• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, June 4, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen 2023: INEC ta hana ma’aikatan ta shiga cuwa-cuwa wajen raba katin rajistar zaɓe

by DAGA WAKILIN MU
January 24, 2023
in Nijeriya
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi dukkan ma’aikatan ta da ke aikin raba katin shaidar rajistar zaɓe da cewa su guji neman na goro daga hannun masu zuwa karɓar katin shaidar rajistar zaɓe (PVC).

Shugaban Sashen Wayar da Kan Jama’a na INEC a Jihar Abiya, Bamidele Oyetunji, shi ne ya yi wannan gargaɗin a wata tattaunawa da manema labarai a Abiya.

Ya ce babban laifi ne da ka iya kai mutum zaman kurkuku idan aka kama shi ya na neman na goro daga hannun masu zuwa karɓar katin rajistar zaɓe, musamman waɗanda ke da matsalar ganin na su katin a sauƙaƙe.

Wannan gargaɗi ya zo ne bayan wasu mata sun fito sun yi ƙorafin cewa wasu ma’aikata sun nemi su biya su ɗan na goro.

A wani labarin kuma, INEC ta bayyana cewa ta yi haɗin guiwa da hukumomin EFCC da ICPC domin kamawa da gurfanar da duk wanda aka kama ya na saye ko sayar da ƙuri’u.

Ko cikin watan jiya sai da INEC ta ƙara jaddada cewa “yan siyasa ne ke maguɗin zaɓe ba mu ba”.

Yayin da ya rage saura kwanaki 60 a yi zaɓen shugaban ƙasa, a ci gaba da shirye-shirye da ta ke yi, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta haddada cewa ba ta yin katsalandan wajen shiga harƙallar murɗe zaɓe.

Da ta ke jawabi yayin ganawa da manema labarai da ƙungiyoyin kare haƙƙi, Kwamishanar INEC ta Tarayya da ke Jihar Ebonyi, Onyeka Ugochi, ta bayyana cewa ‘yan siyasa ne ke shirya maguɗin zaɓe ba hukumar zaɓe ba.

Ugochi ta ce, “amma da ya ke a wannan zaɓe mai zuwa INEC ta fito da tsauraran matakan hana maguɗin zaɓe kwata-kwata, musamman ta hanyar amfani da na’urar tantance katin ɗan takara, wato BVAS da sauran matakai, babu yadda za a yi ‘yan siyasa su ci kasuwar maguɗin zaɓe.

Daga nan ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin kare haƙƙi su tashi tsaye sosai wajen taya INEC tabbatar da ganin cewa ‘yan siyasa ba su samu wata kafar yin maguɗi ba, komai ƙanƙantar ta.

“Za mu yi dukkan abin da doka ta tanadar da abin da ya wajaba domin mu kauce wa masu so mu haɗa baki da su. Saboda hakan ba zai yiwu mu bada kai borin ‘yan siyasa ya hau ba.

“Kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin kare haƙƙi ku tashi tsaye a matsayin ku na masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe, ku taya INEC tabbatar da ganin an gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar nan. Ku taimaka wajen tabbatar da cewa mun yi abin da doka ta wajibta mana mu yi. Kuma ku taimaka wajen hana masu maguɗi su aikata maguɗi.”

Daga nan ta sake jan kunne da gargaɗin cewa masu ƙoƙarin sayen ƙuri’u su sani duk wanda aka kama, to zai yi zaman gidan kurkuku na shekara ɗaya.

Haka kuma INEC ta ce ta haɗa kai da hukumomin EFCC da ICPC domin yin maganin kangararrun ‘yan siyasar da za su yi ƙoƙarin sayen ƙuri’u a lokutan zaɓe.

Yau dai saura kwanaki 32 a yi zaɓen shugaban ƙasa.

Loading

Tags: 2023 electionsAbiyaBamidele Oyetunjicin hancicuwa-cuwadokaINECkatin rajistar zaɓelaifipvc
Previous Post

Jarumin Kannywood, Abdulwahab Awarwasa, ya rasu bayan doguwar jinya

Next Post

Marigayi Awarwasa mutum ne mai biyayya ga na gaba da shi, inji yayan sa

Related Posts

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Tinubu ya yaba wa Sule Lamiɗo a taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar sa
Nijeriya

Tinubu ya yaba wa Sule Lamiɗo a taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar sa

May 13, 2025
Next Post
Abdulwahab Awarwasa (a hagu). Ana addu'a a gaban kabarin sa

Marigayi Awarwasa mutum ne mai biyayya ga na gaba da shi, inji yayan sa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!