A DAIDAI lokacin da ake musayar ra’ayi kan buga kugen fara yaƙin neman zaɓe na shekarar 2023 wanda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi a jiya, mujallar Fim ta hango cewa akwai ‘yan fim na masana’antar finafinai ta Kannywood waɗanda tuni su ke cikin harkokin zaɓen dumu-dumu. A baya ‘yan Kannywood da ke Kano sun sha shiga siyasa ana damawa da su, amma dai sau da yawa a matsayin masu tallar ɗan takara da kuma jam’iyyar siyasa aka san su, sai ƙalilan da su ka fito takara, wato irin su Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama da ya taɓa yin takarar zama gwamna. A jihar ta Kano, babu wani ɗan fim da ya taɓa tsallake ko da zaɓen fidda gwani a jam’iyyar da ya fito.
To, a wannan karon dai an samu canji, ‘yan fim sun ci gaba a fagen siyasa a Kano. Mujallar Fim ta gano cewa akwai waɗanda su ka fito takara har su ka tsallake siraɗin zaɓen fidda gwani, jam’iyya ta tsai da su a matsayin gwanayen ta a babban zaɓen na 2023.
A Ƙaramar Hukumar Nassarawa, mawaƙi Aminu Ladan Abubakar Ala ya na takarar Majalisar Wakilai a jam’iyyar ADP. A Ƙaramar Hukumar Gwale, tsohon furodusa Abdulhadi Ɗalhatu (Awilo) ya na takarar zuwa Majalisar Dokoki ta Jihar Kano a jam’iyyar PDP. Ali Rabi’u Ali (Daddy) ya na takarar Majalisar Wakilai mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Dala a jam’iyyar PRP.
Shi kuwa jarumi Adamu Abdullahi Adamu (Daddy Hikima), wanda aka fi sani da Abale a cikin shirin ‘A Duniya,’ ya samu tsayawa takarar Majalisar Wakilai mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Kumbotso a jam’iyyar ADP.
Irin wannan fitowa takara ta ba-zata da ‘yan fim su ka yi a Jihar Kano, har su ka yi nasarar lashe zaɓen cikin gida a jam’iyyun su, ya ba su damar mutanen jihar su zaɓe su, musamman ma yanzu da ake faɗin “mutum za a zaɓa, ba jam’iyya ba.”
A yanzu babu wanda zai iya yanke hukuncin cewa ‘yan fim ɗin nan da ke takara za su kai gaci a zaɓen ba baɗi ko a’a; Allah kaɗai ya sani. Lokaci da yanayi ne kaɗai za su bayar da amsa.