• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, August 24, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rarara ya ci amanar mu a zamanin Buhari, da in bi shi gara in mutu – Iyan-Tama

by MUKHTAR YAKUBU
June 24, 2026
in Labarai
0
Rarara ya ci amanar mu a zamanin Buhari, da in bi shi gara in mutu – Iyan-Tama

Iyan-Tama da Rarara

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN jarumi kuma furodusa a Kannywood, Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, ya bayyana matsayin sa kan ce-ce-ku-cen siyasar da suka dabaibaye masana’antar, musamman kalaman da wasu ‘yan fim suke yi cewa dukkan masu harkar fim suna goyon bayan tafiyar mawaƙin siyasa Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) da kuma jam’iyyar APC.

Iyan-Tama, wanda sanannen ɗan siyasa ne a Kano, ya ce ba gaskiya ba ne a ce dukkan ‘yan fim suna tare da APC, yana mai jaddada cewa kowane mutum yana da nasa ra’ayin siyasa.

Ya yi wannan kalamin ne a wata hira da aka yi da shi a shafin onlayin na ‘Ɗan’uwa Rano TV’ a Kano.

Ya ce: “Ni uba ne a cikin harkar fim, shi kuma Rarara yaron mu ne. Saboda haka, ba dukkan mu ne ‘yan APC ba. Kowa yana da ra’ayin sa. Ni dai ba zan yi tafiyar Rarara ba. Da na yi tafiyar Rarara gara na mutu.”

Ya ci gaba da cewa, “Rarara ɗin nan ni ne na kai shi tafiyar Muhammadu Buhari, amma daga baya ya ci amanar mu, domin ya cuce mu. Akwai mutanen da zan iya zaɓa a cikin APC, amma ni ba na cikin jam’iyyar.”

Dangane da Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuwa, Iyan-Tama ya ce ba ya cikin masu goyon bayan sake zaɓen sa.

Ya ce: “Ni ba zan zaɓi Tinubu ba, domin tambayoyin da muka yi tun lokacin zaɓen sa har yanzu ba mu samu amsoshin su ba. Kowa yana ganin yadda matsalar tsaro ta ƙara ta’azzara a Arewa, amma an kasa magance ta. Abin da ba a iya yi wa magani tsawon shekaru ba, sai yanzu da ake tunkarar zaɓe ake cewa za a shawo kan sa. Don haka ni ba na tafiyar Tinubu, kuma ba zan zaɓe shi ba.”

Da aka tambaye shi game da yiwuwar goyon bayan sa ga Peter Obi ko Rabi’u Musa Kwankwaso, jarumin ya ce shi masoyin Kwankwaso ne, amma ba zai mara wa Obi baya ba.

Ya ce: “Ni masoyin Kwankwaso ne saboda na yarda cewa mutum ne nagari. Amma ba zan yi tafiyar Obi ba, kuma duk wanda nake da tasiri a kan sa ba zan ƙarfafa masa ya zaɓi Obi ba. Sai dai hakan ba yana nufin ba zai iya cin zaɓe ba idan Allah ya ƙaddara masa.”

Loading

Tags: Dauda Abdullahi Kahutu RararaHamisu Iyan-TamaKannywoodsiyasazaɓen2027
Previous Post

Kalaman Nafisa Abdullahi kan aure ba su wakilci kamfanin mu ba – Abnur Entertainment

Next Post

Gwamnatin Kano ta rufe gidan da furodusa Sultan yake shirin mayarwa dandalin shirya finafinai

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Gwamnatin Kano ta rufe gidan da furodusa Sultan yake shirin mayarwa dandalin shirya finafinai

Gwamnatin Kano ta rufe gidan da furodusa Sultan yake shirin mayarwa dandalin shirya finafinai

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!