da wanene Jarma, haka kuma kyautar motar nan da ya ba mu.”

Wani hali Hussaini Danko ya ke ciki game da waƙoƙin soyayya da aka san shi a kan su, wanda ake ganin ya yi sanyi ba kamar baya ba? Sai Danko ya amsa da cewa, “Lallai ba na daina waƙoƙin soyayya bane, na ɗan tafi hutu ne mun ba wa yara dama su ma su taɓuka, su yi abin da mu ke yi. To yaran ma mun ba su dama, amma sun kasa, kalaman da wannan ya ɗora a waƙar sa, shi wancan zai kwashe ya sauya kari, ba su ‘creating’, ba su binciken waƙoƙi tun na dauri, ka ga mu mu na binciken waƙoƙi, kamar Nura M. Inuwa, ni, Umar M. Shareef, duk muna binciken irin waɗannan waƙoƙin.

“To, akasari gaskiya yaran yanzu waƙoƙi ne kawai ake yin su, wata ma ba kai ba gindi, a ɗauko sweety, waye-waye da sauran su, duk an riga da an wuce irin wannan, mutane sun saba da irin waɗannan kalaman a kunnuwan su. Shi kuma kullum kunne ya na so ya ji baƙon abu ba abin da ya saba ji ba, ko kuma aka ka daki hankalin ƙwaƙwalwar sa, abin da ya sa na ce za ka daki hankalin ƙwaƙwalwar sa, ka haɗo masa nan, ka haɗo masa can a kalma guda ɗaya ne, amma za ta fassara abubuwa da yawa a cikin ta.

“To, a haka dai mun tafi hutun, amma masoya na cewa sai mun dawo. Don na ma dawo yanzu. Kuma na canza ‘tune’ waƙoƙi na gaba ɗaya. Duk wanda zai saurari waƙoƙi kwanan nan, zai ji daban, wani ma sai ya ce ba ni bane.

Wani kira Danko ya ke da shi ga abokan sana’ar sa mawaƙa? Sai ya ce, “Kiran da zan yi ga mawaƙa ‘yan’uwa na, na farko su sa wa kan su haƙuri, kuma ɗauki abin da ya ke yi a matsayin sana’a, domin ka ga mun ɗauke ta sana’a.

“Saboda haka ka sa wa ran ka sana’a ka ke yi, kuma ka na nishaɗantar da mutane. Sannan nan in ka riƙe ta, babu abin da ba za ka samu ba, yau na mallaki gidaje da waƙa, na sayi motoci duk da waƙa. Babu sana’ar da mutum zai yi a matsayin sa na matashi bai yi nasara ba, amma matakin farko shi ne haƙuri, na biyu juriya, na uku kuma a cire hassada a zuciya. In mutum ya riƙe waɗannan zai samu abin da ya ke so ko da a nan gaba ne.” Inji shi.

A safiyar ranar Talata, 3 ga Yuni ne Alhaji Yerima Shettima ya ba mawaƙin kyautar mota a gidan sa da ke cikin garin Kaduna.

An shirya ƙwarya-ƙwaryan taro, inda Yerima ya gayyaci abokan sa irin su Alhaji Shehu Sani Sado, Honarabul Ɗanjuma anjuma (Don J), Honarabul Aminu Monye, da amarya da Hajiya Fati Ladan ya miƙa makullin motar ga Hussaini a gaban su.

Hussaini Danko ya samu rakiyar, Abdalla DZ, Musty Danko, Fiddata Danko da Nakowa.

Hussaini Danko ya daɗe ya na yi wa Yerima waƙoƙin jinjina, inda dalilin hakan ne shi ya kyautata masa.

Aminin Yerima Shettima, Alhaji Shehu Sani Sado ke gaisawa da Hussaini Danko da Yerima na gefen su.

Loading

Previous Post

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

Next Post

Naɗa ni jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry Powder da aka yi zai amfani Kannywood baki ɗaya, inji furodusa Abubakar Galadima

Related Posts

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa
Labarai

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa

July 28, 2025
Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala
Labarai

Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala

July 28, 2025
KADIFF 2025: Uganda ta fi yawan finafinai a bikin baje-kolin na Kaduna – Israel Kashim Audu
Labarai

KADIFF 2025: Uganda ta fi yawan finafinai a bikin baje-kolin na Kaduna – Israel Kashim Audu

July 25, 2025
Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar
Labarai

Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar

July 24, 2025
‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Next Post
Naɗa ni jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry Powder da aka yi zai amfani Kannywood baki ɗaya, inji furodusa Abubakar Galadima

Naɗa ni jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry Powder da aka yi zai amfani Kannywood baki ɗaya, inji furodusa Abubakar Galadima

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!