A wani ci gaba na bunƙasar adabi da yaɗuwar harshen Hausa, Zauren Manazartan Makaɗa da Mawaƙan Hausa ya shirya babban taro na cikar sa shekara 10 da kafuwa.
Taron wanda aka gudanar da shi a ranar Asabar 20 ga Disamba a babban ɗakin taro na Sa’adu Zungur da ke Gidan Mambayya a Unguwar Gwammaja dake cikin garin Kano ya samu halartar mambobin zauren da kuma sauran manyan baƙi daga garuruwa da dama a cikin ƙasar nan.
Tun da farko da yake jawabin buɗe taron, Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya kawo asalin zuwan Hausawa wannan yankin da a yanzu ake kiran sa da ƙasar Hausa, inda ya ce “Hausawa sun zo wannan yankin ne a lokacin wajen dazuzzuka ne babu kowa a wajen, kuma ya samo asali ne daga ƙaura daga wani waje zuwa wani waje, har ta kai ga sun samu gindin zama a wannan yankin da ake cewa Ƙasar Hausa.
“Haka nan Hausawa sun ci gaba da suna rayuwar su da al’adun su har suka samar da kiɗan su daga busa ƙaho, da sauran kayan kaɗe-kaɗe. Don haka Hausawa wasu al’umma ne da suke da al’adu masu inganci da tsari tun tsawon shekaru masu yawan gaske, wanda da wannan ne ma nake kira ga wannan Zauren na Manazartan Makaɗa da Mawaƙan Hausa da su yi ƙoƙarin samar da wata mujalla da za ta rinƙa adana abubuwan al’adu da kuma harshen Hausa.”

Shi ma a nasa jawabin, Alhaji Ibrahim Muhammad Danmadamin Birnin Magaji, a wata muƙala da ya gabatar mai taken ‘Amfani da Kaɗe-kaɗen Gargajiya ga Al’ummar Hausawa,’ ya bayyana yadda Hausawa suka yi amfani da kiɗa wajen isar da saƙo na farin ciki da baƙin ciki a lokacin baya.
Ya kawo misali da yadda mata a cikin gida suke yin amfani da wani salo na kiɗan ƙwarya ko kiɗan turmi domin isar da wani saƙo. Idan haihuwa aka yi akwai kiɗan da suke yi don a sanar da jama’a, haka idan bikin aure ne akwai kiɗan da za a yi haka sauran bukukuwa na al’ada.
Haka nan a fadar sarakuna akwai yanayin kiɗan da ake yi wajen isar da saƙo, haka manoma, mahauta, wanzamai da masu farauta kowa da salon kiɗan da yake yi domin isar da saƙo.
Wannan ta sa a fada basarake ba ya zama babu makaɗa da mawaƙa. Don haka kiɗa da waƙa yana da muhimmanci wajen isar da saƙo a cikin al’ummar Hausawa.
Shi ma a nasa jawabin, Malam Fatihu Mustapha ya kawo asali da kuma yadda aka samar da dandalin Zauren Manazartan Makaɗa da Mawaƙan Hausa shekara 10 da suka wuce inda ya ce “Asali wannan zauren ya samu ne daga tunanin Malam Ibrahim Sheme na yadda za a samar da wani zaure da za a rinƙa tattaunawa a game da Makaɗa da Mawaƙan Hausa domin inganta tarihi da adana shi. Don haka a farko mun fara ne daga Facebook, kuma daga baya sai muka ga ta hanyar manhajar WhastApp zai fi samun jama’a da kuma karɓuwa.
“Kuma alhamdulillah a komawar da muka yi da shi WhastApp muka samu Jama’a da dama a cikin zauren, har da zauren ya kasu gida uku, akwai ‘yan tsohon alƙawari da kuma ‘yan sabon alƙawari, da ‘yan bakin Ganga. Don haka zai ya zama ana tattaunawa a kan waƙoƙi da rayuwa. Kuma waƙoƙin da ake tattaunawa a kan su ba ma na Hausawa ba kaɗai har ma da na kudu da ma na ƙasashen Afirika da Turai. Amma dai an fi yin magana a kan waƙoƙin Hausawa. Don haka a wannan shekara 10 da kafuwa wannan zauren an samar da ci gaba na yaɗuwar ilimi da fahimtar juna da kuma ƙulla zumunta. Don haka a yanzu wannan zauren ya zama wata cibiyar horaswa da ilimintarwa ga jama’a kan al’adun Hausa da tarihin su.”
Shi kuma Uban taro, Sarkin Jama’are, Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, ya nuna farin cikin sa a bisa karrama shi da aka yi na ya zama uban taron wanda duk nauyi ne aka ɗora masa, amma dai shi abin alfahari ne a gare shi, don haka ya yi godiya ga dukkan mahalarta taron da waɗanda suka shirya shi, da kuma dukkan jama’ar da suke cikin guruf ɗin Zauren Manazartan Makaɗa da Mawaƙan Hausa.
Da take jawabin rufewa, Dakta Bilkisu Yusuf Ali, ta nuna alfaharin ta ga zauren saboda hatta karatun ta na digiri na uku da ta yi, ta samu abubuwan ilimi ne a zauren ta sanadiyyar muƙalun da Alhaji Ibrahim Muhammad Danmadamin Birnin Magaji yake kawowa a cikin zauren. Ta kuma yi godiya ga dukkan jama’ar da suka halarci taron da fatan Allah ya kai kowa gidan sa lafiya.

An dai kammala taron ne da misalin ƙarfe uku na rana kuma an tashi daga taron lafiya.