• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Farfesa Abdalla ya ragargaji ‘yan Kannywood kan neman ilimi da ƙwarewa

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
May 19, 2021
in Labarai
0
Farfesa Abdalla ya ragargaji ‘yan Kannywood kan neman ilimi da ƙwarewa
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TSOHON Mataimakin Shugaban Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN),  Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya ƙwanƙwashi ‘yan fim ɗin Hausa tare da ƙalubalantar su da cewa in dai su na so a kira su ƙwararru, to sai sun nemi ilimi mai zurfi a kan harkar fim.

Ya ce: “Idan ka isa kai cikakken ɗan fim ne, in gan ka da digiri a fim, in gan ka da Masters a fim, in kuma gan ka da PhD duk a fim, saboda fim ƙwarewa ne, ba kasuwanci ba ne, sana’a ce. In ka ɗauki matsayin cewa kai ɗan fim ne, dole ka ɗauke shi sana’a.”

Haka kuma ya bayyana cewa komawa YouTube da ‘yan masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood su ka yi su na nuna finafinan su, tare da shirya finafinai masu nisan zango, duk abubuwa ne da shi ɗin nan ya kawo shawara a kan a yi su sama da shekara goma da ta gabata, amma ‘yan fim su ka yi watsi da shawarar.

A cewar sa, a wancan lokacin sai ‘yan fim su ka dinga sukar sa, har wasu na cewa ya na musu hassada ne ko ya na so ya yi musu wayo ya ƙwace harkar.

Farfesan ya faɗi haka ne bayan an karrama shi a lokacin bikin cikar kamfanin Eagle Eye na jarumi Tijjani Asase shekara ɗaya da fara gudanar da ayyukan shirya finafinai, musamman nuna fim mai dogon zango na ‘A Duniya’ a YouTube.

An yi bikin a ranar Lahadi, 16 ga Mayu, 2021 a wurin taro na Banana da ke birnin Kano.

Bayan ya karɓi kyautar karramawar ne Farfesa Abdalla, wanda yanzu malami ne Jami’ar Bayero, Kano, ya yi jawabi inda ya ragargaji ‘yan fim kan sukar da su ka riƙa yi masa a baya, yanzu kuma ala tilas sun dawo kan turbar da ya ɗora su amma su ka ƙi bi. 

A jawabin, ya bayyana irin ƙalubalen da ya fuskanta a yayin da ya fara nazari kan masana’antar da ma irin kallon da wasu daga cikin jigajigan Kannywood su ka riƙa yi masa. 

Ya ce, “Ina ɗaya daga cikin mutanen da su ka fara shigowa wannan masana’antar saboda nazari sakamakon ina wurin da ake ce wa Tsangayar Koyar da Ilimin Sadarwa  wato ‘Mass Communication’.

“A lokacin da mu ka shigo mu na nazari a kan abin da ya ke faruwa a kan finafinan Hausa, babu irin ƙalubalen da ba mu sha ba, babu irin zagin da ba mu sha ba. An ce hassada mu ke, an ce kushe mu ke, an ce ba ma son cigaban mutane.

“Kuma duk waɗanda su ke ‘yan fim a nan, waɗanda shekarun su su ka haura 45, sun san abin da mu ke nufi idan na ce an mana gori da cewa ‘wanda duk ya raina tsayuwar wata, to ya hau ya gyara’.

“To Allah ya kawo mu wani lokaci yanzu wanda masana’antar fim ta mutu amma kuma ta na nan da ran ta. Abin da na ke nufi da wannan shi ne shekara kusan 25 da ta wuce a Kwaliti da ke Zoo Road, yaro ya fito ya ce harka ta koma hannun yara. Duk wanda ya shekara 45 a cikin wannan masana’anta ya san me na ke nufi.

“Sannan yaro ya fito ya ce, ‘Idan ka isa kai ɗan fim ne, mu haɗu a Bata’. Yau ina Bata? Yau ina Ƙofar Wambai? Yau ina Traffic? 

