• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, July 26, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zargin yaɗa baɗala: Kotu ta yanke wa Sayyada Sadiya Haruna hukunci

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
August 23, 2021
in Labarai
0
Zargin yaɗa baɗala: Kotu ta yanke wa Sayyada Sadiya Haruna hukunci
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WATA kotu a birnin Kano a yau ta yanke wa jaruma kuma furodusar finafinan Hausa, Sayyada Sadiya Haruna, hukuncin komawa Islamiyya.

Sadiya dai ta shahara wajen sayar da kayan ƙarin ni’ima da na ƙarfin maza ta hanyar soshiyal midiya, kuma tsarin yin tallar ta ya na ba wasu mutanen mamaki ko haushi, wanda hakan ne ya sa jami’an Hukumar Hisba su ka kama ta a ranar Juma’a da ta gabata, 20 ga Agusta, 2021.

Hukumar ta damƙa ta ga hannun rundunar ‘yan sanda ta Jihar ta Kano, su kuma ‘yan sandan su ka maka ta a kotun shari’ar Musulunci da ke Hukumar Hisbah ta Jihar Kano bisa zargin yaɗa hotunan batsa a kafafen sada zumunta da sunan sana’a.

‘Yan sandan sun gurfanar da kyakkyawar jarumar ne a gaban Mai Shari’a Ali Jibril Ɗanzaki, wanda shi kuma bayan an gabatar masa da bayanai sai ya yanke mata hukuncin sanya ta a makarantar Islamiyya mai suna Darul Hadith har na tsawon wata bakwai.

Ɗaya daga sharuɗɗan da alƙalin ya gindaya mata shi ne za ta riƙa zuwa makarantar tare da rakiyar jami’an Hukumar Hisba.

Haka kuma ya bayyana cewa a duk sa’ilin da ta je makarantar, za ta riƙa sa hannu a wata takarda, shaidar ta je ɗin.

Daga nan aka sake ta, ta tafi gida.

Wakilin mujallar Fim ya so jin ta bakin jarumar kan wannan hukunci da aka yanke mata, amma abin ya faskara.

Kotu ta umarci Sayyada Sadiya Haruna ta koma Islamiyya

Ita dai Sayyada Sadiya Haruna, da yawa su na mata kallon ‘yar taratsi, wadda ke amfani da kalaman batsa da rawar kai a bidiyoyin tallar kayan gyaran jiki da na ƙarin ni’ima da ƙarfin maza. Haka kuma ta kan yawan ambaton ƙirar jikin ta da kyan fuskar ta.

To amma kuma ta kan shirya bidiyoyin waƙoƙin yabon Manzo Allah (s.a.w.), inda ake nuno ta ta na bin waƙoƙin bege da wasu su ka rera.

Ta raɗa wa kan ta laƙabin Sayyada domin nuna shauƙin ta game da son Manzon Allah (s.a.w.).

Kama ta da ‘yan Hisba su ka yi ya jawo ka-ce-na ce a soshiyal midiya, inda wasu ke cewa an kyauta, ya kamata a ɗaure ta, to amma wasu kuma na cewa sam ba daidai ba ne.

Jaruma Ummah Shehu na daga cikin masu kare Sadiya, ta na faɗin cewa kama ta da aka yi an keta mata mutunci kuma Allah ya ce ba a shiga tsakanin sa da bawan sa. 

Wasu masu maganar sun yi wa Umma Shehu caa, su na cewa sam ba ta nuna kishin Musulunci ba kuma kama Sadiya abu ne da ya dace.

Loading

Tags: hausa filmsHukimar HisbahKannywoodMai Shari'a Ali Jibril JanzakiSayyada Sadiya HarunaUmmah Shehu
Previous Post

Ban yi soyayya da Ummi Rahab ba – Adam A. Zango

Next Post

Hisbah ta Kano ta shiga farautar Ummah Shehu

Related Posts

Labarai

Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar

July 24, 2025
‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Next Post
Hisbah ta Kano ta shiga farautar Ummah Shehu

Hisbah ta Kano ta shiga farautar Ummah Shehu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!