• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Za mu ƙara yawan yara miliyan 5 a shirin ciyar da ‘yan makaranta kafin 2023 – Minista Sadiya

by DAGA WAKILIN MU
July 3, 2021
in Nijeriya
0
Za mu ƙara yawan yara miliyan 5 a shirin ciyar da ‘yan makaranta kafin 2023 – Minista Sadiya
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAR Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar-Farouq, ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar ƙara yawan ɗalibai guda miliyan biyar cikin shirin ciyar da yara ‘yan makaranta, wato ‘National Home Grown School Feeding Programme’ (NHGSFP) daga yanzu zuwa shekarar 2023. 

Hajiya Sadiya ta faɗi haka ne a lokacin taron da masu ruwa da tsaki su ka yi kan tantance masu amfana da shirin don haɓaka shi wanda aka yi a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara. 

A sanarwar da mai taimaka mata ta musamman kan harkar yaɗa labarai,  Halima Oyelade, ta fitar a Abuja, an ruwaito ministar ta na faɗin, “Sama da yara ‘yan makaranta tara ne su ke amfana da kyautar abinci sau ɗaya a kowace rana a lokacin zuwa makaranta a kowane zangon karatu a duk faɗin ƙasar nan. 

“Yanzu, mun samu izinin mu ƙara yawan ‘yan makaranta miliyan biyar kafin shekarar 2023. 

“Akwai masu dafa abinci sama da 100,000 da aka ɗauka aiki da kuma ƙananan manoma sama da 100,000 a cikin wannan shiri, da masu amfana ta hanyar su, wanda ya sanya shirin na NHGSFP ya kasance muhimmi wajen kyautata cigaban zamantakewa da tattalin arziki kuma ya kamata a ƙarfafa shi, a inganta shi a ko’ina a ƙasar nan.

Mai girma Minista, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta na gabatar da jawabin a taron da aka yi jiya a Gusau

“Ina murnar ganin yadda ma’aikatan gwamnatocin Zamfara da Tarayya da ke gudanar da shirin na NHGSFP da kuma sauran masu ruwa da tsaki su ke aiki tare da juna kuma cikin kusanci don tantance yawan masu amfana da shirin kuma su ke gyara bayanan su don samun tasiri da tsare gaskiya.

“Saboda haka, a yayin da mu ke gode wa gwamnatin Zamfara saboda sadaukarwar ta ga aiwatar da NHGSFP, ina kuma ba kan mu ƙwarin gwiwa kuma mu tabbatar da mun ƙara azama domin ganin an samu ƙarin yara masu amfana da wannan shiri.” 

Sadiya ta ƙara da bayyana cewa an fito da shirin NHGSFP ne da tunanin zai kasance mai fuskoki daban-daban don ƙara yawan ɗalibai, inganta abincin ɗalibai, mara wa  masu noma abinci ƙwarin gwiwa tare da ƙara yawan ɗalibai da samar da aikin yi da kuɗaɗen shiga.

 “Hasali ma dai, manufar sa ita ce a samar da abinci mai gina jiki ga dukkan ‘yan makaranta da ke makarantun firamare na gwamnati sau ɗaya zuwa sau uku a rana.”

Ta ce manufar Shugaba Muhammadu Buhari ita ce a yaƙi fatara da yunwa, don haka aka ƙirƙiri ‘National Social Investment Programme’ wanda ya ƙunshi shirye-shirye da su ka haɗa da NHGSFP, N-Power, ‘Conditional Cash Transfer’ da ‘Government Enterprise and Empowerment Programme’.

Dandazon jama’a su na sauraren jawabin ministar
Minista tare da ɗaya daga cikin waɗanda su ka amfana daga shirin

Loading

Tags: Halima OyeladeMinistry of Humanitarian AffairsNational Home Grown School Feeding ProgrammeSadiya Umar Farouq
Previous Post

Zai yi wahala a maye gurbin Zainab Booth – Jaruman Kannywood

Next Post

Hotuna: Minista Sadiya a taron shirin ciyar da ‘yan makaranta a Gusau

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Za mu ƙara yawan yara miliyan 5 a shirin ciyar da ‘yan makaranta kafin 2023 – Minista Sadiya

Hotuna: Minista Sadiya a taron shirin ciyar da 'yan makaranta a Gusau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!