• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ban yi soyayya da Ummi Rahab ba – Adam A. Zango

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
August 23, 2021
in Labarai
0
Ban yi soyayya da Ummi Rahab ba – Adam A. Zango
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ADAM A. Zango ya bayyana cewa ko kaɗan bai yi soyayya da jaruma Ummi Rahab ba kamar yadda wasu ke tunani. A madadin haka, rashin biyayyar ta a gare shi ne babban abin da ya raba shi da ita.

Fitaccen jarumin kuma mawaƙi a masana’antar Kannywood ya faɗi haka ne a wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, wadda aka wallafa bidiyon ta a yau. 

A cewar Zango, tun kafin Rahab ta zo kamfanin sa akwai mutane da dama waɗanda ya raine su amma daga ƙarshe su ka bijire masa.

Ya ce a baya an datse mata harkar fim amma ya dawo da ita, kuma ya ci gaba da kula da ita a cikin masana’antar.

Ya ce, “Soyayyar da ta ke tsakani na da Ummi ta uba da ‘ya ce, domin na riƙe ta tun ta na shekara goma sha ɗaya. Kuma yanda mu ke da ita zan ma iya bayar da auren ta.

“Sannan kuma duniya ta san ni da ita. Kuma ni ina karɓar jarabta kowace iri ce ta zo gare ni.

“Sannan kuma duk mutumin da aka ce ka ɗauke shi kamar ɗa ko ‘ya, to babu ranar da mahaifin ka zai ce Allah ya tsine maka, sai dai yai ta maka addu’a a kan hanyar da ka canza ko kuma ka bi idan mara kyau ce.” 

Adam A. Zango cikin bidiyon hirar sa da BBC Hausa

Jarumin ya jaddada cewa, ”Soyayyar da ke tsakani na da Ummi Rahab ta uba da ‘ya ce, wanda waɗanda su ke kusa sun sani; waɗanda su ke nesa ne su ke yi wa abin kallon wani abu daban. 

“Kowa ya sani, ko in ce waɗanda su ka sani sun sani, tun ta na shekara goma sha ɗaya na ke kula da ita. 

“Amma ina so mutane su sani ba a hannu na ta ke ba, ina kula da ita ne a cikin masana’anatar Kannywood ne; ta na da iyayen ta waɗanda su ke kula da ita, su ne masu ba ta tarbiyya. Ni nawa kare ta da kuma kare mata mutuncin ta da kuma ɗora ta a kan hanyar da ta dace a cikin masana’anatar, shi ne aiki na tun ta na yarinya har zuwa lokacin da ta girma.

“An datse mata harkar fim ɗin kafin ta girma; da ta girma kuma ni dai na sake dawo da ita.”

Cikin wata siga mai cike da tausayi, Zango ya ce, “Ka haifi yaro ne, ba ka haifi halin sa ba; ɗan da ka haife shi ma ya na iya fin ƙarfin ka ballantana kuma wanda ka ɗauke shi a matsayin ɗa. Don haka ba wani abu ba ne, wani kes, wanda ya faru tsakani na da ita wanda mutane su ka dinga juyawa, su ka maida shi kamar wani abu. 

“Kuma ‘yi abin da ya kamata’ ko ‘bar abin da bai dace ba’ shi ne ya haɗa ni da ita. Daga ƙarshe na ce Allah ya ba mu sa’a, lokaci zai nuna mai gaskiya!”

Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Ummi Rahab kan wannan taƙaddama amma abin ya faskara.

Loading

Tags: Adam ZangoBBC Hausahausa filmsKannywoodUmmi Rahab
Previous Post

Hotuna: Dinar auren Garzali Miko

Next Post

Zargin yaɗa baɗala: Kotu ta yanke wa Sayyada Sadiya Haruna hukunci

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Zargin yaɗa baɗala: Kotu ta yanke wa Sayyada Sadiya Haruna hukunci

Zargin yaɗa baɗala: Kotu ta yanke wa Sayyada Sadiya Haruna hukunci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!