GWAMNAN Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana ƙudirin gwamnatin sa na ci gaba da taimaka wa masana’antar shirya finafinai ta Kannywood a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.
Haka kuma ya jinjina wa shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), saboda sadaukarwar sa ga ciyar da gwamnatin sa gaba.
Gwamnan ya bayyana haka ne a daren ranar Juma’a, 3 ga Satumba, 2021 a lokacin wani zama na musamman da ya yi tare da masu ba shi shawara na musamman kan harkokin nishaɗantarwa da kuma wasu manyan ‘yan fim.
Da ya ke bayyana wa mujallar Fim yadda zaman ya gudana, shahararren mawaƙin nan kuma mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin nishaɗi, Ibrahim Ibrahim, ya ce sun je ofishin gwamnan ne domin su gabatar da bayanai kan wasu ayyuka da gwamnan ya ba su.
Zuwan nasu ya faru ne jim kaɗan bayan da wasu daga cikin shugabannin ƙungiyoyin Kannywood su ka kai wa gwamnan ziyara.
Ibrahim ya ce, “A matsayin su na ‘yan cikin gwamnati a duk lokacin da gwamna ya ga dama zai iya neman su domin su tattauna kan wasu muhimman abubuwa. Don haka ko da wannan zuwan da mu ka yi mun je ne domin gwamna ya ba mu wani aiki da za mu yi kuma ya nemi ganin mu kan wata harka ta cigaba don ganin yadda za a bunƙasa abubuwa tare da yi mana godiya kan irin gudunmawar da mu ke bayarwa.
“Sannan gwamna ya jaddada goyon bayan sa ga shi shugaban Hukumar Tace Finafinai, Isma’il Na’abba Afakallah.”
Ya ce, “Don ba na mantawa, sai da gwamnan Jihar Kano ya buɗe baki ya ce ‘shugaban Hukumar Tace Finafinai Afakallahu, abin alfaharin mu’.
“Daga nan kuma mai girma gwamna ya yi tsokaci kan ziyarar da ‘yan’uwan mu su ka kai masa, wanda kuma cikin mu kowa ya tashi ya gabatar da bayanai daidai yadda ya kamata. Kuma ni daga cikin bayanan su, wallahi ban ji inda wani ya ci mutuncin wani ba, ban ji inda wani ya kama sunan mutum ba, ban ji inda wani ya ce ya na faɗa da wani ba, tsakani na da Allah.”
Mawaƙin ya ci gaba da cewa Ganduje ya yi tsokaci kan yadda wasu daga cikin ‘yan masana’antar ta Kannywood su ka kai masa ziyara, inda ya ce, “Mai girma gwamna ya jaddada cewa akwai wasu sun zo wajen sa su ma ‘yan’uwa ne; sun zo da buƙatar cewa su ma za su bada gudunmawa, za su yi tallace-tallace da sauran su. To dai mai girma gwamna ya jaddada mana cewa duk wanda ya zo mu karɓe shi hannu biyu-biyu, amma abin da gwamna ya ce, ‘Duk wanda ya zo ya bi tsari ya yi rajista, to a ba shi dama ya gudanar da ayyukan sa ko ɗan Kano ne ko da ba ɗan Kano ba ne’.
“Manufar rajista shi ne in dai zai bi ƙa’idoji ya kuma bi doka, wanda ina ganin wannan dokar ba ta mutum ɗaya ba ce, shi ma gwamna gadar ta ya yi. Shekarau ya yi, an bi shi an bi dokokin, Kwankwaso ma ya yi kuma mun je mun yi, sannan Ganduje ya zo mun je mun yi.
“To idan wani bai yi ba, ni ban san dalilin wani ba kuma ban taɓa yin tsokaci ko na soki wani da cewa me ya sa bai yi ba? Domin wannan ra’ayin kan sa ne.”
Ibrahim ya kuma ce gwamna ya nanata cewa duk mutumin da ya bi doka, to fa la shakka kowa ɗan sa ne.
Bugu da ƙari, Ibrahim ya ce gwamna ya hore su da su kiyaye harshen su, musamman ma su mawaƙa da su ke yi masa waƙa da kada su ci mutuncin wani ko zagin wani ko faɗar baƙar magana ko kuma tozarta mutum da iyalin sa.
Haka kuma gwamnan ya bayyana cewa duk wanda ya yi amfani da damar sa ya ci mutuncin wani, to fa kada su manta shi shugaba ne, ya na da ‘ya’ya, ya na da iyali, bai ga dalilin da don ba ka ra’ayin mutum ko ba ka tafiyar sa sai ka zage shi, sai ka tozarta shi, sai ka haɗa sunan sa da dabba ko ka faɗi wasu munanan kalamai.
Duk da cewa ya ce gwamna bai hana su su yi waƙoƙin adawa ba, amma ya ce kada a dira kan matar mutum ko iyalin sa kan wani abu da sauran su, kuma sannan daga baya mutum ya ce zai je ya yi tallar sa.
Ya ce, “Duk da cewa ba wani abu ba ne gwamnoni ma ana yi wata ran kuma sai ka ga an zauna a inuwa ɗaya. Sannan duk wanda ya ke so ya shigo Gandujiyya ƙofar sa a buɗe ta ke. Kuma kowa ya je ya yi rajista.”
A ƙarshe, Ibrahim Ibrahim ya bayyana ra’ayin sa da cewa shi idan a kan kan sa ne duk wani ɗan Kannywood so ya ke ya ga ya koma Gandujiyya, kuma ya bi doka, don ko su ma ya ce ko su da su ke cikin gwamnati ba sa zuwa su yi abu kai-tsaye na harkokin fim har sai da su ka yi rajista.
Ya ce duk waɗanda aka ce sun je gun gwamna shi ba wanda ba ya ma’amala da shi, hasali ma daga cikin su akwai wanda su ke samo aiki su kirawo shi ya je ya yi ya ƙaru da shi, shi ma kuma in ya samu zai kirawo su su yi su ƙaru da juna.
Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci taron sun haɗa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Malam Muhammad Garba, Jamilu Jadda Garko, shugaban ƙungiyar jarumai Alhassan Kwalle, Sani Sule Katsina, Ali Nuhu, Adam A. Zango, Dauda Kahutu (Rarara), da sauran su.
Copyright © Fim Magazine. All rights reserved
www.fimmagazine.com