• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jarumin Kannywood Yakubu Mohammed ya ɗauki nauyin karatun wasu yara

by ABBA MUHAMMAD
August 22, 2024
in Labarai
0
Jarumin Kannywood Yakubu Mohammed ya ɗauki nauyin karatun wasu yara

Hagu zuwa dama: Yakubu Mohammed, Bashir, Victor (Shugaban makarantar) sai Muhammad Sudais da abokin a harabar makarantar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHAHARARREN jarumi kuma mawaƙi a Kannywood, Yakubu Mohammed, ya ɗauki nauyin karatun wasu yara biyu daga Ƙaramar Hukumar Wudil da ke Jihar Kano waɗanda aka nuno suna rera yaren Aluta.

Yakubu ya ɗauki nauyin karatun Bashir Yahaya Ubale da Muhammad Inuwa tun daga firamare har zuwa jami’a.

Maƙasudin ɗaukar nauyin karatun yaran, shi ne sakamakon wani bidiyo da wani ɗalibin Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano (KUST) da ke Wudil, mai suna Muhammad Sudais, ya wallafa a Facebook yaran su na Aluta irin wanda ɗaliban jami’a ‘yan gwagwarmaya su ke yi a harabar jami’ar.

Wannan ya ba Yakubu sha’awa, shi ma sai ya ɗauka ya ɗora a Facebook da Instagram.

Daga baya, sai ya nemi a nemo masa inda yaran suke, sai shi Muhammad Sudais da wata Ummukhursum su ka nemo masa bayanan inda yaran su ke.

Yakubu ya ziyarci yaran da iyayen su, inda ya gana da su.

Sannan ya sa Ummukhursum ta nemo masa makarantar kuɗi da ya kamata a saka su.

Ummukhursum ta nemo wata makaranta mai suna De Fountain Knowledge Academy, a Wudil, aka yi wa Bashir da Muhammad rajista, ta yadda da zarar an koma makaranta a Satumba za su fara zuwa makaranta.

A yayin ziyarar, Yakubu ya saya wa yaran kayan sawa, kuma a lokacin su ka canza kaya, sannan ya ɗebe su zuwa makarantar da aka yi masu rajista.

Bashir da Muhammad tare da iyayen su sun yi matuƙar farin ciki da wannan cigaba da su ka samu.

Haka kuma sun yi wa Yakubu addu’o’i da godiya.

Bashir da Muhammad, kowane da rasiɗin kuɗin rajistar da aka yi masa a hannun sa

Aluta dai kalma ce da aka fi amfani da ita a cikin ƙasashen Afrika don yin nuni ga gwagwarmaya ko yaƙi da zalunci, rashin adalci na zamantakewa, ko ko wani nau’i na zalunci ko cin hanci da rashawa. Ya ƙunshi ra’ayin haɗin kai da tsayin daka don samun ‘yanci da daidaito.

Ana danganta kalmar sau da yawa tare da ƙungiyoyin ɗalibai, ƙungiyoyin ƙwadago, da gwagwarmayar siyasa.

Aluta ta ƙunshi ƙudirin ƙalubalantar tsarin mulki da bayar da shawarar kawo sauyi ta hanyar zanga-zangar da aka shirya da sauran nau’o’in tsayin daka.

Loading

Tags: agajimakarantaYakubu Mohammed
Previous Post

Ali Nuhu ya buɗe shagon Rufaida haɗe da sunan kamfanin sa na FKD

Next Post

Zurfafa hulɗa da BBC zai taimaka wajen samun ƙara wayewar al’ummar mu, inji Minista

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Zurfafa hulɗa da BBC zai taimaka wajen samun ƙara wayewar al’ummar mu, inji Minista

Zurfafa hulɗa da BBC zai taimaka wajen samun ƙara wayewar al'ummar mu, inji Minista

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!