• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 4, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda Mutuwa Ta Ratsa Kannywood A Cikin 2023

Mujallar Fim ta lissafa mutane masu alaƙa da industiri waɗanda su ka riga mu gidan gaskiya

by ABBA MUHAMMAD
December 31, 2023
in Nijeriya
0
Jama'a na addu'a a bakin kabarin Alhaji Usman Baba Pategi (Samanja Mazan Fama)

Jama'a na addu'a a bakin kabarin Alhaji Usman Baba Pategi (Samanja Mazan Fama)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Litinin, 16 ga Janairu
Allah ya ɗauki ran jarumin barkwanci a Kannywood, Kamal Aboki, sanadiyyar haɗarin mota da ya ritsa da shi a kan hanyar Maiduguri zuwa Kano.

Litinin, 23 ga Janairu
Allah ya ɗauki ran jarumi kuma furodusa a Kannywood, Abdulwahab Awarwasa. Ya rasu a garin Jos, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Litinin, 23 ga Janairu
Allah ya yi wa Khalid ɗan tsohon shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), rasuwa, a wani asibiti da ke ƙasar Ghana.

Alhamis, 16 ga Maris
Hajiya A’isha Salisu, mahaifiyar darakta a Kannywood, Sadiq Hussaini Jeep, a Kano.

Lahadi, 19 ga Maris
Dakta S.U. Garba, mahaifin jarumar Kannywood, ya rasu a gidan sa da ke Minna, Jihar Neja.

Litinin, 24 ga Afrilu
Allah ya ɗauki ran shahararriyar ‘yar wasan kwaikwayo Hajiya Balaraba Tanko, a gidan ta da ke Tudun Wada, Kaduna.

Talata, 25 ga Afrilu
Malam Muhammad Barde, mahaifin furodusa a Kannywood, Alhaji Habibu Barde ya rasu a asibitin Federal Medical Centre da ke Azare, Jihar Bauchi.

Litinin, 8 ga Mayu
Jarumin Kannywood, Malam Aminu Muhammad (AZ), ya rasu a asibitin Nassarawa da ke birnin Kano.

Lahadi, 25 ga Yuni
Marubuci kuma abokin ‘yan fim, Alhaji Auwal Garba Ɗanbarno, ya rasu sanadiyyar haɗarin mota da ta ritsa da shi a garin Jogana da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa ta Jihar Kano.

Alhamis, 13 ga Yuli
Hajiya Hajara Aliyu, mahaifiyar jarumi a Kannywood Alhassan Kwalle, ta rasu a gidan ta da ke unguwar Bachirawar Madugu, a Ƙaramar Hukumar Ungogo a cikin garin Kano.

Lahadi, 13 ga Agusta
Allah ya ɗauki ran jaruma a Kannywood, Malam Hauwa Magaji Gwarzo, a gidan ta da ke unguwar Kakuri Hausa, Kaduna.

Lahadi, 20 ga Agusta
Allah ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Hannatu Umar Sani, rasuwa, ta rasu a gidan yayar ta da ke unguwar Katampe, Abuja.

Marigayiya Hannatu Umar Sani
Marigayiya Hannatu Umar Sani

Laraba, 23 ga Agusta
Allah ya ɗauki ran furodusa a Kannywood Aminu S. Sufi. Aminu ya rasu a gidan sa da ke Titin Lokoja, unguwar Rigasa, Kaduna.

Alhamis, 31 ga Agusta
Hajiya A’isha, mahaifiyar Abba El-Mustapha ta rasu a Kano.

Laraba, 6 ga Satumba
Allah ya ɗauki ran mahaifiyar jarumi kuma mai bada sutura a Kannywood Umar Big Show. Hajiya Hauwa Hussaini ta rasu a asibitin Nassarawa da ke Kano.

Laraba, 6 ga Satumba
Allah ya yi wa mahaifin darakta a Kannywood Sadiq S. Hussaini Jepp rasuwa. Alhaji Salisu Hussaini Maigwanjo ya rasu a gidan sa da ke unguwar Fagge ‘Yantaya, Kano.

