FITACCIYAR jarumar Kannywood, Amal Umar, ta yi kira ga al’ummar Nijeriya da shugabannin ta da su mayar da hankali wajen magance matsalolin tsaro da na rayuwar yau da kullum da suka addabi ƙasar, maimakon shagaltuwa da batutuwan da ba su da wani tasiri kai-tsaye ga rayuwar jama’a.
Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin saƙon Barka da Juma’a da ta wallafa a shafin ta na sada zumunta, inda ta fara da addu’ar Allah ya haɗa al’umma da albarkar ranar Juma’a.
“Ya Allah Ka kawo mana mafita ga halin da Nijeriya take ciki. Mu ci gaba da addu’a, domin Allah ba Ya barci, kuma Shi ne Mai kawo sauƙi,” inji ta.
Amal ta ce ya kamata shugabannin ƙasar su tuna alƙawurran da suka ɗauka ga jama’a tare da gudanar da ayyukan su cikin tsoron Allah.
“Ku ji tsoron Allah, ku san cewa Allah Yana kallon duk abin da kuke yi. A kullum ana sace yara, ana kashe mutane, ana azabtar da su, amma matsalolin ƙasar na ci gaba da ƙaruwa. Ya kamata mu riƙa tattauna abubuwan da suka fi muhimmanci ga rayuwar al’umma, ba wai mu shagaltu da batutuwan da ba za su kawo mana mafita ba,” inji ta.
Ta kuma miƙa ta’aziyyar ta ga iyalan waɗanda suka rasa ‘yan’uwan su sakamakon matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar, tana addu’ar Allah Ya jiƙan su tare da ba iyalan su haƙurin jure rashin.
Jarumar ta yi amfani da damar wajen fayyace matsayin ta kan harkokin siyasa, tana mai cewa ta janye daga harkar siyasa tun bayan zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata.
Amal ta ce: “Ina ganin wasu suna zuwa ƙarƙashin saƙonni na suna cewa ni ma na shiga gaba a siyasa. Ina so ku sani cewa na daina siyasa tun daga lokacin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa. Mutunci na ya fi mini komai. Duk abin da mutum zai samu a siyasa ba zai kai darajar mutuncin sa ba.”
Ta ƙara da cewa ba ta da niyyar komawa siyasa, tana mai roƙon jama’a da su daina danganta ta da duk wani al’amari na siyasa.
Sai dai ta jaddada cewa duk wani ɗan Nijeriya yana jin raɗaɗin halin da ƙasar ke ciki, musamman matsalar tsaro da ta hana mutane gudanar da harkokin su cikin walwala.
“Abin da ke faruwa yana damun kowa, domin mu duka ‘yan Nijeriya ne. Ana sace mata ana wulaƙanta su, ana ɗaukar yara daga makarantu, har ta kai iyaye suna tsoron kai ‘ya’yan su makaranta. Wasu ba sa iya ziyartar ‘yan’uwan su a wasu jihohi saboda fargabar rashin tsaro,” inji ta.
Amal ta sake kira ga shugabannin Nijeriya da su cika alƙawurran da suka ɗauka na kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da ɗaukar matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙasar.
“Ku tsaya tsayin daka ku gyara mana ƙasar mu. Ku ji tsoron Allah, ku cika amanar da aka ɗora muku,” a cewar ta.
![]()







