• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zuwa ga Adam A. Zango: Ina aka kwana da marayun ka na Zariya?

by DAGA BASHIR YAHUZA MALUMFASHI
October 24, 2021
in Tsokaci
0
Adam A. Zango

Adam A. Zango

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BAYAN gaisuwa mai yawa tare da fatan ka na lafiya. Allah sanya haka, amin.

Bayan haka, ba tare da ɓata lokaci ba, na rubuto maka wannan saƙo ne da nufin jin inda aka kwana dangane da babban abin alherin da ka yi iƙirarin ka aikata a bara (Oktoba 2020), inda ka sanar da al’umma cewa ka fidda zunzurutun kuɗi, kimanin naira miliyan 47, domin ɗaukar nauyin karatun wasu yara marayu sama da 100, a wata makaranta mai zaman kan ta, mai suna ‘Professor Ango Abdullahi College’.

Babban dalilin da ya sanya na tado maka da wannan batu shi ne, saboda a bara, daidai lokacin nan, al’amarin naka ya tada ƙura a nan kafafen sada zumunta na soshiyal midiya da kuma jaridu, mujallu, rediyo da talabijin.

A wancan lokacin, mutane da yawa sun riƙa tababa da kokwanto kan al’amarin, har ma wasu kai-tsaye su ka ƙaryata ka, wasu ma har su ka nemi taɓa mutuncin ka.

Idan ba ka mance ba, ni kai na daga jaridar Aminiya na kira ka a waya sau uku, ba ka ɗaga ba, kuma na turo maka tes amma ka ƙi amsa tambayar mu. Haka mu ka gaji mu ka buga labarin ta hanyar abin da mu ka samu daga hukumar makarantar da kuma wani ɓangare na fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau.

Haka kuma, a barar dai, manyan ‘yan jarida na Arewa, kamar Malam Ibrahim Sheme da Malam Jaafar Jaafar, duk sun yi ƙoƙarin bin diddigin al’amarin ba tare da samun gamsasshen bayani ba.

A yanzu, na tado da bayanin nan ne domin mu ji daga bakin ka, shin me ake ciki game da wannan babban aikin alheri da ka ce ka ɗabbaƙa a bara? Har yanzu ka na ci gaba da ɗaukar nauyin yaran nan kuma wane matakin karatu su ke a yanzu?

Amsoshin da ka bayar za su inganta al’amarin nan kuma ka wanke wa masu kokwanto dukkan shakku. Haka kuma aikin naka zai zama abin koyi daga jaruman fim irin ka, kasancewar duk wanda ya assasa alheri kuma aka yi koyi da shi, zai rabauta ninkin-ba-ninkin.

Wassalam. Ina yi maka fatan alheri!

* Malam Bashir Yahuza Malumfashi shi ne Editan Labarai na jaridar Aminiya

Loading

Tags: Adam A. ZangoAminiyaBashir Yahuza Malumfashihausa actorshausa filmsIbrahim ShemeJaafar JaafarKannywoodprof ango abdullahi college
Previous Post

Umaru Ɗan Ɗanduna, direban da Shata ya waƙe, ya rasu ya na da shekara 88

Next Post

Cewar Rarara: Zan tsaya takarar Majalisar Tarayya a 2023

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Gwamna Abba Kabir Yusuf
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Alhaji Dauda Adamu Kahutu (Rarara)

Cewar Rarara: Zan tsaya takarar Majalisar Tarayya a 2023

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!