• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, October 12, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jarumar Kannywood Momee Gombe ta gina masallaci a matsayin sadaƙatul jariya ga iyayen ta

by ABBA MUHAMMAD
June 25, 2026
in Labarai
0
Jarumar Kannywood Momee Gombe ta gina masallaci a matsayin sadaƙatul jariya ga iyayen ta

Masallacin da Momee Gombe ta gina a kusa da gidan iyayen ta a Gombe

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCIYAR jarumar Kannywood, Momee Gombe, ta sake jawo hankalin jama’a bayan da ta gina sabon masallaci a matsayin sadaƙatul jariya ga mahaifin ta da mahaifiyar ta a kusa da gidan su da ke Gombe.

An buɗe masallacin ne a yau Alhamis cikin yanayi na farin ciki da godiya ga Allah, tare da halartar malamai, ‘yan’uwa, abokai da maƙwabta, waɗanda suka taru domin shaida wannan gagarumin aikin alheri.

A jawaban su, malamai sun yi bayani kan falalar gina masallatai da muhimmancin ayyukan sadaƙatul jariya, waɗanda lada ke ci gaba da gudana ga mamaci ko wanda ya aikata su ko da bayan rasuwar sa.

Sun yaba wa Momee Gombe bisa wannan kyakkyawan tunani na sadaukar da masallacin ga iyayen ta, tare da addu’ar Allah ya karɓi wannan aiki, ya sanya shi cikin ma’aunin kyawawan ayyukan su.

Mahalarta taron sun bayyana cewa wannan aiki abin koyi ne ga matasa da masu hali, domin yana nuna yadda za a yi amfani da ni’imar da Allah ya yi wa mutum wajen amfanar al’umma da neman yardar sa.

Momee Gombe a Ka’aba

Bayan kammala wa’azi da addu’o’i, an gudanar da sallar jam’i ta farko a sabon masallacin, inda aka yi addu’ar Allah ya sanya shi ya kasance cibiyar ibada, ilimi da haɗin kan al’ummar yankin.

An kuma yi wa Momee Gombe addu’ar Allah ya saka mata da alheri, ya ƙara mata ɗaukaka da albarka, tare da sanya wannan aiki ya zama haske gare ta da iyayen ta a duniya da lahira.

Daga cikin fitattun ‘yan Kannywood da suka halarci bikin buɗe masallacin akwai Abdulazeez Ɗan Small, Salisu S. Fulani, Nasiru A. Ƙoƙi (Shehu Jaha) da Hamza Dogo Ɗandago.

Loading

Previous Post

‘Kakanda’ ya samu takarar zama Gwarzon Fim a gasar bajekolin finafinai ta Eurasia-Kinofest a Rasha

Next Post

Ɓatagari sun farfasa motar da ake kai jarumar Kannywood Halisa Muhammad asibiti

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Ɓatagari sun farfasa motar da ake kai jarumar Kannywood Halisa Muhammad asibiti

Ɓatagari sun farfasa motar da ake kai jarumar Kannywood Halisa Muhammad asibiti

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!