“Shi ya sa na ce Kannywood ta mutu sannan kuma na ce ta na nan da nisan kwana.”

Farfesa Abdalla ya ci gaba da cewa: “Abin da mu ka dinga faɗa a shekara ta 2001, a rungumi harkar yanar gizo-gizo, wato intanet, aka ce ba za a yi ba, wanda da yawa daga cikin ‘yan fim da su ke sana’ar yanzu, mu mu ka buɗe musu imel, a lokacin ba su san shi ba; mu mu ka fara kafa dandalin nazarin finafinan Hausa a Yahoogroups, lokacin ba WhatsApp ba Facebook ba Instagram ba Telegram babu wayar hannu; mu mu ka fito da shi. 

“Dalilin da ya sa mu ka ce a yi wannan, saboda a yaɗa finafinan Hausa duniya ta sani, a san ga abin da mu ke yi, a san kuma mu ma mu na da fasaha. Aka ce ba za a yi ba, mutane su ka ce ‘yan boko ne mu, mu na so mu yi wa mutane wayo. 
“Mu ka ɗauko Turawa daga Ingila. British Council da French Embassy da ma American Embassy, su ka zo duk domin a haɗa kai a haɓaka abin, saboda a tallata finafinan Hausa duniya ta san me mu ke ciki. Wasu daga cikin ‘yan masana’antar su ka ce wayo mu ke so mu yi musu.

Ubandoman Ringim, Dakta Munzali Taura (a dama), gab da zai miƙa kyautar karramawa ga Farfesa Abdalla Uba Adamu

“Ɗaya daga cikin wanda ya zo daga British Council ya na so ya taimaka mana, kuma ya na daga cikin mashirya fim ɗin ‘Mission Impossible’. Ya zo zai kawo mana sanayya, zai kawo mana ilimi, amma aka bijire.

“Kuma dalilin da ya sa ‘yan fim a lokacin su ka bijire shi ne sun ce ba sa yi wa kowa fim sai ƙananan yara da mata. Mu ka ce, ‘A’a, ku yi wa duniya, duniya ta san abin da ku ke ciki. Ana yin finafinai a ƙasashe irin su Chadi, Senegal, Mauritaniya, duk ana yin finafinai a nan wurin, kuma ana yin nazarin finafinan a duniya. Idan ka je jami’o’i na duniya irin su Amerika da su Germany, su na nazarin waɗannan finafinan, amma ban da namu’.”

Har wa yau farfesan ya bayyana cewa su manazarta ba su ce a daina fim ba, amma a canza jigon labari.

“Da zarar mun faɗi a canza jigo, sai a ce buƙatar mu mu ke yi wa. Waɗanda su ke sayar da kaset sai su ka shigo su ka zama ‘yan fim. Sai ya zamto ɗaukakar fim a wannan lokacin shi ne za a kawo jarumi a ce a sa shi a cikin fim. ‘Idan aka saka min wane, fim ɗi na zai tashi ya sayu!’

“Amma duk ma ba wannan ne illa ba. Fim labari ne. A manta da batun kyamara. Finafinan da ake yi a da a Amerika, wanda a da babu wata ƙayatuwa ta kyamara, yanzu su ne su ka zama zakarun gwajin dafi. 

“Don haka ba kyamara ce fim ba. Da waya ‘i-phone’ yanzu ana yin fim. Kar ka ce sai ka na da babbar kyamara za ka yi fim. Shi fim labari ne; idan ba ka da labari, ba ka da fim.

“A nan ma mu ka zo mu ka ce a zo a inganta labari. Har Turawa mu ka ɗebo domin su koya mana yadda ake rubuta labari. Har kuɗi mu ka ba su. Amma aka zo aka ce mu na so mu yi babakere, mu handame masana’antar, sai dai mu yi gaba!

“Duk da cewa a wancan lokacin ba fim ɗin da ya fi tasiri kamar na Indiyawa, sai kuma aka koma ana kwafo labarin da su ke yi, ana rawa da waƙa saboda a lokacin idan ka kai fim ɗin ka kasuwar Bata ka zama sarki.