Asabar, 9 ga Satumba
Mawaƙiya Hauwar Aleebaba, ta rasu sanadiyyar banke ta da mota da wani matashi ya yi a Kano.

Hajiya Gwaggo ta na sanya wa El-Mustapha albarka, kwanaki kaɗan kafin rasuwar ta
Hajiya Gwaggo ta na sanya wa El-Mustapha albarka kwanan nan

Talata, 12 ga Satumba
Hajiya Habiba Yusuf, mahaifiyar tsohuwar jaruma Hadiza Maina, ta rasu Asibitin Barau Dikko da ke Kaduna.

Asabar, 30 ga Satumba
Malama Sabira Ishaq Koli, matar furodusa kuma ɗan kasuwa a Kannywood Alhaji Rabi’u Koli, ta rasu a Asibitin Manal da ke Kawo, Kaduna.

Laraba, 4 ga Oktoba
Allah ya ɗauki ran jarumar Kannywood, Hajiya Binta Ola. Hajiya Binta ta rasu a gidan ta da ke Sabuwar Unguwa cikin birnin Katsina.

Asabar, 14 ga Oktoba
Malama Fatima Muhammad, mahaifiyar furodusa a Kannywood Hamisu Bawasa, ta rasu a gidan ta da ke ‘Yantukwane, Tudun Wada, Kaduna.

Marigayiya Hajiya Binta Ola; a dama kuma jama'a ne ke yi mata addu'a a gaban kushewar ta
Marigayiya Hajiya Binta Ola; a dama kuma jama’a ne ke yi mata addu’a a gaban kushewar ta

Alhamis, 19 ga Oktoba & Asabar, 28 ga Oktoba
Allah ya ɗauki ran mahaifiya da yayan jarumin Kannywood, Tanimu Akawu. Hajiya Amina ta rasu a gidan ‘yar ta da ke Layin Zana a cikin garin Jos, Jihar Filato. Shi kuma Alhaji Mustapha ya rasu a hanyar kai shi asibiti kafin rasuwar mahaifiyar su, tsakanin su kwana tara.

Asabar 11 ga Nuwamba
Allah ya ɗauki ran shahararren ɗan wasan kwaikwayo, Alhaji Usman Baba Pategi (Samanja) a Asibitin Garden City da ke Titin Sultan cikin garin Kaduna.

Asabar, 18 ga Nuwamba
Alhaji Ibrahim Sa’idu Gamagira, mijin furodusa kuma tsohuwar shugabar Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, ya rasu Belam Hospital da ke Abuja.

Litinin, 20 ga Nuwamba
Allah ya ɗauki ran darakta a Kannywood Aminu S. Bono. Ya rasu a gidan sa da ke Kano.

Talata, 12 ga Disamba
Allah ya ɗauki ran jarumi Auwal Bauchin-Bauchi. Ya rasu a wani asibitin kuɗi da ke hanyar Jos a garin Bauchi.

Marigayi Alhaji Ibrahim Sa'idu Gamagira (Maje). A dama, matar sa ce, Hajiya Fatima Ibrahim Ahmad (Lamaj)
Marigayi Alhaji Ibrahim Sa’idu Gamagira (Maje). A dama, matar sa ce, Hajiya Fatima Ibrahim Ahmad (Lamaj)

Loading

Tags: Kannywoodmutuwarashe-rasherasuwa
Previous Post

Aure-aure A Kannywood Cikin 2023

Next Post

Darakta a Kannywood, Ibrahim Al-Imash ya zama mai anini biyu

Related Posts

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya

July 1, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina

June 30, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

June 23, 2025
Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya
Nijeriya

Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya

June 21, 2025
Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu
Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu

June 20, 2025
Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Next Post
Darakta a Kannywood, Ibrahim Al-Imash ya zama mai anini biyu

Darakta a Kannywood, Ibrahim Al-Imash ya zama mai anini biyu

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!