JARUMI kuma mawaƙi a Kannywood, Yusuf Haruna (Baban Chinedu), ya ƙaryata masu cewa an ba su kuɗi ko gida ko mota shi da aminin sa mawaƙin siyasa, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), bayan ɓarnar da aka yi masu a ranar da Abba Kabir Yusuf ya lashe zaɓen Jihar Kano a matsayin gwamna.
Baban Chinedu ya yi bayani ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a Instagram da Facebook.
Ya ce, “Ina yi wa Musulmi na duniya gaba ɗaya barka da wannan lokaci na azumi. Yadda mu ka shigo shi lafiya, Allah ya sa mu ƙare shi lafiya. Kuma Allah ya ba mu ladan da ya ke cikin shi.”
Sai ya ci gaba da cewa, “Yawanci ni a azumi idan an yi magana ba na sa baki, amma ya kamata in yi magana saboda abu ne da ake so a cutar da ni, don haka na ga ya kamata in yi magana a kai.
“Akwai hotuna da ake ta sawa, wani ka ji ya ce an ba Rarara miliyan ɗari, an ba Baban Chinedu miliyan hamsin, an ba Rarara miliyan talatin, an ba Baban Chinedu miliyan goma, an ba Rarara gida da mota, an ba Baban Chinedu takalmin mota. All this one rubbish, ƙarya ne fa jama’a. Kamar mutum ne ya sare ka, kuma ya je ya na watsa maka ruwan batir, inda za a taimake ka, a gani don a ƙi taimakon ka.
“Yaya za ku zo ku riƙa yi mani ƙarya a cikin midiya? Duk abin da aka sa a cikin midiya cewa an ba mu ni da Rara, ƙarya ne, babu wanda ya ba mu, babu wanda ya ɗauki wani abu ya ba mu.
“Wannan abu asara ce Allah ya kawo, idan Allah ya yi za ka maida. Ina so mutane su sani cewa da arziki da rashin shi daga Allah ne. Wallahi mutum bai iya yi maka arziki, sai dai ya zama sila.
“Innallaha yarzuƙun nasi binnas. Za ka iya kuɗi ta hannun wani, amma ‘Innallaha’ ya zo da farko fa, ba wai nas yarziƙun nasi ba ne, a’a za ka iya yin wahala ka bi mutum a siyasa ka yi komai, amma in ba ka da rabo a jikin shi, bai isa ya yi maka arziki ba wallahi.
“Da arziki da rashin shi duka daga Allah ne. Ni ban taɓa sa wa a rai na wallahi wani zai iya biya na ba. Amma idan ka ga abin da na yi asara ya dawo, Allah ne ya yi mini. Ba na tunanin wani zai maida mani. An yi hira da ni, na yi maganar iya abin situdiyo. Da na dawo na zo Kano na ga ɓarnar da aka yi mana, wallahi, tallahi abin ya tada min da hankali. I was shocked!
“Da ma ni ban yi maganar asarar da Rara ya yi ba. Asarar da Rara ya yi, wanda na gani da ido na, wanda ido Allah ya nuna mani, to ba zan yi rantsuwa ba, amma ina ganin cewa babu wani ɗan siyasa daga sama har ƙasa da zai iya biyan Rara wannan kuɗin, sai dai a rage masa zafi, amma babu wanda zai iya dunƙule kuɗi a lokaci ɗaya ya biya Rara abin da ya yi asara, babu shi, sai dai ya taimake shi, zai iya yiwuwa, amma zai wahala, sai dai ya rage mashi.
“Ko ni nan ɗan ƙarami da ban kai shi asara a ciki ba, wanda na ke bidiyo, waɗanda su ka san abin da na yi asara, waɗanda su ka san abin da aka ɗauka, akwai lokacin da na kawo kaya sun half trailer, kayan restaurant da na ke buɗe wa ne. Ina da mashin, mashin na ‘ice cream’ da sauran su, wanda su kaɗai sun fi kayan miliyan sha wani abu. Ban da kayan sound, ka je ka duba.
“Akwai mashin ɗi na da na saya kusan miliyan uku da wani abu, na gan shi a station, duk inda aka kama kaya a station ɗin Kano babu inda ba kaya na. Ni kai na da na zauna da na zo na yi lissafi na yi asara ya fi na miliyan arba’in da wani abu, na Rara kuma ba a magana.
“Wallahi ban san Rara ya yi wannan asarar ba sai da ido na ya zo na gani. Waye zai ɗauki kuɗi ya biya ka? Kuma in ka na sa rai wani ya yi maka arziki, you are wasting your time, it’s only God that gives and takes. Nobody can give you, nobody can take from you, except God. Allah ne kaɗai zai yi maka, kuma a haka da ni da Rara da sauƙi a na mu, domin Allah ya rufa mana asiri. Akwai The King, akwai Ahmad M. Sadiq, wanda su da wannan shagunan su ka dogara, mu inda aka shiga aka rusa mana, mun san yaran mu na cin abinci, amma ba da su mu ka dogara ba. Akwai wanda da iya nan su ka dogara, gaba ɗaya an ƙone nasu, an kwashe, ba abin da ya rage masu.
“Ni yanzu ko wannan abin da aka yi mani, wallahi ban karye ba, wallahi alhamdu lillahi. Allah ya rufa min asiri. Idan Allah ya yi maka ni’ima, ka nuna. Alhamdu lillahi, na gode wa Allah. An yi min ɓarna iya ɓarna.”
Baban Chinedu ya ƙara da cewa, “To, akwai magana da zan bayar a nan wurin, wanda ban taɓa faɗi ba. Ya kamata in nuna wa mutane menene bambancin Baban Chinedu da Rara. Saboda wani lokaci ana ganin mu kamar ba a san wannan bambanci ba.
“Idan Rara ya yi abu, sai a ce don me zai yi kaza, ai ya yi butulci. A’a, ya kamata ku san bambancin Baban Chinedu da Rara.
“Rara bai taɓa zama yaron Shekarau ba tun da ya ke. Rara bai taɓa zama yaron Kwankwaso ba tun da ya ke. Amma Baban Chinedu yaron Kwankwaso ne. Rarara yaron T. Gwarzo ne. Ku je ku bi rekod. In ma ba ku sani ba, ku je ku ɗauko waƙoƙin sa na baya. Ni kuma yaron Kwankwaso ne. Mu na da bambanci. Gidan Kwankwaso ko ba na gidan, ina kiran shi maigida ne. Shi kuma ko ba ya gidan T. Gwarzo ya na kiran T. Gwarzo maigidan shi.
“Mu na da bambancin gida, Allah ya haɗa tafiyar tare, mu na neman abinci tare, amma mu na bambancin gidaje. Shi maigidan shi T. Gwarzo ne. Shekarau ba maigidan Rarara ba ne, Kwankwaso ba maigidan Rara ba ne, sai dai ya yi tafiyar shi. Kamar ni ne da Buhari yanzu, na yi tafiyar Buhari, kuma har yanzu ina tafiyar Buhari, amma Buhari ba maigida na ba ne, amma Kwankwaso maigida na ne, ba ma shi kaɗai ba ne ne. Ina so ka san bambancin wanda ka ke bi da kuma maigidan ka.”