• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ɓatagari sun banka wa ofisoshin INEC 3 wuta a Ebonyi

by DAGA WAKILIN MU
May 19, 2021
in Nijeriya
0
Ɓatagari sun banka wa ofisoshin INEC 3 wuta a Ebonyi
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WAƊANSU mutane waɗanda ba a san ko su waye ba sun banka wa ofisoshi uku na Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) wuta a Jihar Ebonyi a yau Laraba.

Ofisoshin su ne na ƙananan hukumomin Ezza ta Arewa da Izzi.

Jami’in Yaɗa Labarai na INEC a jihar, Mista Cornelius Ali, wanda ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai a Abakaliki, ya ce ɓatagarin da su ka aikata hakan sun ƙone ofisoshin tare da injinan janareto da rumfunan zaɓe da wasu muhimman kayayyakin zaɓe.

Ya ce shugabannin hukumar sun kai ziyarar gani da ido zuwa ofisoshin da gobarar ta shafa da nufin sanin yawan ɓarnar da aka yi.

Sai dai ya kwantar da hankali kan fargabar da ake yi kan ko wannan ɓarna za ta kawo barazana ga shirin da ake yi na gudanar da aikin rajistar masu zaɓe wanda za a yi a watan Yuni.

Mista Ali ya ce, “A safiyar yau, mun samu rahoton cewa wasu mutane sun kai hari tare da banka wa ofisoshin mu na ƙananan hukumomin Ezza ta Arewa da kuma Izzi wuta, inda su ka lalata muhimman kadarorin hukumar.

“Da mu ka je can, mun ga an ƙone gine-ginen da ofisoshin mu ɗin ke ciki yayin da kuma an ragargaza injinan janareto da rumfunan zaɓe da sauran kayayyakin INEC da ke cikin waɗannan ofisoshin baki ɗaya.”

Kakakin hukumar ya ƙara da cewa ɓatagarin sun ja wa hukumar babbar asara, to amma ya ce harin ba zai rage mata ƙwarin gwiwa ba wajen sauke nauyin da aka ɗora mata na yi wa jama’a aiki.

Ita kuwa da aka tuntuɓe ta, Jami’ar Yaɗa Labarai ta Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Ebonyi, Missis Loveth Odah, cewa ta yi aiki ya yi mata yawa, ba za ta iya magana da ‘yan jarida ba.

Loading

Tags: Independent National Electoral CommissionINEC
Previous Post

Farfesa Abdalla ya ragargaji ‘yan Kannywood kan neman ilimi da ƙwarewa

Next Post

Waƙa: Nura M. Inuwa maƙura ne!

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Waƙa: Nura M. Inuwa maƙura ne!

Waƙa: Nura M. Inuwa maƙura ne!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!