MATASHIN mawaƙi a Kannywood, Muhammad Khalid, wanda aka fi sani da Kawu Ɗan Sarki, ya na ɗaya daga cikin mawaƙan wannan zamani da tauraruwar su ke haskawa.
Kawu Ɗan Sarki ya yi fice ne tun da ya saki wata waƙa mai suna ‘Ingallo’, wadda ta yi suna a soshiyal midiya.
Kwanan nan Kawu Ɗan Sarki ya yi hira da mujallar Fim inda ya ba da tarihin sa da dalilin sa na shiga harkar waƙa, da sauran su, kamar haka:
FIM: Ka faɗa mana da tarihin rayuwar ka.
ƊAN SARKI: Suna na Muhammad Khalid, amma an fi sani da Kawu Ɗan Sarki. Ina da kimanin shekara 28 a duniya. Ni haifaffen Jihar Bauchi ne, kuma dukkan karatu na a Jihar Bauchi na yi, amma iyakaci na sakandire.
Ni kafinta ne, sai dai yanayin jiki na bai ba ni damar in iya yin wani aikin ƙarfi ba. Idan na fita sana’ar kafinta a rana, ina samun kuɗin da ba su kai N2,000 ba, kuma kuɗin a wurin magani su ke ƙarewa, wasu lokutan ma har sai an yi ciko a gida.

FIM: Ya aka yi ka fara waƙa?
ƊAN SARKI: Sanadin fara waƙa ta shi ne neman kuɗi. Kamar yadda na faɗi, ba zan iya aikin ƙarfi ba. Abin dai da yawa, amma dai a taƙaice, ni abin da ya kai ni situdiyo ba waƙa ba ce, neman kuɗi na je. Saboda ina aikin ƙarfi, aikin kafinta, in samu dubu ɗaya, amma ta ƙare a magani, har ma a ƙara da ciko a gida. Wannan shi ya sa na koma situdiyo, in samu naira ɗari, ɗari biyu a cikin inuwa!
FIM: Yaushe ka fara waƙa?
ƊAN SARKI: Ban share wasu shekaru masu yawa a harkar waƙa ba.
FIM: Me ya sa ka ke amfani da kalmomin batsa a waƙoƙin ka?
ƊAN SARKI: Masu zargin ina saka kalmomin batsa a cikin waƙoƙi na su daina; kawai dai ina zurfafa kalamai ne saboda su yi ƙwari a cikin waƙoƙi na.
FIM: Waɗanne irin waƙoƙi ka fi yi?
ƊAN SARKI: Yanayin waƙoƙi na kala daban-daban ne. Ina na soyayya, suna, biki, siyasa da sauran su, amma dai na fi karkata ga waƙoƙin soyayya.
FIM: Wace waƙar ka ce fitacciya, wadda kowa ya san ta?
ƊAN SARKI: Waƙar ‘Ingallo Na Ciwo’.
FIM: Wanene ubangidan ka a harkar waƙa?
ƊAN SARKI: Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ne ubangida na a Kannywood, saboda shi ya ɗauki nauyin bidiyon mafi yawan waƙoƙi na har duniya ta san ni.
FIM: Menene burin ka a kan wannan sana’a?
ƊAN SARKI: Ina da burin in bar baya mai kyau. Sannan ina fatan na ci lokaci na tare da fatan kafa mutane da yawa.
FIM: Waƙoƙin ka za su kai nawa zuwa yanzu?
ƊAN SARKI: A ƙiyasi waƙoƙi na za su kai talatin da biyu a halin da ake ciki. Sannan ni ba na rubuta waƙa, kawai idan na buɗe kiɗa na ba na tashi sai na kammala waƙa ta, sai dai in yi ‘yan gyare-gyare idan na kammala.
FIM: Ko akwai ƙalubale da ka ke fuskanta?
ƊAN SARKI: Babban ƙalubalen da ke damu na shi ne wasu na tunanin na yi girma ne da na kawo haka, ko na tara manyan kuɗaɗe, ta yadda za ka ga wani ya kawo maka matsalar sa da ta kai N500,000, amma kai ba ka da hali.

FIM: Ya mu’amalar ka ta ke da masoyan ka?
ƊAN SARKI: Ina da kyakkyawar mu’amala da su, domin a rana ina amsa kiran waya sama da dubu biyu daga masoya na na sassan duniya daban-daban. Haka kuma ina amsar saƙonni ta ‘WhatsApp’ shi ma babu iyaka, da sauran shafuka na na sada zumunta.
FIM: Mun gode, Kawu.
![]()







