• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, October 12, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

‘Kakanda’ ya samu takarar zama Gwarzon Fim a gasar bajekolin finafinai ta Eurasia-Kinofest a Rasha

by ALI KANO
June 25, 2026
in Labarai
0
‘Kakanda’ ya samu takarar zama Gwarzon Fim a gasar bajekolin finafinai ta Eurasia-Kinofest a Rasha
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FIM ɗin Nijeriya mai dogon zango, ‘Kakanda’, ya sake cimma wata babbar nasara a matakin ƙasa da ƙasa bayan da aka zaɓe shi tare da ba shi takarar lambar yabo ta Gwarzon Fim (Best Film) a bikin Eurasia-Kinofest da aka kammala kwanan nan a birnin Sochi na ƙasar Rasha, da ke gaɓar tekun Black Sea.

Babban Furodusan fim ɗin, Dakta Ahmad Mohammed Sarari, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sa na soshiyal midiya domin murnar wannan gagarumar nasara.

Khalid Musa ne ya rubuta labarin fim ɗin, Toka Mcbaror ya ba da umarnin shirya shi, yayin da Sarari ya shirya shi.

Sarari tare da wasu mahalartan bikin baje-kolin finafinai na Eurasia-Kinofest da aka yi a Rasha
Dakta Sarari da wasu mahalartan bikin baje-kolin finafinan

‘Kakanda’, wanda fim ɗin Hausa ne, shi ne kaɗai fim daga Nijeriya da ma nahiyar Afrika da aka zaɓa tare da ba shi takara a wannan rukuni, lamarin da ke nuna yadda fim ɗin ke ƙara samun karɓuwa a duniya tare da zama wani babban cigaba ga masana’antar finafinai ta Nijeriya da kuma Kannywood.

Sanarwar ta bayyana cewa bikin Eurasia-Kinofest na murnar al’adun al’ummomi ne tare da inganta gaskiyar tarihi, ɗabi’u na gargajiya da kuma kyawawan ƙimomin ruhi da ɗabi’a.

Saboda haka, zaɓen ‘Kakanda’ na nuna irin ƙimar fasaha da al’adun da fim ɗin ke ɗauke da su..

Sarari ya bayyana farin cikin sa da ɗaukacin tawagar ‘Kakanda’ kan wannan nasara, yana mai cewa samun wannan takara shaida ce ta jajircewa, sadaukarwa da ƙwazon duk waɗanda suka taka rawa wajen samar da fim ɗin.

Babban furodusan ya kuma yi ta’aziyya tare da yaba wa marigayi Nura Shariff bisa irin gudunmawar da ya bayar wajen samar da fim ɗin. Ya ce jajircewar sa, sadaukarwar sa da ƙwazon sa sun taka muhimmiyar rawa wajen nasarar da fim ɗin ya samu.

Sarari a Sochi

A cewar sa, abin da Nura ya bari zai ci gaba da kasancewa wani muhimmin ɓangare na wannan nasara, kuma tarihin rayuwar sa zai ci gaba da zaburar da ‘yan wasa da masu shirya fim ɗin yayin da ‘Kakanda’ yake ci gaba da samun ɗaukaka a fagen finafinai na duniya.

“Jajircewar sa, sadaukarwar sa da ƙwazon sa sun kasance wani muhimmin ɓangare na wannan nasara, kuma tarihin sa zai ci gaba da zaburar da mu,” inji Sarari.

Ahmad Mohammad Sarari a Sochi, ƙasar Rasha

Loading

Tags: Ahmad Muhammad SarariEurasia-KinofestKakandaMalam Khalid MusaNura SharifSochiToka Mcbaror
Previous Post

Gwamnatin Kano ta rufe gidan da furodusa Sultan yake shirin mayarwa dandalin shirya finafinai

Next Post

Jarumar Kannywood Momee Gombe ta gina masallaci a matsayin sadaƙatul jariya ga iyayen ta

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Jarumar Kannywood Momee Gombe ta gina masallaci a matsayin sadaƙatul jariya ga iyayen ta

Jarumar Kannywood Momee Gombe ta gina masallaci a matsayin sadaƙatul jariya ga iyayen ta

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!