WASU tsofaffin jarumai na masana’antar Kannywood da kuma wasu daga cikin matasa da ake damawa da su sun kafa wata sabuwar ƙungiyar mata ‘yan fim mai suna ‘Association of Kannywood Female Artistes’ (AKAFA).
Ƙungiyar, wadda ta mata zalla ce, ta ƙunshi matan aure da zawarawa da ‘yan matan da su ke harkar fim ko su ka taɓa yi a baya.
Haka nan ƙungiyar za ta yi tafiya da ‘ya’ya da kuma jikokin duk wata jaruma waɗanda iyayen su su ka rasu, da ma waɗanda iyayen su ke da rai.
Sabuwar ƙungiyar dai ta na ƙarƙashin shugabancin Rashida Adamu Abdullahi (Maisa’a) da Mansurah Isah a matsayinf sakatariya, yayin da Muhibbat Abdussalam ta ke a matsayin jami’ar yaɗa labarai.
A lokacin da ta ke yi wa mujallar Fim bayani game da ƙungiyar, Muhibbat ta bayyana cewar, “Duk da cewar ita wannan ƙungiyar sabuwa ce, amma za mu iya kiran ta ba sabuwa ba, tunda tamu ce ta ‘yan fim da su ka ƙunshi na baya da kuma na yanzu har da mawaƙa da matan aure da ma duk wata mace da ta taɓa yin fim ko waƙa ko wani aiki a cikin masana’antar Kannywwod.”
Ta ci gaba da cewa, “Mun kafa wannan ƙungiyar ne domin mu haɗa kan mu, mu ƙulla zumunci a tsakanin mu har ma da yaran mu da su ke tasowa, domin mu waɗanda mu ka yi fim a baya da masu yi a yanzu mu na da kishin junan mu, dukkan mu mana kallon mu a matsayin ‘yan’uwan juna, don haka mu ka kafa ƙungiyar domin ƙulla zumunci a tsakanin mu, kuma yaran mu su haɗu su san juna. Domin a yau idan aka ce ba ma raye ‘ya’yan mu za su ci gaba da zumunci a tsakanin su. Kuma a yanzu abin da mu ke shirin yi a cikin mu duk wadda ta ke cikin matsala za mu haɗu mu taimaki junan mu, domin mu magance matsalolin mu a tsakanin mu.”
Da wakilin mujallar Fim ya tambaye ta ko me ya bambamta wannan sabuwar ƙungiyar tasu d sauran ƙungiyoyin mata ‘yan fim da aka yi a baya kuwa, sai ta ce, ” A gaskiya wannan ƙungiyar ta ‘Association of Kannywood Female Artistes’ (AKAFA) ta na da bambanci sosai da na baya, saboda ita wannan ba mu fara ba sai da mu ka yi wa juna alƙawarin cewa ba cuta babu cutarwa, kuma ba za mu bar wani ya cuci wani ba. Don haka za mu yi tafiya ta taimakon juna ne a tsakanin mu da kuma ƙulla zumunci.”
Ƙungiyar dai zuwa yanzu ta na da mambobi da su ka haɗa da Mansurah Isah, Rasheeda Adamu Abdullahi (Maisa’a), Muhibbat Abdulsalam, Samira Ahmad, Rahama Hassan, Asma’u Sani, Jamila Gamdare, Fati Slow, Fauziyya Sani (Maikyau), Fati S.U. Garba, Amal Umar, Maryam Isah Abubakar (Ceeter), Hadiza Gabon, Ruƙayya Umar Santa (Dawayya), Ummi Gombe, Halima Atete, Aishatul Humaira, Fati Washa, Momee Gombe, Fati KK, da sauran su.
Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa a yanzu haka ƙungiyar za ta gudanar da babban taron Sallah nan da sati biyu masu zuwa domin tabbatar da kafuwar ta.
A yanzu kenan an yi wa Ƙungiyar Matan Kannywood ta Nijeria, wato K-WAN, kishiya. A da K-WAN, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Hauwa A. Bello, ita kaɗai ƙungiyar mata ‘yan fim a masana’antar.
![]()







