• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

‘Yan fim da marubuta sun fidda ni kunya a bikin ‘ya ta, inji jaruma Asma’u Sani

* Na koyi wani babban darasi daga bikin, inji ta

by MUKHTAR YAKUBU
December 14, 2024
in Ranar Murna
0
‘Yan fim da marubuta sun fidda ni kunya a bikin ‘ya ta, inji jaruma Asma’u Sani

Uwar amarya, Hajiya Asma'u Sani

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMAR Kannywood, Hajiya Asma’u Sani, ta bayyana cewa ‘yan’uwan ta ‘yan fim da kuma marubuta littattafai sun fitar da ita kunya da irin karar da suka yi mata a bikin auren ‘yar ta, A’isha Ibrahim Yusuf, wanda aka kammala.

Asma’u ta bayyana hakan ne a hirar da ta yi da mujallar Fim a lokacin da take bayyana ɗimbin farin ciki tare da godiya ga mahalartan bikin.

Ta ce: “To alhamdu lillah, duk da ka same ni a cikin baƙi ana kusa da kammala taron bikin auren ‘ya ta kuma autar mata a cikin ‘ya’ya na, da man matan biyu ne, Sumayya Abubakar, matar Jamilu Ibrahim, sai kuma wannan A’isha, ita ma ga shi Allah ya nuna mana lokacin auren ta. Kuma alhamdu lillah, ina ƙara godiya ga Allah.

Amarya A’isha Ibrahim Yusuf da angon ta

“Ina yin hidimar taruka iri-iri tun daga auren Sumayya da kuma sunan ‘ya’yan da ta haifa duk taron bukukuwa ana yi, amma ban taɓa yin hidima irin wannan ba. Gaskiya ban taɓa tara mutane irin wannan ba.

“Alhamdu lillah, ko a na Sumayya da Jamilu an taru, sai dai a yanzu da yake an ƙara samun arzikin ɗaukaka, jama’a sun ƙaru, don haka mutane daga garuruwa daban-daban, baƙi babu inda ba a zo ba. Legas, Nassarawa, Kaduna Abuja, Gombe duk da sauran garuruwa sun zo wajen wannan taron bikin.

“Kuma alhamdu lillah, gaskiya na ga taro na ga soyayya a wajen mutane. Babu abin da zan ce, sai dai na ce na gode wa Allah.

“Kuma a gaskiya jarumai na masana’antar finafinai ta Kannywood sun yi mini kara sun ba ni mamaki, ‘yan’uwa na jarumai sun fitar da ni kunya.

“Na sani ni ta mutane ce, kuma ina zaune da mutane lafiya, ba na rigima da kowa, kowa ya san ni da haka. Amma yadda jarumai suka yi mini kara wallahi na yi mamaki. Sun yi kara sun zo wajen biki an yi hidima sosai an yi abubuwa. Sun yi alheri a wajen taron bikin, sun fitar da ni kunya.

Asma’u Sani, Ruƙayya Dawayya, tare da sauran jarumai

“Haka nan marubuta su ma sun zo don ina cikin su, dukkan su ƙawaye na ne. Don Bilkisu Yusuf Ali aminiya ta ce sosai, babu inda ba na shiga a cikin gidan su, haka ita ma take a gidan mu. To duk sun zo sun yi mini kara.

“Irin su Fauziyya D. Sulaiman, Hadiza Nuhu Gudaji, Bushira Nakura, Sadiya Garba Yakasai, Lubabatu Ya’u, duk da sauran su, marubuta dai su ma sun yi mini kara.

“Ga kuma oga na, Ado Ahmad Gidan Dabino MON, kuma shugaban mu na MOPPAN kuma sarki na mawallafa.”

Uwar amaryar ta ce akwai darasin da ta koya daga wannan taro.

“Gaskiya alhamdu lillah, wannan taro na samu darasi sosai, domin babban darasin da na samu a tara jama’a shi ne kana so ka sallami waɗancan, kuma ga wasu sun zo, wani ma gani yake yi kamar ka ƙi kulawa da shi. Kuma ba haka ba ne. Kowa so kake ka ba shi haƙƙin sa a matsayin sa na baƙon ka, masoyin ka.

“To alhamdu lillah na sake samun ƙaruwa ta ilimi a kan wannan.”

Ta ƙara da cewa: “Duk abubuwa ga su nan sun gudana, don haka sai an yi haƙuri idan aka tara jama’a.

“Kuma ina godiya ga Allah da kuma ɗimbin jama’ar da suka halarci taron bikin. Wanda aka saɓa wa, ya yi haƙuri, ba da sani ba aka yi hakan ba. Kowa nawa ne saboda yana so na ya zo don haka ba zan yi abin da zai ɓata masa ba ina sani.

“Allah ya kai kowa gidan sa lafiya.”

Asma’u ta ba da shawara ga amarya da kuma surukin ta, ta ce, “Amarya da ango su yi haƙuri, Allah ya ba su haƙuri na zama da juna, domin kuwa shi zaman aure zama ne na zo mu zauna zo mu saɓa, tunda ana zama tare wani zai saɓa wa wani. Shi zai iya yi mata laifi, ita ma za ta iya yi masa. Don haka sai an yi haƙuri da juna a rinƙa yin sulhu a tsakani ba sai an tafi wani waje ba.

“Allah ya kawar da fitina a tsakanin su, ya ba su zaman lafiya. Ina godiya sosai. Allah ya saka wa kowa da alheri.”

Loading

Tags: aureBiki
Previous Post

An ɗaura auren A’isha ‘yar jaruma Asma’u Sani

Next Post

Ministan Yaɗa Labarai ya yi kira ga jihohi da kada su rushe Ma’aikatun Yaɗa Labarai

Related Posts

An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu
Ranar Murna

An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu

May 2, 2025
Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu
Ranar Murna

Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu

April 25, 2025
Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 
Ranar Murna

Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 

April 20, 2025
Ahlan tare da 'yar sa Hassana, amaryar mako mai zuwa
Ranar Murna

Jarumi a Kannywood, Ahlan zai aurar da ‘yar sa Hassana

February 16, 2025
Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir
Ranar Murna

Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir

December 20, 2024
Mawaƙi Abdul Respect ya zama angon Hassana Abubakar
Ranar Murna

Mawaƙi Abdul Respect ya zama angon Hassana Abubakar

December 16, 2024
Next Post
Ministan Yaɗa Labarai ya yi kira ga jihohi da kada su rushe Ma’aikatun Yaɗa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai ya yi kira ga jihohi da kada su rushe Ma’aikatun Yaɗa Labarai

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!