FITACCIYAR jarumar Kannywood da Nollywood, Rahama Sadau, ta bayyana cewa rasuwar mahaifin ta, Alhaji Ibrahim Sadau, ta bar mata babban giɓi a rayuwar ta, wanda har yanzu ba ta iya cike shi ba, yayin da ake cika shekara ɗaya da rasuwar sa.
Rahama ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafukan ta na sada zumunta a yau Litinin, inda ta tuna da mahaifin ta tare da bayyana irin kewar da take yi masa.
“Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un. Tsawon shekara guda kenan ba tare da na sake jin kiran mahaifina ba, ba tare da na ziyarce shi ba, kuma ba mu sake zama tare kamar yadda muka saba ba,” inji ta.
Alhaji Ibrahim Sadau dai ya rasu ne a ranar Asabar, 22 ga Yuni, 2025, kwana ɗaya bayan dawowar sa daga gudanar da aikin Hajji.
Jarumar ta ce rashin sa ya haifar mata da wani babban giɓi a rayuwar ta wanda kalmomi ba za su iya bayyana girman sa ba.
“Rashin mahaifi na ya sanya wani giɓi a rayuwa ta wanda kalmomi ba za su iya bayyana girman sa ba, musamman ganin cewa mun gudanar da bukukuwan Sallah guda biyu ba tare da kasancewar sa a cikin mu ba,” inji ta.
Jarumar ta ƙara da cewa duk da yawan abubuwan tunawa da take da su game da mahaifin ta, ta fi mayar da hankali wajen ci gaba da yi masa addu’a.
“Duk da irin yawan abubuwan tunawa da nake son rubutawa game da mahaifi na, na fi zaɓar ci gaba da yi masa addu’a a kullum har zuwa ƙarshen rayuwa ta, domin a gani na babu kyautar da ta fi wannan ga mamaci,” inji ta.
Rahama ta bayyana mahaifin ta a matsayin uba nagari wanda ya rayu cikin karamci, nasiha da kyawawan halaye, tana mai cewa soyayyar sa, kulawar sa da jagorancin sa abubuwa ne da ba za su taɓa gushewa daga zukatan iyalan su ba.
Ta ce har yanzu tana kewar lokutan da yake tara ‘ya’yan sa wuri guda yana sanya annashuwa a cikin gida, tare da yadda yake tashin su domin yin sallah.
“Na yi kewar sa fiye da yadda zan iya bayyanawa da kalmomi,” inji ta.
Rahama ta ƙara da cewa rayuwa ba tare da mahaifi ba abu ne mai wahala, tana mai cewa duk da ƙoƙarin da take yi na jure wannan rashi, akwai lokutan da zafin kewar kan fi ƙarfin ta.
A ƙarshe, ta yi addu’ar Allah ya gafarta wa mahaifin ta, ya yalwata masa rahama, ya sanya shi cikin Aljannar Firdausi, tare da bai wa iyalan sa haƙurin jure wannan babban rashi.
Sakon na Rahama ya ja hankalin masoya da abokan aikin ta a masana’antar shirya finafinai, inda da dama suka yi mata ta’aziyya tare da yi wa marigayin addu’ar samun rahama.
Saƙon ya kuma nuna irin kusancin da ke tsakanin jarumar da mahaifin ta, wanda rasuwar sa har yanzu ke ci gaba da haifar mata da raɗaɗi da kewar da ba ta gushe ba.

![]()







