• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zurfafa hulɗa da BBC zai taimaka wajen samun ƙara wayewar al’ummar mu, inji Minista

by WAKILIN MU
August 28, 2024
in Nijeriya
0
Zurfafa hulɗa da BBC zai taimaka wajen samun ƙara wayewar al’ummar mu, inji Minista

Daga hagu: Mai Gudanarwa, Harsunan BBC, Fiona Crack; Minista Mohammed Idris, da Mataimakin Shugaban Sashen Labarai na BBC kuma Daraktan BBC, Jonathan Munro

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira da a zurfafa alaƙa tsakanin Nijeriya da BBC domin samar da al’umma mai masaniya a kan lamurra.

Idris ya bayyana haka ne a wata ziyara da ya kai hedikwatar BBC da ke Landan.

Ziyarar dai wani ɓangare ne na ƙoƙarin samar da kyakkyawar alaƙa tsakanin Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Nijeriya da kafafen yaɗa labarai daban-daban, na gida da waje.

Ta haɗa da ganawa da manyan shugabannin BBC, ciki har da Mataimakin Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na BBC kuma Daraktan BBC, Jonathan Munro.

Idris ya jaddada muhimmancin kafafen yaɗa labarai wajen tsara fahimtar jama’a da haɓaka cigaba.

Ya ce: “Kafofin watsa labarai suna taka rawa mai muhimmanci wajen tsara labaran da suka dace, da samar da fahimtar juna, da samar da cigaba, don haka ya zama wajibi ga kafafen yaɗa labarai da ke isar da saƙo ga duniya su zurfafa fahimtar yanayin zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da al’adun al’ummomin da suke ba da rahoto akai.”

Idris ya kuma bayyana muhimmancin rawar da BBC ke takawa wajen bayar da rahotanni kan tafiyar siyasar Nijeriya, yana mai cewa yana da muhimmanci BBC ta daidaita rahotannin da take yi kan Nijeriya ta hanyar mai da hankali kan cigaban da ƙasar ke samu.

Ya ƙara da cewa, “Nijeriya tana da ɗimbin matasa masu tasowa da ƙaunar da ba a saba gani ba na cin gajiyar damarmaki ko da kuwa ana fuskantar ƙalubale masu tarin yawa, lamarin da ke buƙatar a ba da muhimmanci ga sakamako mai kyau a Nijeriya.”

Ya kuma yi nuni da cewa yaɗa labaran ƙarya babbar matsala ce da ke kawo cikas ga cigaba da kuma lalata amanar da ke tsakanin gwamnati da jama’a.

Idris ya yi kira ga BBC da ta yi aiki tare da abokan hulɗar ta na ƙasa da ƙasa don magance waɗannan matsalolin.

Ministan ya yaba da yadda BBC suke faɗaɗa ayyukan su a Nijeriya ta hanyar samar da ƙarin yarurrukan da suke gabatar da shirye-shirye da su, wato Hausa, Ibo, Yarbanci, da Pijin.

Ya ce hakan ya taimaka wajen yaɗa bayanai da yawa tare da samar da ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya da dama.

Loading

Tags: BBCFiona CrackJonathan MurnoMohammed Idris
Previous Post

Jarumin Kannywood Yakubu Mohammed ya ɗauki nauyin karatun wasu yara

Next Post

Minista ya jaddada muhimmiyar rawar kafafen yaɗa labarai a cikin al’umma

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Minista ya jaddada muhimmiyar rawar kafafen yaɗa labarai a cikin al’umma

Minista ya jaddada muhimmiyar rawar kafafen yaɗa labarai a cikin al'umma

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!