“Akwai lokacin da wasu jarumai a nan kasuwar Malam Ƙato za su yi wata gasa cewa kowa ya ɗauki motar sa su je su daki garu, gobe a ga waye zai sayo sabuwa. Lokacin ana ji da  kasuwar fim ɗin. Sai mu ka ce, ‘Ba kan mota za ku kashe kuɗi ba, a kan labari za ku kashe kuɗi, duniya ta san abin da mu ke yi’. Aka ce, ‘Farfesa, idan ka raina tsayuwar wata, ka hau ka gyara.’ Na ce, ‘Allah ya bada haƙuri!’

“Amma duk da haka, a lokacin da aka zo za a shirya taron finafinan Hausa, ni aka je aka kirawo dai aka ce na zo na shirya. Amma da abin ya ishe ni ma daga baya na ce na bari, na koma ɓangaren ‘yan Hip Hop. Duk na watsar da wannan tarkacen ‘yan fim ɗin. Sai mu ka ce da su, ‘Tunda ya ke ni na bari, na kauce na ƙyale ku, amma wallahi akwai lokacin da za ku zo ku sake neman mu, kuma idan ku ka zo neman namu mu na nan ba za mu gudu ba saboda ‘yan’uwan mu ne ku, al’adar mu ce, rayuwar mu ce.”

Haka kuma ya tuno da cewa akwai lokacin da su ka bada shawara kan a tashi a rungumi dirama mai dogon zango, wato ‘series’, musamman irin ta su Ƙasimu Yero, amma aka baɗa masu toka a fuska.

Da ya juyo kan taɓarɓarewar kasuwancin fim wanda a baya aka dinga nuna isa da fariya a kan sa, Farfesa Abdalla ya ce, “Yanzu dai kasuwar Bata ta ci wuta, waɗannan ƙananan yaran da su ke maganar YouTube a lokacin da ake wannan taƙaddamar na ‘mu haɗu a Bata’, waɗansu ma a makarantar firamare su ke, yau kuma yaran ne dai su ne shegun. Yaro da ‘yar kwamfutar  sa da ‘yar datar sa da ba ta shige ta ƙananan kuɗi ba ya na zaune a gida ko ya na kwance a gida ana matso masa daloli. Kai kuma ka je ka yi wani kaset, an bar ka da kwantai, ka rasa yadda za ka yi da shi!

“To yanzu dai kun ga abin da mu ke cewa: a rungumi intanet ɗin, kuma a canza alƙiblar labari.

“Saboda haka na yi murna da Allah ya ba ni dama a wannan taron mu ka zo maudu’in da mu ke ta ƙoƙarin mutane su zo su sani su ka ƙi tun shekara ashirin da ta wuce, yau sai ga shi an zo, yau sai ga shi ‘series’ ɗin nan da ake gudu, ake cewa menene menene ‘ai dirama ce ta su Ƙasimu Yero, ai su Ƴasimu Yero sun wuce’, sai ga shi yau shi ake ɗaukakawa, yau ga shi an samo sabbin wuraren tura saƙwannin finafinai, yau sai ga shi ɗan fim a Kano ya na so a ga fim ɗin sa a Australiya da South Africa, ya na so duniya ta ga abin da ya ke yi. 

“Kuma mu na faɗa: idan ka na so duniya ta ga fim ɗin ka, dole sai ka gyara labarin ka. Ba za ka je ka ɗauko labarin Indiya ka ce za ka wanke shi ka yi mai kwaskwarima ka ce shi ne a matsayin wakilin al’adar Hausawa ba mutum ya kalla, a’a, kai za ka yi asara. 

“Saboda haka yanzu alhamdu lillahi an samu sabuwar alƙibla, sai a ɗauka a yafa a kuma inganta ayyuka.”

