ƘUNGIYAR ‘Yan Fim Masu Goyon Bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin ya sake yin wa’adi na biyu ta gudanar da taron addu’a da saukar Alƙur’ani mai tsarki domin neman zaman lafiya da kuma kawo ƙarshen matsalolin tsaro da suka addabi Nijeriya.
A taron da aka gudanar a yau Litinin a Filin Baje-koli da ke kan titin Gidan Zoo a cikin birnin Kano, membobin ƙungiyar daga sassa daban-daban na ƙasar nan tare da dattawan ƙungiyar sun halarta.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Dauda Kahutu (Rarara), ya ce an shirya taron ne domin roƙon Allah ya kawo ƙarshen matsalolin tsaro da suka dabaibaye ƙasar nan.

Ya ce: “Mun shirya wannan taron addu’a ne domin mu roƙi Allah ya kawo mana ƙarshen matsalolin tsaro da ake fama da su a Nijeriya. Wannan matsala ta shafi kowa da kowa, musamman mu a Arewa, domin idan ba ta same ka kai-tsaye ba, za ta shafi wani na kusa da kai.”
Rarara ya ƙara da cewa matsalar tsaro ba ta gwamnati kaɗai ba ce, illa ta shafi dukkan al’umma, don haka wajibi ne kowa ya taka rawar da ta dace wajen nemo mafita.
“Harkar tsaro ba ta mutum ɗaya ba ce, ko shugaba ko talaka. Dole ne mu haɗa kai wajen samar da mafita ta hanyar addu’a da kuma taimaka wa hukumomin tsaro ta hanyar kai rahoton duk wani mutum ko motsi da ake zargi,” inji shi.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya tona asirin duk masu hannu wajen haddasa matsalolin tsaro, ko suna cikin al’umma ko kuma a cikin gwamnati.
Bayan jawabin sa ne aka fara saukar Alƙur’ani, sannan aka ci gaba da gabatar da addu’o’i na neman zaman lafiya, tsaro da haɗin kan ƙasa.
A cikin addu’ar kammalawa, Malam Nura Hussaini ya yi addu’o’i masu tsawo, inda ya roƙi Allah ya kawo ƙarshen duk wani nau’in fitina da rashin tsaro da ake fama da shi a ƙasar nan.
Ya ce: “Ya Allah, Kana ganin halin da muke ciki na wahala da rashin tsaro. Muna roƙon Ka Ka kawo mana agaji, Ka hallaka masu tayar da fitina a duk inda suke. Duk wanda yake da hannu a wannan matsala, idan mai mulki ne Ka ƙwace mulkin sa, idan mai arziki ne Ka rage masa ikon da yake amfani da shi wajen cutar da jama’a.”

Bayan kammala addu’ar, aka yanka sa da rago tare da raba sadaka ga mahalarta taron da sauran mabuƙata.
An gudanar da taron cikin lumana, inda aka fara shi lafiya kuma aka kammala shi lafiya.
![]()







