SHAHARARREN kamfanin shirya finafinan Hausa, Abnur Entertainment, wanda ya shirya fitaccen shirin ‘Ƙaddara’, ya nesanta kan sa daga kalaman da jaruma Nafisa Abdullahi ke yi a shafukan sada zumunta kan batun aure, musamman waɗanda suka jawo ce-ce-ku-ce a cikin ‘yan kwanakin nan.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a yammacin yau Litinin.
A cewar kamfanin, ra’ayoyin da Nafisa ta bayyana a kan batun aure nata ne na ƙashin kan ta, kuma ba sa wakiltar manufofi ko aƙidar fim ɗin ‘Ƙaddara’ da kuma masu shirya shi.
Kamfanin ya jaddada cewa yana mutunta darajar aure tare da muhimmancin sa a addinin Musulunci da kuma al’adun Hausawa da sauran al’ummomin Nijeriya.
Sanarwar ta ƙara da cewa masu shirya fim ɗin ba sa goyon bayan duk wani furuci ko matsayi da zai iya rage martabar aure, ko kuma ya haddasa ruɗani da saɓani a tsakanin jama’a.
“Mun yi imani cewa aure wata muhimmiyar cibiya ce ta gina iyali da al’umma, don haka duk wani ra’ayi da ya saɓa wa wannan fahimta ba ya wakiltar kamfanin mu ko ayyukan mu,” inji Abnur.
Saboda haka, kamfanin ya yi kira ga masoya da masu kallon fim ɗin ‘Ƙaddara’ da su bambance tsakanin ra’ayin mutum da kuma manufar aikin fasaha da kamfani ke gabatarwa.
Tun bayan da Nafisa Abdullahi ta bayyana wasu ra’ayoyi kan rayuwar aure a shafukan sada zumunta, lamarin ya tayar da ƙura, inda jama’a suka riƙa bayyana mabambantan ra’ayoyi kan batun.
Yayin da wasu suka nuna rashin jin daɗin su tare da sukar kalaman nata, wasu kuwa sun bayyana cewa za su daina kallon duk wani fim da jarumar ta fito a ciki. Sai dai akwai kuma waɗanda suka kare haƙƙin ta na bayyana ra’ayin ta, suna masu cewa bambancin fahimta abu ne da ke faruwa a cikin al’umma.
![]()