Da ya ke ƙarƙare bayanan sa, malamin ya jefa wasu tambayoyi tare da ƙalubalantar ‘yan Kannywood da cewa: “Da ma ina ta fatan ranar da Allah zai ba ni dama na maida martani a kan (batun) ‘duk wanda ya raina tsayuwar wata ya hau ya gyara’. Ni, Farfesa Abdalla Uba Adamu, ba ma wata ba, tauraruwa na hau na gyara! Yau wata na uku da sauka daga kujerar Mataimakin Shugaban jami’ar NOUN, na yi kuma shekara biyar a matsayin Mataimakin Shugaban makarantar.

“Ina Vice-Chancellor mu ka fito da ‘film programme’, BSc Film Production. Idan ka isa kai kuma, ka na so ka nuna kai ingantaccen ɗan fim ne, to ka je National Open University ka yi BSc Film Production, saboda fim abu ne na ilimi, ba wai na jahilci ba. Saboda haka mun riga mun fito da shi. Amma abin kunya, babu ɗan  Kano da ya yi rajista!

“McArthur Foundation wata ƙungiya ce mai tallafa wa jami’o’i a Nijeriya. Sun bada kuɗi a yi ‘postgraduate programme’ a Film and Multimedia. Ɗaya daga cikin abin da za a ɗaukaka a ‘programme’ ɗin shi ne ‘streaming services’ irin su Netflix da su YouTube, kuma a shirye mu ke mu koya muku yadda za a yi amfani da su.

“Saboda haka, ni ma ga nawa ƙalubalen nan: idan ka isa kai cikakken ɗan fim ne, in gan ka da digiri a fim, in gan ka da Masters a fim, in kuma gan ka da PhD duk a fim, saboda fim ƙwarewa ne, ba kasuwanci ba ne, sana’a ce. In ka ɗauki matsayin cewa kai ɗan fim ne, dole ka ɗauke shi sana’a. 

“Sannan mu canza akalar labaran da mu ke yi, mu ɗauki maudu’in da ya ke faruwa yau da kullum mu na yin fim a kan sa kamar yadda na gani a cikin wannan fim na ‘A Duniya’. 

“Ya za a yi mu warware matsalar da ta ke damun mu, mu kuma faɗakar da jama’a kan wani baƙon al’amari da mu ke ciki? To wannan shi ne fim. Wannan kuma shi zai jawo mana mutane su zauna su ga me mu ke yi na cigaba na finafinan Hausa. 

“Amma in dai za ka zauna ka na amfani da aro na wani don kawai ka burge, to waɗanda ka ke burgewar yanzu an daina burge su. Amma idan aka zo aka yi abin da ya shafi rayuwar mutane kamar su daba, satar mutane da ƙwacen waya, mutane za su so su gani. Kuma irin wannan shi ake yi a wasu ƙasashen da ke faɗin duniya.”

Tun a farkon wannan jawabi nasa dai sai da Farfesa Abdalla Uba Adamu ya bayyana jin daɗi kan karramawar da jarumi Asase ya yi masa, ya ce ita ce irin ta ta farko da aka yi masa a Kannywood.

Haka kuma ya bayyana ta a matsayin karramawa mafi muhimmaci a rayuwar sa.

Ya yi nuni da cewa sama da shekara goma da fara gwagwarmayar sa a Kannywood, bai taɓa samun karramawa daga masana’antar ba sai yanzu.

Ya ce, “Duk da da na samu lambobin girmamawa da dama, wasu ma na bogi ne, wasu da kuɗi aka ban, amma duk ba su da amfani da muhimmancin da wannan ta ke da shi.”

Farfesa Abdalla Uba Adamu ya na gabatar da jawabin sa. A bayan sa, Tijjani Asase ne, a dama kuma Ubandoman Ringim, Dakta Munzali Taura

Loading

Previous Post

‘Yan wasa 500 za su fito a diramar ‘Gidan Dambe’, inji Tantiri

Next Post

Ɓatagari sun banka wa ofisoshin INEC 3 wuta a Ebonyi

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Ɓatagari sun banka wa ofisoshin INEC 3 wuta a Ebonyi

Ɓatagari sun banka wa ofisoshin INEC 3 wuta a Ebonyi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!