ƘUNGIYAR ‘Kannywood Family’ ta shirya gagarumin bikin karrama gwarazan Kannywood maza da mata.
Bikin wanda aka yi wa laƙabi da ‘Legendary Award Night’, za a gudanar da shi ne a gobe Litinin, 17 ga Fabrairu, 2025 da misalin ƙarfe 6:00 na yamma, a ɗakin taro na otal ɗin ‘The Afficent’ da ke Magaji Rumfa, Kano.
Mashirya taron sun ce biki ne da ya ƙunshi sada zumunci, haɗa kan juna, da zaman lafiya.
An kafa kwamitocin da za su jagoranci bikin, kamar haka:
- Kwamitin karɓar baƙi: Hauwa Waraka, Fati Muhammad, Esha Golden da Nura MC Khan.
- Kwamitin walwala: Hadiza Maikano, Danja, Fati Al-Amin da Maijidda Abbas.
- Kwamitin tsaro – Halisa Muhammad, Waziri Godowoli da Kalambaina Ikon Allah.
- Kwamitin ‘yan jarida: Mujallar Fim, Abba Pash, Sadamcy Photograpy da sauran bloggers.
- Kwamitin tattara bayanan waɗanda suka rasu: Hajiya Fatima, Hajiya Maryam CTV, Hajiya Zulai Bebeji, Hajiya Asma’u, Hafsat Suleiman da Fati Suleiman.
Shugabannin taron sun ce ƙofa a buɗe take ga duk mai son ba da shawara da gudunmawa.
Haka kuma katin gayyata yana hannun furodusa Yakubu Gwammaja, kowa a wurin sa zai karɓa.
Sannan ana gayyatar duk wani ɗan Kannywood, ba a ɗauke wa kowa ba.