• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, October 12, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Kano ta rufe gidan da furodusa Sultan yake shirin mayarwa dandalin shirya finafinai

by MUKHTAR YAKUBU
June 24, 2026
in Labarai
0
Gwamnatin Kano ta rufe gidan da furodusa Sultan yake shirin mayarwa dandalin shirya finafinai

Jami'ai suna kulle gidan Sultan; hoto na dama, Sultan Abdurrazak ne

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Gwamnatin Jihar Kano ta ba da umurnin rufe wani gini da ake zargin za a mayar da shi Dandalin Shirya Finafinai (film house) a Ɗorayi Ƙarama, cikin Unguwar Bello, a Ƙaramar Hukumar Gwale ta Jihar Kano.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan rufe ginin, Shugaban Kwamitin Kar-ta-Kwana na Daƙile Gine-ginen da Ba Su Cika Ƙa’idoji ba, wanda kuma shi ne Shugaban Riƙo na Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano, Dakta Ɗalhatu Aliyu Sani, ya bayyana cewa ginin zai ci gaba da kasancewa a rufe har sai gwamnati ta kammala nazari kan lamarin.

Ya ce kwamitin zai ci gaba da bibiyar duk wani gini da aka dakatar da shi ko kuma ake gudanar da shi ba bisa ƙa’ida ba, domin ɗaukar matakin da ya dace.

An dai shafe kusan mako guda ana ta ce-ce-ku-ce kan wannan gini tun bayan da mamallakin sa, Sultan Abdurrazaq, ya bayyana aniyar sa ta buɗe Dandalin Shirya Finafinai a wurin nan gaba kaɗan.

Bayan sanarwar ne wasu mazauna unguwar Ɗorayi, waɗanda suka bayyana kan su a matsayin membobin kwamitin unguwa, suka rubuta takardar nuna rashin amincewa tare da miƙa ta ga hukumomin da abin ya shafa.

A ranar Talata, Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa lamarin ya isa gaban sa, inda ya gayyaci mamallakin wurin da kuma masu ƙorafi daga unguwar domin sasanta matsalar.

Sai dai, a cewar sa, har zuwa lokacin da aka tsara zaman, masu ƙorafin ba su halarta ba. Sultan Abdurrazaq ne kaɗai ya je tare da jiran zuwan su na wani lokaci, amma bayan ya ga sun ƙi bayyana, aka sallame shi ya tafi.

Daga baya ne masu ƙorafin suka isa ofishin, inda aka sanar da su cewa wanda suke ƙara ya riga ya tafi bayan ya jira su ba tare da sun zo ba. Daga nan aka nemi su sake dawowa a ranar Laraba domin ci gaba da tattaunawa.

Sai dai kafin a samu cikakken bayani kan sakamakon zaman da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu a ranar Laraba, 24 ga Yuni, Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano ta ba da sanarwar rufe ginin tare da ɗaukar matakin dakatar da duk wani aiki a wurin.

Matakin da Hukumar Tsara Birane ta ɗauka kan wannan gini ya haifar da mabambantan ra’ayoyi a tsakanin al’umma, inda wasu suke ganin akwai yiwuwar siyasa ta shiga cikin lamarin.

Masu wannan ra’ayi na danganta hakan da kasancewar Sultan Abdurrazaq ɗan tafiyar Kwankwasiyya ne, kuma ya taɓa neman tikitin tsayawa takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar NDP, amma bai samu nasarar samun tikitin ba.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin da abin ya shafa ba su yi wata sanarwa da ke nuna cewa matakin da aka ɗauka yana da alaƙa da siyasa ba.

Loading

Tags: Abba El-MustaphaHukumar Tace Finafimai ta Jihar KanoSultan Abdurrazak
Previous Post

Rarara ya ci amanar mu a zamanin Buhari, da in bi shi gara in mutu – Iyan-Tama

Next Post

‘Kakanda’ ya samu takarar zama Gwarzon Fim a gasar bajekolin finafinai ta Eurasia-Kinofest a Rasha

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
‘Kakanda’ ya samu takarar zama Gwarzon Fim a gasar bajekolin finafinai ta Eurasia-Kinofest a Rasha

'Kakanda' ya samu takarar zama Gwarzon Fim a gasar bajekolin finafinai ta Eurasia-Kinofest a Rasha

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!