ƘUNGIYAR Furodusoshin Arewa (AFPAN), reshen Jihar Kano, ta ziyarci Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, domin taya shi murnar sabon matsayin da ya samu.
Membobin ƙungiyar sun kai ziyarar ne a ranar litinin 31 ga Yuli, 2023 a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Malam Gambo Musa, da mataimakiyar sa, Hajiya Mansurah Isah.
Da ya ke jawabi kan manufar ziyarar tasu, Gambo Musa ya ce sun je ne domin taya El-Mustapha murnar kama aiki da kuma fatan alheri.
Ya ƙara da cewa kasancewar El-Mustapha mutum mai kishin masana’antar Kannywood, sun san zai kai ta ga cigaban da ake buƙata fiye da yadda ake zato, don haka ne ma tun daga yanzu su ka yi wani tsari na karrama shi su ka so da hoton sa na musamman domin karrama shi.
Ya ce: “Don haka mu na yi maka fatan alheri da kuma samun nasara a jagorancin ka.”

A nasa jawabin, El-Mustapha ya nuna farin cikin sa tare da godiya bisa zaɓar sa da ƙungiyar ta yi domin ta karrama shi, sannan ya yi wa ƙungiyar alƙawarin yin aiki tare domin kawo wa hukumar da kuma Jihar Kano cigaban da ake buƙata.
Shi dai El-Mustapha, tun bayan kama aikin sa a ranar 25 ga Yuli ɗaiɗaikun mutane da kuma ƙungiyoyi a Kannywood su ke yin tururuwa zuwa ofishin sa domin kai masa ziyara da kuma murnar kama aiki a matsayin sa na ɗan cikin su.
Rukunin farko da su ka fara kai masa ziyara su ne Majalisar Dattawan Kannywood a ƙarƙashin jagorancin Malam Khalid Musa da su ka haɗu dukkan su su ka halarci ofishin don taya shi murna da yi masa fatan Allah ya taya shi riko.
Ita ma ƙungiyar ‘Kannywood Movement for Kwankwasiyya’ ta su furodusa Alhaji Sheshe ta kai irin wannan ziyarar ga El-Mustapha.
Ƙungiyar masu ba da umarni, wato ‘Screen Guild of Directors’ wadda Aminu S. Bono ya ke jagoranta, ita ma ta kai wa shugaban ziyarar taya murna da kuma fatan Allah ya sa ya yi jagoranci cikin adalci da sanin ya-kamata.
Haka ‘ya’yan ƙungiyar masu gala da ta ‘yan kasuwar fim su ma sun kai makamanciyar irin wannan ziyarar taya murna.

