• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Waƙa: Nura M. Inuwa maƙura ne!

by DAGA BAMAI DABUWA KIRIKASAMMA
May 20, 2021
in Mawaƙa
0
Waƙa: Nura M. Inuwa maƙura ne!
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WAƘA baiwa ce da ba kowane mutum ke da ita ba. Duk wanda zai iya zama ya tsara ko ya rera waƙa, wannan mutumin na da matuƙar baiwa. Idan har akwai mutane na musamman keɓantattu, to mawaƙa ne.

Fasahar da ke cikin tsararriyar waƙa ta wuce duk yadda ake tunani. Wani zai ɗauka abin da ake buƙata a waƙa kawai ƙafiya ce. Da ita ne ma kawai su ke auna haɗaɗɗiyar waƙa. Ba haka ba ne, amma dai ƙafiyar na ɗaukar kaso mafi tsoka idan da za a karkasa da bai wa kowane tsari da salon waƙa maki.

Kusan duk mawaƙan Hausa sun ƙware ainun wajen tsara waƙa da sarƙa ta da haɗaɗɗun ƙafiya. Ya na daga kyakkyawan misali idan mu ka duba wata waƙar bege da Umar Abdul’azeez (Fadar Bege) ya yi, lokacin ya na da rai, inda ya ke wa Allah maɗaukakin Sarki kirari kamar haka:

“Ka kaɗaita abin bauta mai riƙe lamari na,Allah buwayi ina roƙo don isar Annabi na,Ka ƙara haske a harshe na da zan yaba wa gwani na,Kai ka ke yadda duk ka ga dama kar ka shafe batu na,Roƙo na ke yi da babbar murya ya maji roƙo na,Tsira aminci ka ƙara wa uban dukkan alami na,Mahmudu wanda ya sauka a Makka sannan ya koma Madina.”

Wani abin mamaki da Fadar Bege shi ne wasu baitukan a majalisi ya ke yin su da ka (wato a lokacin ya ke ƙirƙira.)

Nura M. Inuwa ya na rera sabuwar waƙar sa ta ‘Garƙami Wandon Ƙarfe’ ga dandazon masoyan sa a wasan da ya yi a filin Trade Fair na Kano ranar Talata da ta gabata

A ɗayan bangaren na mawaƙa, idan mu ka kalli Nura M. Inuwa, sai duk wani lissafi ya birkice. Nura ya yi ƙwarewar da ya ke iya juya waƙa yadda ya so. Ko da yake wasu za su iya cewa ai ya na samun isasshen lokaci ne na tunani da tsari, shi ya sa waƙoƙin ke kyau. Ko ma dai yaya ne, ya iya. Sannan a duk lokacin da ya saki album, ana ajiye waƙar kusan kowa ne, a saurari tasa. Saboda ya iya.

Dangane da ƙafiya a waƙa, bari ka ji yadda shi ya ke yin ta da salo, wanda ba kowa ke yi ba. Mu ɗauki misalin wannan waƙar da baitin ta ya fara:

“Ke ce ta fari zo gimbiya amarya,Haƙuri za ki yi komai da lokaci ga shi naki ya zo mai fari na hali.”

A wannan waƙar ya saki fasahar da keta tunani, yadda ya ke jan dogon baiti masu sarƙaƙiyar da bagware ba zai iya biyawa ba. Misali:

“Gatan tuwo miya ce ba da wai ba a daka a raya jure hakan waye ne saman ki kalwa?Kanwa uwar gami, ke ce ƙure wa masu zunɗen ki sun manta sun yi shuka idon makwarwa.Na yo batun a da can mun ji kwalla ta fi fanteka, zurfin tukunya ma ba ya kai na garwa.Aiki da hankali ba kamar ƙwaƙwalwa ku yi ta yin shewa kar ku yi rayuwa wacce za ta zamto kamar kashin dankali.”

A misalin wannan baitin, kalmar “wa” ce ƙafiyar da ya yi amfani da ita. Ba kuma yadda ta ke hawa ba ne abin burgewa. Yadda a ƙarshen baitukan ya ke kuma shigar da ƙafiyar a duk inda aka samu saukar sauti ko hawa. Kamar dai wajen da ya ce “ƙwaƙwalwa” da kuma “shewa”.

Daga ƙarshe kuma ya na ƙare kowane baiti da kalmar ‘li’ saboda ita ce ƙarshen amshin farko, ‘hali’.

*Bamai Dabuwa Kirikasamma, wanda marubucin zube ne kuma mai sharhi kan rubutun zube, mazaunin Jihar Jigawa ne

Loading

Tags: Hausa musicmawakan hausaNura M. Inuwa
Previous Post

Ɓatagari sun banka wa ofisoshin INEC 3 wuta a Ebonyi

Next Post

Shugaban INEC na so jama’a su kare kayan hukumar daga masu ƙona su

Related Posts

Za a gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ran Asabar
Mawaƙa

Za a gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ran Asabar

August 23, 2026
‘Ya’ya biyu mata na Mudassir Kasim sun yi saukar karatun Alƙur’ani
Mawaƙa

‘Ya’ya biyu mata na Mudassir Kasim sun yi saukar karatun Alƙur’ani

August 2, 2026
Sani Danja: Waƙar ‘Barau Jigijim’ ta tayar da ƙura, ya ƙaddamar da gasa a kan ta
Mawaƙa

Sani Danja: Waƙar ‘Barau Jigijim’ ta tayar da ƙura, ya ƙaddamar da gasa a kan ta

July 15, 2026
Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar
Mawaƙa

Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar

December 11, 2025
Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Next Post
Shugaban INEC na so jama’a su kare kayan hukumar daga masu ƙona su

Shugaban INEC na so jama'a su kare kayan hukumar daga masu ƙona su

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!